BAYAN WASU SHEKARU
Khadija ce ta dawo daga asibiti, da ƙyar take hawan stairs ɗin gidan. Kamal ne ya kamata ya raka ta zuwa asibitin amma ya yi wasu baƙi daga ƙasar waje. Ta ji haushin ganin ya bar ta daidai lokacin da take buƙatar sa amma wannan haushin dandanan ya ƙaura lokacin da likita ya tabbatar mata da cikin da ke gare ta yana cikin ƙoshin lafiya. Farin ciki take sosai da ƙara samuwar juna biyu da ta yi, ta yanda take yin komai ganin ta kula da shi, bata son wanin abun ya same shi kamar na farkon. Abinda ya faru da ita ya yi matuƙar girgiza ta yanda har yau bata samun baccin kirki da dare. Bata son kawar da idonta ko na daƙiƙa ne gudun kar Amriya ta dawo ta cutar da ita. Ta ji daga bakin mijinta cewa Amriya ta musulunta amma duk da haka hankalinta bai kwanta ba. Tana kare kanta ta hanyar salloli, addu'o'i da azkar haka kuma ta mayar da sauraron karatun alƙur'ani abun jinta a koda yaushe..
“Hanne zo ki buɗe ƙofa dan Allah, na gaji sosai wallahi.” Khadija ke ƙwalawa ƴar aikinta da ita kaɗai ce a gidan kira.
Zaune ta yi bakin ƙofar tana jiran Hanne. Sai da ta sake ƙwala mata kira kafin ta zo ta buɗe mata.
“Gaisuwa Hajiya, yaya ganin likitan?” Ƴar aikin ke tambayar ta.
“Alhamdulillahi, lafiya lau baby yake. Zan cigaba da tattakawa ko cikin gida ne, hakan yana rage raɗaɗin naƙuda.”
Da taimakon Hanne Khadija ta tashi ta shiga cikin gida. Juyowa Khadija ta yi da mamaki jin Hanne na dariya.
“Me aka yi kuma?”
“Cikin wata na shidda kawai kike amma kin fara maganar haihuwa.”
“Toh ki sani na fara tunanin haihuwa tun lokacin da na san inada juna biyu.” Khadija ta bata amsa tana mai zaunawa kan ɗaya daga cikin kujerun falon.
“Salmah ta zo?” Khadija ta tambaya.
“Ta zo baki daɗe da fita ba amma ta ce zata je karɓar wani saƙo amma zata dawo zuwa shidda na yamma.”
“Shikenan, ina ga zan ɗan samu bacci kafin ta dawo.”
“Toh ni zan je in cigaba da girki kafin dawowan yallaɓai.”
Kai ta gyaɗa mata kafin ita ma ta hau sama zuwa ɗakinta dan ta huta. Ta so yin bacci amma tunani ya hana. Nan da ƴan kwanaki ne birthday ɗin Kamal kuma tana son shirya masa partyn suprise, saidai wannan lokacin busy yake game da zanukan da yake yi. Ya buɗe workshop ɗin yake son buɗewa. Khadija ta ji daɗi sosai da mafarkin mijinta ya tabbata, saidai tun bayan wannan ya daina samun lokacinta da ma nashi lokacin. Akwai haushi ! Amma bata ce komai ba, gudun kar ta kunno wata rigimar, komai yana tafiya daidai a tsakaninsu yanzu. Ba daidai ba ne ta ɓata komai dan kawai yana busy.
“Na tabbatar komai zai dawo daidai idan ya gama wannan kwangilar." Ta faɗa a ranta.
Khadija ta yi nisa sosai cikin tunaninta ta yanda bata ji buɗowar ƙofa ba.
“Na tashe ki?” Salmah ta tambaye ta da tuni ta shigo cikin ɗakin.
Zabura Khadija ta yi domin bata yi tsammanin ganin ta yanzu ba.
“Kin tsorata ni mahaukaciya, ba a koya miki knocking ba ne kafin ki shigo?”
“Nayi knocking yafi sau dubu, amma baki amsa ba.” Salmah ta faɗa tana zaunawa kusa da aminiyar tata. Zaunawa Khadija ta yi don jin yaya Salmah ta ke.
“Humm.."
“Kamar yaya humm? Me kuma kika yi?”
“Na ɓata yinin ranar nan ina zarga cikin post neman package ɗina amma shashahun nan sun kasa gano wanne post ne saƙon nawa yake.”
CZYTASZ
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
HorrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...