CHAPTER 49

127 8 2
                                    


“Na sha faɗa miki ki daina kira na Salmah. Na fara gajiya kina ji na?” Ammar ke faɗawa Salmah da ke tsaye gabansa.

Kuka Salmah ta fara, ta fara ƙin jurar wannan son da take yiwa Ammar shi kuma baya son ta. Tana son dawo da shi amma shi kwata-kwata baya ra'ayinta, shikenan ya daina son ta. Ta yi samari da dama a wannan ƴan shekarun amma ta kasa mantawa da Ammar domin shi ne namijin rayuwarta.

“Kada ka yi min haka Ammar, kai ne kaɗai wanda nake da. Nayi kuskuren yanke alaƙarmu amma kai ma ka sani it's impossible na sake yarda na koma rayuwata ta baya.”

“Ki daina ɗorawa kanki laifi, kin yi abinda kike ganin ya dace ni ma haka. Na rufe wannan babin yanzu, ke ma ki yi hakan dan Allah Salmah.” Ammar ya faɗa wannan karon da sanyin murya.

“Ammar ba zan iya ba.” Ita ma ta faɗa a hankali. “Ina matuƙar son ka.” Ta ƙarasa faɗa a sanyaye.

“Ki yiwa girman Allah ki rabu da ni Salmah.” Ya faɗa cikin daka mata tsawa.

“Shikenan babu wani ɗigo na sona da ya yi saura a zuciyarka? Na tabbatar zamu iya ƙara hasa wutar soyayyar da ke zukatanmu. Zaka iya aure na a matsayin matarka ta biyu, na rantse maka da Allah zan kasance mai biyayya a gare ka, ba zan haifar maka da wata matsala ba.”

Kama hannun Ammar ta yi ta kai wajen bakinta tare da yi masa ɗan ƙaramin kiss.

“Bana son ki yanzu Salmah I'm sorry kuma bana buƙatar sake kunna wata wutar soyayya.” Ya ce yana fizge hannunsa daga na tsohuwar budurwar tashi.

“Kuma dan Allah ki daina zuwa kina harassing ɗina, zaki haifar da matsala ne a gidana.”

“Okay shikenan, zan yi ƙoƙarin mantawa da kai duk da na san hakan abu ne da ba zai taɓa yiyuwa ba a gare ni.”

“Sorry ni tafiya zan yi ki kula da kanki Salmah.” Yace da ita kafin ya tafi.

Yinin ranar bai daina tunanin maganar da suka yi ba. Haka ne ya daina sonta amma baya son ganin ta cikin wannan halin. Yana son a ko iya abota su tsaya yanda zai kwantar mata da hankali har ta fahimci cewa shi ya manta da babin soyayyarsu amma hakan ma ba mai yiyuwa ba ne domin bai san iya adadin haɗarin da ke ciki ba.

Knocking ƙofar ofishinsa ya ji ana yi.

“Waye? Ya shigo."

Sarat ce ta shigo hannunta cike da takardu.

“Farfesa Kasim ne ya ce in kawo maka wannan documents ɗin.”

“Tun sati biyu baya ya kamata a ce ya bani su, amma da yake nan babu mai bin dokar aikinsa, sai yau ya aiko min su.” Ya faɗa da ɗan ɓacin rai.

“Na ga yanzu tsohuwar budurwarka na yawon kawo maka ziyara, ko matarka tanada labari?”

“Wani raini ne tsakanina da ke yanzu Sarat?”

“Ba sau ɗaya muka kwanta a gado ɗaya ba. Me yasa kake tunanin raini ba zai shiga tsakaninmu ba?” Sarat ta faɗa cikin sigar raini.

“Ya isa haka Sarat, a wajen aiki muke. Na san cewa rabuwa da nayi da ke ya tsaya miki har yau a wuya but let's be professional. mu manta da duk wannan.”

“You're a real jerk, da gaske kana tunanin hakan sauƙi ne da shi? Idan ka manta na tuna maka mahaifiyata ta kama mu a gidana kuma tun daga ranar ta daina ganin mutuncina. Ta san cewa mun kwana tare kuma I feel his judgment every time she looks at me. Da gaske kana tunanin hakan sauƙi ne da shi? I feel that my life is destroyed.” Sarat ta faɗa tana zaunawa ɗaya daga cikin kujerun gurin.

Ajiye biron hannunsa ya yi, ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya gareta.

“Ban san cewa alaƙarmu ta samar miki da matsala ba har haka a rayuwarki.”

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now