CHAPTER 15

214 32 0
                                    

Zahara bata taba jin nauyi irin na yau ba. Karasowa tayi a sanyaye ta gaishe su da siririyar murya. Tambayoyi ne birjik a cikin kanta wanda ta gagara amsa su...

“Zo ki zauna 'yata, bari na kawo abin sha.”
Tashi Mama tayi ta nufi hanyar kitchen. Da kallo Zahara ta bita kafin ta yanke shawarar zaunawa domin jin me ke tafe dashi. Karasawa tayi a hankali ta zauna kusa da yayan ta da ta jima rabon ta da shi. Koda ta zauna, suka fara magana. Ji tayi suna maganar zane (art), suna fadar wasu abubuwa da bata taba jin su ba a rayuwar ta. A bakin Kamal, ba abin mamaki bane, domin ganin zanukan dake cikin falon sa, ta tabbatar shi mai son zane ne amma bata taba tunanin yayan ta yasan wani abu ba a harkar zane.

Mama ce ta dawo dauke da jus da ruwa, kama mata Zahara tayi wajen zubawa su Kamal. A yanda take a rikice, addu'a take kar ta barar da lemun. Bayan ta zuba musu lemun, Mama tayi shigewar ta daki. Yayan ta kuma baida niyyar tashi ya barta tare da Kamal. Duk da ba wasu makusanta bane sosai ita da yayan nata, amma kowa a gidan yasan yanda yake bata kariya. Bayan wasu mintuna, ya yanke shawarar basu wuri.

Kamal shan lemun sa yake cikin kwanciyar hankali, ita kuwa na ta kokarin ganin ta sarrafa tambayar da take son yi masa. Jira take har ya gama shan lemun, bai kuwa bata lokaci ba ya ajiye kofin.

“Ya kike?” Ya tambaye ta yana kallon ta.

“Lafiya lau...”

Tayi niyyar yi masa tambayoyin amma kamar an toshe mata baki. Sunkuyar da kanta tayi, domin bata iya jure kallon sa... bare kuma da yace yana son auren ta.

“Na sani, da na sanar da ke kafin nazo gidan ku amma kuma bana son ki ki karba ta. Nazo ne kawai na gabatar da kaina gidan ku, domin nuna da gaske nake ba da wasa ba. Abinda kika fada min rannan yasa nayi nazari sosai. Bai dace ki yarda da ni ba, alhali bamu wani san juna ba. Ba zan takura ki ba, domin ki aminta da ni. Nasan kina da tambayoyi da dama, ki sani zaki iya fada min komai. Zan kokarta ganin na amsa duk wasu tambayoyin ki.”

Shuru yayi kafin ya cigaba
“Kuma bana son kiyi tunanin zuwa gidan ku da nayi saboda wata manufa ce ta daban. Idan kina so, ba zan sake zuwa ba, har sai idan ke kika ce nazo.”

Sauraron shi take da kyau kuma ta kasa daina zuzuta kanta kan cewa yayi wannan tattakin ne saboda ita, domin tabbatar mata da gaske yake. Ba zata iya cewa ba ta yarda dashi, amma tasan ba yanda za'a yi ya dinga duk wannan kan abinda baida muhimmanci a wajen sa.

“Me yasa ni? Me yasa sai ni kake son aure?”

“Ba zan iya amsa wannan tambayar taki ba Zahara...”

Tana jin dadin yanda yake kiran sunan ta.. cike da yanga da dadin ji.

“Ba zan iya amsa tambayar ki ba, domin ni kaina bani da amsar ta. Ba zan ce ina miki mahaukacin son nan domin idan na fadi hakan nayi karya, amma kina daukar hankali na sosai. A da ina tunanin hakan a matsayin birgeni kawai kike, amma na gane yafi hakan. Ni ba yaro bane, ba wai dan kina daukar hankali na ba zan yi wata alaka da ke, mu rabu bayan na samu wacce nake so. Addini na yayi min hani da yin hakan. Kina daukar hankali na ne kawai, domin kamar yanda kika ce bamu wani san juna ba. Dan haka zan yi kamar yanda masu cewa soyayya wata aba ce dake ginuwa ta hanyar sanin masoyi, sanin halin sa har ma da kurakuran sa. Dan haka ina son sanin wacece ke kuma idan kema a lokacin kin ga wani abun da yayi miki game da ni. Ki sanar da ni zan zo na nemi auren ki.”

Shuru yayi domin barin ta taji da abinda ya koro mata.

“Of course, idan baki da ra'ayin yin hakan, zan fahimta. Zan ji ba dadi amma zan fahimta, zan yi kokari ganin ban dauki abun da nauyi ba. Ina son kiyi tunani sannan ki fada min abinda kika yanke. Waya ta a kunne take a koda yaushe, zaki iya kira na kowanne lokaci, a lokacin da kika so, zan kasance cikin kaguwar jin amsar ki da sa ran ki amince.” Ya fada da dan guntun murmushi.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now