CHAPTER 20

201 33 4
                                    


Kwanaki na shudewa babu abinda ya sauya gidan Alhaji Yusuf. Kamar yanda yace, Ammar ya bar gidan iyayen sa ya koma sabon gidan shi da babu nisa da kamfani. Yana ganin abinda ya faru ya gyarashi na wani bangaren, domin ya bashi damar yin tunani akan matsalar shi, ya kan zauna yayi nadamar laifin da ya aikatawa mahaifiyar sa. Amma idan ya tuna yanda mahaifiyar sa tayi masa, sai yaga ba laifin sa bane.

A bangaren Hajiya Karima kuwa, ta kasa gasgata abinda danta yayi mata. Tayi tunanin idan tace zata sallamashi zai ji tsoro yayi abinda take so, saidai tayi kuskure. Mamakinta kasa boyuwa yake, a takaice dai cikin zuciyarta tsoron rasa danta take, wanda shi kadai ne yake sauraronta kuma yake mata biyayya ba tareda wata matsala ba.

Tana jin kamar a dawo baya, ta hana bakinta fadar wadannan kalaman kuma ta shawo kan matsalar ta wata hanyar.  Tayi ta kokowa da son kiran dan nata na tsawon makonni amma ji da kai ya hanata kuma zuciyarta na ce mata ai zai dawo gare ta. Jiran da take yi masa kenan a kullum.

Tsawon watanni kenan tana jira amma bata ga inuwar danta ba, babu kuma labarin shi. Hakan ba karamin tayar mata da hankali yayi ba, har ta fara fidda rai. Gashi kawarta na fushi da ita. Babu mai goya mata baya, har mijinta ya daina shiga al'amarin, alhali shine na farko da ya kamata ace ya saka  lamarin.

Saidai Hajiya Karima bata san ba rabuwa da danta bane kadai tashin hankalin da zata fuskanta. A safiyar yau, kamar kowacce safiya tsayin wasu watanni, Afnan ta daina zuwa school. Hajiya Karima tayi ta mata tambayoyin dalilin barin zuwanta school, ita da ke da kokari sosai. Amsar da Afnan take bata na damunta : Kawai bana son zuwa ne.

Duk da fadan da Hajiya Karima ke mata, Afnan taki tayi mata bayanin me yake damunta. Hajiya Karima ta fara tsorata da canjin da 'yarta take samu. Ta daina cin abinci sosai, amma sai kiba take yi, batada aiki sai yawan bacci da cin gyada. Halin da har ya janyo hankalin Rakiya mai aikin su. Afnan ta kan yawan ce mata ta hada mata tea da mint domin duk safe zata ce bata jin dadi. Hajiya Karima ta lura da duk yanayin 'yar tata amma taki ta yarda da abinda take tunani.

Saidai yau da safen nan, taga Afnan ta sauko daga sama ta nufo inda take, lokaci guda kuma ta nufi toilet a guje rike da bakinta. Ganin yanayin 'yar tata, Hajiya Karima tabi bayanta ita ma. Tana saka kafarta cikin dakin, karnin amai ya bade mata hanci. Nan taga Afnan durkushe gefen masai tana amaye duk abinda taci jiya.

Yanzu ne ta gasgata abinda take tunani, komai gashi zahiri a idonta, amma taki yarda. 'Yarta juna biyu gareta. Duk da haka sai da ta yiwa Afnan tambayar kamar idan taji gaskiyar ga bakin 'yar tata wani abu zai canza.

“Ciki gare ki?”
Zabura Afnan tayi tareda faduwa kasa, muryar Mommy ta tsorata ta. Dama kwana biyun nan tsoron yin amai take gabanta, yau ma bata ankare bane har ta rutsa ta. Tasan ko ba dade ko ba jima Mommy zata gano gaskiya kuma abin mamaki murnar hakan take. Murna take saboda daga yau babu wata barazana da zata sake fuskanta. Fashewa da kuka tayi yayin da ita kuma Hajiya Karima ke addu'ar Allah yasa mafarki take.

“Mom..” Afnan ta fada cikin kuka tana mai tuna irin ciwon da taji ranar da ta gane tana da ciki. Saidai wannan ciwon ba komai bane akan ciwon sanin uban cikin da ba kowa bane face mjin wacce ta rike ta.

“Mom? Har kina da karfin gwiwar kirana Mommy? Idan da kina daukata a matsayin mahaifiyar ki da ba zaki janyo min wannan abun kunyar ba.”

Afnan kuka take kamar ranta zai fita.

“Please Mom..”

“Please what?” So kike in taya ki murna ko me? Me zan fadawa mahaifiyar ki wacce ta bani amanar ki? Me zan fadawa mutanen da zasu ce ban baki tarbiyar ba domin ba uwa ta gari bace ni? Ta yaya kike son na kalli idon duniya?”

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Onde histórias criam vida. Descubra agora