CHAPTER 18

284 32 8
                                    



ZAHARA

Koda suka isa gidan Kamal, yayi mata nuni da ta zauna. Ajiye files din tayi bisa center table, ta fara aikin gyaren su kafin ya dawo. Dawowa yayi falon, ya sauyo kayan jikin sa, sannan yaje ya kawo mata abin sha duk da tace masa bata jin kishi. Bayan anyi haka, ya kama mata suka fara gyara documents din. Sai wajen karfe tara na dare sannan suka kare.

“Bari na hada wani abun da zamu ci.” Cewar Kamal. Ita kuwa Zahara gida take son zuwa ganin har dare ya fara yi.

“Nagode, amma gida zan je, bana son hankalin mama ya tashi. Domin ban fada mata zan kai warhaka ba.”

Mikewa yayi tare da ce mata ba zai dau lokaci ba, zai dafa wani abun marar nauyi ne. Ya fada ba tare da ya jira jin me zata ce ba, ya shiga kitchen.

Yanke shawarar kara yan mintuna tayi, da wannan damar tayi amfani ta shiga gyara wasu documents din.

Mintuna da dama suka zo suka wuce, amma Zahara bata ga Kamal ba, saidai motsi da take jiyowa daga kitchen, gajiya tayi da jira har ta kai ga tashi domin leka shi. Dariya ta kusan kwace mata lokacin da ta tarar dashi ya rike murfin tukunya da niyyar garkuwa da shi kar mai ya waltsar masa. Fiddo farfesun kaza yayi daga cikin freezer, yana kokarin soyawa.

“Kar ki karaso nan, dan zaki kone.” Cewar Kamal.

“Kawo, bari inyi..” Zahara tace tana mai kokarin karasawa.

“A'a.. kar ki matso dan zaki kone. Zan yi kar ki damu.”

“Ba lallai mu samun cin abun nan ba a yanda yake yi, bari ni zan yi ka yarda da ni.” Zahara ta fada tana mai karbar murfin tukunyar daga hannun sa. Dan ja baya yayi kafin ya yarda ya bar mata.

Sai da ta jira man ya daina turiri sannan ta kalle shi, tana tunanin reaction din da yake jira kenan domin dan murmushi yayi mata. Ita kuwa tayi sauri ta mayar da hankalin ta kan suyar farfesun kafin ta sume dan kunya.

Nacewa yayi sai yayi miyar farfesun, ita kuwa ta cigaba da suyar. Suna cikin shirya dinner, suka ji ana knocking kofa. Annurin fuskar sa ne ya sauya zuwa wacce ke dan ba Zahara tsoro. Wanke hannu yayi sannan yaje ya bude kofar.

“Me kika zo yi nan?” Zahara taji ya fada amma bata jin me dayan ke cewa.

Ji tayi an rufe kofa, taji sautin tafiya na nufo inda take. Cokalin dake hannunta ta damke sosai, tana tunanin ko mahaifiyar su Kamal ce. Har ta fara tunanin kunyar da zata kwasa idan ta hada ido da mahaifiyar Kamal. Wani tunani zata yi a kanta? Ta ganta tsamo tsamo cikin gidan danta a daidai wannan lokacin, ba wata uwa da zata yarda da wannan. Duk da ba komai suke aikatawa ba, ba zata fahimci hakan ba ita. Wayyo Allah, yanzu ya zata yi? Da tun dazu tayi tafiyar ta amma ta biyewa son zuciyar ta na kara son kasancewa da Kamal.

Saidai tsoron Zahara ya ragu lokacin da taga wata matashiyar budurwa ce ta shigo kitchen din. Kusan farin ciki ne ya saukarwa Zahara ganin ba daya daga cikin yan gidan su Kamal bane. Amma sai ta fara tambayar kanta wannan kuma wacece kuma me take yi nan a wannan lokacin?

“Ooh kenan da wannan yarinyar ce kake cin amanata?”

Wani irin bugu zuciyar Zahara tayi, kafafuwanta suka yi sanyi, hannuwanta suka hau bari. A ranta tace kenan yana da budurwa.

“Hafsat stop.” Kamal ya fada yana shigowa cikin kitchen din shima. Zahara tayi zaton zai mata bayanin dalilin da yasa yake kulata alhali yana da budurwa, amma sai taga ya saki fuska ba tare da ya kula wacce ya kira da Hafsat ba.

Yanada kwarin gwiwa har haka? Dole ma tayi tafiyar ta gida ! A hankali ta ajiye cokalin hannunta saidai a daidai lokacin wacce ya kira da Hafsat ta tuntsure da dariya.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now