CHAPTER 28

147 27 2
                                    


Zuciyar Zahara bugawa take da sauri-sauri, cikin ƙanƙanin lokaci ta daina jin duk wani sauti da ke kewaye da ita. Idanunta sun ƙafe akan masoyan guda biyu.

Abinda yake yi kenan duk wannan lokacin? Ta tambayi kanta. Soyayya yake da best friend ɗinshi ni kuwa ya jefar da ni babu labarinsa. Hakan zai yi min kenan? Ya gama amfani da ni ya jefar. Duk wannan tunanin Zahara ce ke yin sa ne.

Maryam da mamakin ganin wani abu ya ɗauke hankalin ƙawarta, ta bi inda Zahara take kallo da kallo. Nan ita ma ta ga tashin hankalin da ya ɗauki hankalin ƙawarta. Ta ji tsoro na ɗan lokaci. Ita da ta kawo ta nan dan ta sauya mata tunani. Bata taɓa tunanin irin wannan coincidence ɗin zai faru ba. Gyara nustuwarta tayi sannan ta ɗan zunguri Zahara a ƙafa. Ɗan zabura Zahara tayi tare da dawowa daga duniyar tunani.

Maryam fiddo wayarta tayi ta yiwa Zahara text : Sakarai ne, please.. Ki daina kallon su. Kar ki zubar da ajinki, mun zo nan ne dan nishadi.

Karanta saƙon Zahara tayi ba tare da tace komai ba. Tasan ƙawarta tana da gaskiya amma ba zata iya controling damuwar da ta zo ta mamaye ta ba.

“Me kuke kitsawa ne ƴan mata? Na ga lokaci guda kun yi shuru.” Cewar Habib cikin sigar zolaya.

Maryam kallon ƙawarta tayi. Nan take ta fahimci abinda ƙawar tata take nufi. Gyaɗa kai tayi tare da cewa
“Muna tambayar abinda ya kamata ayi oda ne."

Murmushi Habib ya yiwa Zahara kuma maganarta ta bashi dariya. A ranshi yana tunanin sanyi sanyi gare ta ko kuma a takure take saboda yanzu ne suka huɗu.

“Toh me kuke so a kawo muku? Ni ina son cin abinci sosai domin kuwa yunwa nake ji. Tsawon kwanaki kenan ban samu cin abinci ba sosai sakamakon aiki."

Dariya Mansoor yayi tare da cewa
“Kai dai abokina faɗi gaskiya baka son su ce maka acici. Na fa sanka."

“Barshi ya yi magana dear. Ai Zahara kaɗai zai wayancewa a nan. Mu mun sanshi." Cewar Maryam.

“Kar ki saurare su Zahara. Daman sun shirya tarar min yau, amma nasan ba zaki yarda ba."

“Dole akwai dalili idan sun ce maka acici.” Zahara ta faɗa tare da yin murmushin dole da mazajen biyu kaɗai ne ba zasu gane ba.

“A'a Zahara ba zaki biye musu ba kema. Three against one, akwai zalunci a ciki!"

“Kana da gaskiya, dan haka na koma tsaginka. Nasan Maryam da Mansoor suna jin daɗin sako mutum gaba."

“Yauwa kinga zai zama mu biyu against the world, babu wanda zai iya tsaida mu."

Nishaɗi ne ya kewaye table ɗin saidai Zahara ba zata iya hana kanta tunanin Kamal ba. Tana iya ƙoƙarinta ganin ta hana kanta kallon inda suke amma akai-akai tana juyawa na wasu ƴan daƙiƙu dan ta ƙara tabbatarwa kanta da tsohon saurayinta ne. A duk lokacin da ta kalle su kuma ta ga yanda Kamal yake washe baki, sai ta ji tana nadamar yarda da shi da tayi. Bata ganin fuskar Khadija amma Zahara ta tabbatar tana cikin farin ciki. Khadija ta jima tana nuna mata Kamal nata ne kuma su biyu ko ba daɗe zasu ƙare a tare. A baya ta ɗauka kawai farfaganda ne na ƙawa mai kishi amma daga ƙarshe ta gane gaskiya. Kamal dama cen yana son bestie ɗinsa, amma sai da ya fara soyayya da Zahara kafin ya fahimci hakan.

Zahara bata daina yiwa ƙanta tambayoyi ba kuma daga ƙarshe ta fahimci kasantuwar masoyan a wurin ba ƙaramin cutar da ita yake ba. Dan haka ta ji babu abinda take so da wuce zuwa gida, bata ɓata lokaci ba wajen fahimtar da ƙawarta. Sake turo mata text Maryam tayi :

« Na rantse miki Zahara, idan kika bar restaurant ɗin nan, ba ni ba ke. Haka zaki dinga guduwa duk lokacin da kika haɗu da shi wani wuri? Ina kika kai ajinki da mutuncinki? Ina son ki share su kiyi kamar baki taɓa sanin su ba. Su gasu cen suna nishaɗinsu ke kuma kin zo kin wani takure kanki. Kiyi haƙuri ki danne ki cigaba da biyewa shirmen Habib domin yafi wannan sakaren Kamal ɗin. »

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Onde histórias criam vida. Descubra agora