“Zahara? Ga Sheikh Said nan ya zo.” Mama ta sanar da ita.
Kwance Zahara take bisa gadonta, ba bacci take ba tana nazarin rayuwarta ne...gobenta..ta yaya zata fita daga wannan al'amarin. Maganar mahaifiyarta ce ta dawo da ita daga duniyar da ta shiga.
“Ok, zan yi alwala kafin nan.” Ta ce wa Mama.
Gyaɗa mata kai Mama ta yi sannan ta fita. Ta lura a sannu ƴarta na samun sauƙi. Karatun Malam yana taimaka mata sosai, tana fatan ta samu warakar wannan tsoron na fita.
A ɓangaren na Zahara, ta ja numfashi karo na barkatai gaban madubi. Lokacin da ta ga gashin kanta da take matuƙar so, da yanzu ya fara tasowa, ta fahimci Amriya ɓarna ba ta iya tunani ba har ma da ta jiki ta yi mata. Tun bayan da ta dawo hayyacinta ta nemi da Mama ta siyo mata kayan gyaran gashi.
Tana ji a jikinta ta ketare abubuwa da dama, kamar wacce ta daɗe cikin doguwar suma. A koda yaushe tana ƙoƙarin tuna abubuwan da suka faru amma ta kasa. Daga ƙarshe ta yanke wata ƙila ƙwaƙwalwarta ce ke ƙoƙarin kare ta daga tuna abubuwan da suka faru a baya.
Babban abun shi ne bata san ina alaƙarta da Kamal ta kwana ba. Ana yawan faɗa mata irin ƙoƙarin da ya yi wajen taimaka mata amma ita har yau ta kasa samun kuzarin tunkarar shi har ta yi masa godiya. Tana jin tsoro amma na me? Bata sani ba. Abinda kawai ta sani bata shirya haɗuwa da shi ba.
Alwala Zahara ta ida, ta saka dogon hijabi da ya saukar mata har ƙasa. Ta fito sannan ta rufe ɗakinta kafin ta nufi falo. Ta tarar da Malam kamar koda yaushe zaune kan ɗaya daga cikin kujerun falon da ƙur'ani a hannunsa.
“Assalamu alaykum.” Zahara ta yi masa sallama kai ƙasa koda ta shigo falon.
Sheikh Said ya amsa sallamar sannan ya ce ta zauna zasu fara karatun yanzu. Tambayar ta ya yi jiki da kuma ko tana ganin wani abu da ba daidai ba ko miyagun mafarkai. Ya kuma tambaye ta idan tana yin addu'o'in da ya bata.
Zaunawa Zahara ta yi ƙasa kafin ta bashi amsa da komai lafiya, babu wani abu da take gani kuma tana yin addu'o'in da ya bata kamar yanda yace.
“Masha Allah hakan ya yi kyau, kuma kar ki dena domin su ne makamai akan sheɗanu.”
“Insha Allahu Malam.” Zahara ta faɗa.
Sheikh Said ya ce zai fara karatu.. ya fara da bismillah.
Gyaɗa kai Zahara ta yi sannan ta kasa kunne tana saurare. Kamar koda yaushe idan Sheikh Said na karatu ta kan ji duk jikinta yayi sanyi zuciyarta ta cika da farinciki. Kalamansa na ratsa ko'ina na jikinta kuma sai ta ji duk wata fargaba da tsoro sun ƙaura daga gare ta. Karatun ya ɗauki mintuna ashirin kamar kullum. Bayan ya ida Sheikh Said ya tambayi Zahara.
“Yaya kike ji?”
Zahara da ta rufe idanunta ta buɗe su.
“Lafiya lau alhamdulillahi.” Ta bashi amsa.
“Masha Allah.. mun kusa tsayar da karatun amma zaki iya cigaba da yi kullum da kanki, haka zaki iya sauraron wasu ruqyoyin a youtube nan ma wata riba ce. Amma kafin mu ida, akwai abinda nake son na tambaye ki.”
“Na'am?”
“Hadizatu tna son yin magana da ke.”
“Hadizatu?” Zahara ta maimata tana bincikar ƙwaƙwalwarta neman fuskar me wannan sunan.
“Eh, Amriya sunanta yanzu Haduzatu. Zan iya tabbatar miki da ta musulunta kuma tana gudunar da addininta yanda ya kamata amma tana son yin magana da ke kafin ta ɓace daga rayuwarki baki ɗaya.”
Jin sunanta kaɗai ya isa ya tsorata Zahara. Tsoro ne fal a cikinta da kuma tunani iri-iri. Har tana tunanin Amriya ke juya tunanin Sheikh ba wai ta shiryu ba.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
KorkuLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...