Rabon da Khadija taji irin wannan kuncin zuciyar, tun ranar da iyayen ta suka rabu. A lokacin tana da shekaru 15 dan haka tana fahimtar duk abinda ke faruwa. Kunci ba komai bane akan halin da ta shiga kwanakin da biyo bayan mutuwar auren iyayen ta. Yau gashi ta sake tsintar kanta cikin yanayin, kuma tsoro da fargaba ne suka dabaibaye ta na gudun abinda zai faru nan gaba..lokutan bakin ciki.. nadama da kuma wahala. Bata taba tunanin Kamal zai yi mata irin haka ba. Ta kawo tunani iri-iri na dalilin da yasa Kamal ke gudun ta, amma bata taba kawowa saboda Zahara bane.
Dafa bango tayi domin taimakawa kafafuwan ta da suka kasa daukan ta. Kamal shima bai ji dadin ganin zanen Zahara da tayi ba, bayan abinda Ammar ya fada masa. Ya kara tabbatar masa gaskiyar cewa Khadija tana son shi. Ba wani kwararre bane shi wajen gane irin haka. Amma yanzu da yasan gaskiya, lamarin ya ida cabewa. Ta yaya zai iya sanar da ita baya jin abinda take ji ba tare da ya cutar da ita ba? Kuma tashin hankalin yanzu, ta ga hoton Zahara dole zata so yayi mata cikakken bayani.
Kamal kokarin yanda zai yi ya tattara kalaman da zai yi amfani da su wajen yiwa Khadija bayani yake. Matsawa yayi kusa da ita, ita kuma tayi tsalle tayi baya tare da hadewa da bango.
“Kar ka matso kusa da ni, ta yaya ka iya yin haka? Me ke ga wannan yarinyar da kuke ta rawar kafa a kanta?”
“Maganar me kike?” Kamal ya tambaye ta. “Baki san me kike fada ba Khadija, bansan me aka fada miki ba, amma kin yi kuskure. Ba abinda kike tunani bane.”
“Nasan me nake fada, saboda yarinyar nan Ammar da Salmah suka rabu. Fada min ba soyayya kake da ita ba... Fada mini please.”
“Ba soyayya nake da ita ba, amma a shirye nake idan ta amince da ni. Babu wani bashi da kika biyo ni Khadija, rayuwa ta ce. Idan kina tunanin ta dalilin ta ne kawar ki da Ammar suka rabu good, ba zan tilasta ki ba ki karya ta kanki amma ba ke zaki fada min abinda zan yi ba.”
Khadija ji tayi tamkar an caka mata wuka a kirji. Taji numfashi na kokarin ya gagare ta. Dafe daidai zuciyar ta tayi tana tambayar kanta idan da gaske wanda ke gaban ta best friend dinta ne Kamal.
“Dan Allah ce da ni mummunan mafarki nake. Na tabbatar mafarki nake.. fada min please.”
Kamal yaji ba dadi na ganin halin da ta shiga. Amma bata da yancin shiga rayuwar shi. Ya tsani a dinga shiga sha'anin sa, kuma ba yau hakan zai canza ba. Ko mahaifiyar shi ta daina shiga harkokin sa.. domin bai bata dama ba.
“Listen Khadija, you are my best friend... kin fi kowa sanin ko ni waye. Kin san cewa ba zan bibiyi abinda bani da ra'ayi a kan...”
Katse shi tayi
“Ni ba best friend din ka bace, ban taba daukan kaina a wannan matsayin ba kuma kaima kasan da haka. Kasan cewa ina matukar sonka, kana tunanin zan zauna banda saurayi alhali ina da masu sona. Ban kula samari ne saboda ina hango kaina a matsayin matar ka.”Kamal kara tunkarar inda take yayi, amma ta kara danganewa da bango da iya karfin ta.
“A'a.. bani bukatar wata tausayawar ka, kuma ka sani ba zan taba hakura da kai ba. Na rasa shekaru da dama na rayuwa ta ta 'ya mace saboda kai, bana tunanin zan yafe maka wannan. Ina son ka fada min komai game da yarinyar nan.”
Kamal yayi kamar bai gane me take nufi ba, sun dade tare amma bai taba ganin wannan dayan fuskar tata ba. Khadija ta kasance mai nutsuwa da tunani.
“Eh, ka jini da kyau Kamal. Na cancanci sanin ko iya wannan ne.”
“Baki biya ta bashin komai Khadija, i'm sorry amma ni ban taba yi miki wani alkawari ba. Ba lallai zan san abinda kike ji ba game da ni idan baki fada min ba yau. Ba laifi na bane kuma kinsan da hakan.”
“Nima ba laifi na bane idan sakarcin ka ya hana ka gane na haukace a kanka. Ina yin duk wani abinda kace nayi. Dan Allah Kamal...nasan tsakanin ka da ita pass attraction ne kawai...mun san juna tsawon shekaru...ba zaka ce baka jin sona ko kadan a zuciyar ka ba. Please kar ka min haka.”
ESTÁS LEYENDO
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
TerrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...