CHAPTER 5

1.4K 34 0
                                    

Kwanaki da yawa sun shude, Zahara bata sake jin wani motsin Amriya ba, babu wani sauyi da ta sake ji a kanta. Wannan shurun kuwa ba karamin tayar mata da hankali yake ba. Tana son tayi amfani da wannan shurun wajen cigaba da rayuwar ta kamar baya, amma duk lokacin da zata nufi wannan corridor sai taji kamar ana kallon ta. Sai dai ba ita kadai bace ke cikin rudu ba a wannan kamfanin. Uban gidan ta da sauran abokanan aikin ta hankalin su a tashe yake na ganin sauyin da ta samu. Sai dai ba wanda yayi gigin fadar wani abun dan kar su janyo fushin uban gidan su.

A yau, Mr. Amar Yusuf ya shirya wata yar walima a gidan su domin taya kamfani murna kan wata contact da ya samu daga kasar Korea. Mr. Amar ya nemi duk ma'aikatan su hadu a dakin meeting inda ya basu labarin nasarar da suka samu da kuma walimar da ya shirya tare da basu adreshin gidan su. Zahara da tuni ta yanke shawarar kirkiro wani abun da zai hana ta zuwa, taji Mr. Amar yace wajibi ne kowa sai ya halarta.
Bayan duk abinda ta aikata, duk abinda wannan Amriya ta aikata mata, bata jin zata iya zuwa wajen wannan walimar, amma gashi uban gidan ta yace wajibi ne sai kowane ma'aikaci yaje. Kuma ita ce sakatariyar sa dan haka dole idan bata je ba zai gane. Allah Allah take kar budurwar sa taje, domin ba zata iya hada ido da ita ba. Ga kuma dan uwan shi Mr. Kamal, idan ta kai kanta har gidan su, tasan har fitsari zata iya yi a wajen. Irin kallon nan nashi.. har yau yana zo mata a munanan mafarkan ta.

Zungurar ta da taji ana yi ne a baya ya dawo da ita hayyacin ta, ta juya taga Sarat ce.

"Wane irin kaya zaki saka?" Sarat ta rada mata a kunne ta yanda sauran ba zasu ji ba.

Har yanzu suna cikin dakin meeting, duk da an kare meeting din amma basu watse ba kowa maganar walimar yake.

"Toh yaya?" Sarat ta sake tambayar ta.

Kada mata kafada Zahara tayi alamar bata sani ba. Ita ba wasu kaya gare ta, bacin jeans da dogayen rigunan da ba zata iya zuwa wajen walimar da su ba. Dan haka kawai zata yi shigar ta ne kamar yanda ta saba. Zata je ne kawai dan a san tazo.

"Muna iya zuwa muyi chopping." Cewar Sarat, amma Zahara taki.

"Bakauya ce ke wallahi." Sarat ta fada tare da jan tsaki. "Toh ni cancarewa zan yi, domin nasan manyan mutane zasu halarci wannan walimar, kuma ni akwai wanda nake hari. Ina son ya fada tarkona." Sarat ta fada.

"Humm Allah ya bada sa'a."

"Kin tabbatar ba zaki je muje ba? Zamu iya zuwa Ahmad SH Mall."

"Akwai abubuwa da dama da zan yi, ki huta lafiya." Zahara ta mike tsaye da niyyar barin wurin amma wani masifaffen ciwon kai da taji yasa ta koma ta zauna da karfi ta yanda tayi sanadin janyo hankalin mutane kanta.

"Zahara, lafiya?" Mr. Amar ya tambaye ta yana mai matsowa kusa da ita.

Da sauri ita kuwa Zahara tayi baya dan kar ya taba ta. Taga irin kallon da yayi mata ganin abinda tayi, hakan kuwa bai mata dadi ba. Bata son ta zamar masa wata matsala ce alhali yana da matar zai aura.

Kara kokarin riko hannun ta yayi, amma ta sake yin tsalle tayi baya.

"Kawai na dan gaji ne, kuyi hakuri dan Allah." Zahara ta fada tare da ficewa daga dakin meeting din kamar wata barauniya.

Ta tabbatar yau, maganar ta kawai za'a dinga yi a kamfanin. Toilet ta shiga ta rufe kanta na wani dogon lokaci. Wanke fuskar ta tayi, ta dan huta kafin ta dawo hayyacin ta. Daga karshe fitowa tayi ta nufi hanyar ofishin ta, sai dai tana fitowa taci karo da Mr. Amar, jikin ta ya bangaji faffaden kirjin sa. Hakuri ta shiga bashi akan buge shi da tayi ba tare da ta gani ba.

"Kin dan jima, kin tabbatar lafiyar ki kuwa?"

"Eh, amm..nagode. Kar ka damu. Zan je na cigaba da aiki na kafin naje gida." Ta fada da kokarin barin wurin amma ya riko hannun ta.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant