Fitowa tayi daga cikin daki, taci karo da Kamal zai wuce ta corridor.
"Kin tashi?" Ya tambaye ta. "Ya kike jin jikin ki?
"Na gode da nesanto da kayi daga wurin nan. Amma ina ga ni zan wuce gida."
A tsanake yake kallon ta na wasu yan dakiku kafin ya bata amsa da katuwar muryar shi da ta kusan tsorata ta.
"Ba zaki je gida ba, kin min alkawarin zaki min bayanin komai."
"Dan Allah, ka barni naje gida. Ina tunanin shine mafita a yanzu. Bana son na saka ka a cikin abinda bai shafe ka ba. Kuma ba lallai ba ka yarda da ni idan na fada maka abinda ke faruwa da ni. Nafi son na je gida."
"Kina tunanin, a maida ki gidan da zan yi, labarin bai shafe ni ba tuni? Ko ba komai na cancanci wannan. Kan na yarda da abinda zaki fada mini kuwa, ba zan iya cewa komai ba tinda baki fada min komai ba. Ba zan miki alkawarin yarda da abinda zaki fada ba, amma nayi miki alkawarin zan martaba duk wata kalma da zata fito bakin ki. Muje falo, zan yi order lunch sai ki min bayanin komai."A ranta tunani take : A'a ba zata iya saka shi a wannan labarin ba, domin Amriya zata iya cewa ta cutar da shi. Kuma in tayi hakan bata kyauta ba. Ya kamata ta bar wurin nan da sauri.
"Zan maka bayani wani lokacin, zan je wajen aiki yanzu ne."
Tayi masa karya dan ya barta ta tafi. Bata da tunanin zuwa wajen aiki bayan abinda Amriya ta fada a kan Salmah. Bata iya ma tunanin irin kunyar da zata ji idan taje gaban ogan ta ba. Tana jin kanta tamkar wata muguwa kan abinda Amriya tayi. Wahalar ta tsaya a ita daya, ba zata so wasu su samu matsala ba ta dalilin ta. Ya kamata tayi nesa da kowa amma bata san me zata yi ba ko ta yaya zata yi ba... Tana tsoron ta cutar da mutane fiye da yanda take yi yanzu.
"Kina da taurin kai amma ni na fiki, please, kije falo kafin nayi odan abincin. Bayan nan sai ki min bayanin komai. Kar ki damu a kaina, kawai ki fada min abinda ke faruwa da ke."
"Bai shafe ka ba Malam.." Ta fada wannan karon da dan bacin rai. Bata san ta ina ta samu wannan kuzarin ba, amma wannan ce kadai hanyar da zai sa ya fahimci bata son saka shi a matsalar ta.
"Ya shafe ni, saboda ya shafi dangina, ba zan barki ki tafi ba dan haka kina iya ihu iya son ranki. Zaki gajiyar da kanki ne kawai." Ya fada mata shima sannan ya cigaba da tafiyar shi zuwa kitchen kamar komai bai faru ba.
"Ba..zaka..gane ba.." Ta fada tana kokarin bin bayan shi amma shi kuma ya kara sauri ba tare da ya kula ta ba.
Kofar fita ta nufa tana kokarin budewa amma ta kasa domin a rufe take, kuma babu keys a jiki. Ganin ba sarki sai Allah dole tayi yanda yace. A sanyaye ta koma falo ta zauna a daya daga cikin kujerun falon. Tsabar haushin da ya bata yasa bata lura da manyan hotunan zane. Kusan duka falon an kawata shi da zanukan. Tana tunanin shi ke zana su ganin daga gefe akwai zanen da ba'a karasa ba. Da alamu mai son zane ne shi.
Ta kusan rabin awa zaune tana kallon zanukan. Daga karshe wani ya konkwasa kofa. Kamal ne ya fito da sauri yaje ya bude.
"Yauwa nagode." Taji ance kafin a rufe kofar. Mikewa tayi da niyyar sake gwada sa'ar ta wannan karon ko ya barta ta tafi gida, sai dai kafin ta karasa sai gashi ya shigo falon ledoji a hannun sa. Komawa tayi ta zauna. Shi kuma ya ajiye ledojin bisa table ya koma ya fita kamar yanda ya shigo. Tana kallon sa ya cika table din da kayan ci da na sha ba tare da ya kula ta ba. Bayan kai komo mai yawa da yayi daga karshe yace mata ta fara cin abincin. Plate ya turo mata gabanta, sannan ya ajiye mata coffee mai madara. Ganin ya tsare ta da ito, ta fara cin abincin. Jinta take duk a takure dan idan ta kai loma sai ta fi minti biyar bata hada ta ba.
"Ni bana cin komai sai coffee, dan haka duk wannan ke na siyowa shi. Ki ci..." Ya umarce ta.
"Ni gida zan je, bana son hankalin iyaye na ya tashi. Basu da labarin inda nake tun jiya. Ban ma san wani hali suke ciki ba yanzu."
YOU ARE READING
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
HorrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...