CHAPTER 17

200 33 3
                                    


ZAHARA

Koda ta koma gida, wanka ta shiga tati. Biki yayi biki an kuma watse lafiya. An kai amarya Maryam gidan mijin ta amma kuma sai da su Zahara suka tsaya suka gyara gidan su Maryam din kafin su koma gidajen su.

Abinda ya faru a daren nan ba karamin tayar mata da hankali yayi ba, a ranar bikin kasa komai tayi illa tunani. Tana tsoron fada ne amma tasan aikin Amriya ne, duk da tsoho yace ba zata sake dawowa ba. Koma dai meye a yanda take, wata kila ma kawai imagination ne irin nata. Kuma layar da Mama ta bata, har yanzu tana daure a hannun ta. Abinda yasa daga baya ta dena tunanin Amriya, hankalin ta ne ya koma ga Kamal da duk yinin yau bai kira ta ba.

Bata daina duba wayar ta ba, kuma a duk lokacin ta duba bata ga sakon shi ba sai taji yar damuwa a ranta. Haka bata daina dubawa ko matsalar network ne ko na wayar. Domin bai taba tsallake rana bai turo mata texte ba dan jin ya take. Har sai da ta fara tunanin kiran sa jin me yake yi kuma me yasa bai kira ta ba, amma ta kasa samun kozarin yin hakan.

A kamfani kuwa Mr. Ammar aiki yake ba hutu, haka ma'aikatan ma bai barsu ba. Dukan su dole suyi aiki da irin salon yake so, Zahara dake tunanin yanayin sa zai dawo daidai, tana jin kamar kara tabarbarewa ma yayi. Duk safe, idan yazo tana lura yanayin yanda yake magana da yanayin al'amuran sa babu abinda ya sauya. Zaman kamfanin ya rage dadi ga Zahara. Daman lokacin da aka dauke ta aiki a kamfanin, ba dan tana so ba amma tuna kyan hali da raha na Mr. Ammar yana sa taji kwarin gwiwar cigaba da aikin. Hakan nasa taji  son zuwa ta tunkari Salmah amma bata tunanin zai iya sauya wani abu kamar yanda Kamal ya fada mata.

Lokacin da ta fito daga bathroom, taga message din Farida, tana tambayar ta idan bata biyo da gyalen ta ba. Dubawa Zahara tayi cikin jakar ta bata ga gyalen ba. Ta kira ta domin sanar da ita.

“Ok, kar ki damu nasan ko gidan Maryam na baro shi. Gashi ina jin wahalar komawa.”

“Zan iya zuwa na dubo miki shi, idan kina so.”

“No, it's not urgent. Toh ya kike ya gajiyar biki kuma?”

“Lafiya lau, yanzu na fito daga wanka ma. Ina son na kwanta tun yanzu dan na tashi da wuri insha Allah.”

“Ok, bari na barki ki huta.  Nace ko gobe kina da dama muje restaurant?” Cewar Farida.

“Bayan kin sauko daga aiki.” Ta kara da hakan. “Nasan zaki yi mamaki amma akwai abinda nake son fada miki.”

Eh da mamaki jin hakan daga bakin ta, amma Zahara ta amince ko dan jin me zata fada mata goben.

“Ok, zan I would be available zuwa karfe bakwai na yamma insha Allah.”

“Cool, zan kira ki kafin muje akwai inda nake son mu biya.”

“Ok, Allah ya kaimu.”

“Ameen, ok sai da safe.”

Koda Farida ta katse kiran. Zahara ta kwanta. Bata samun yin wani dogon tunani ba barci ya dauke ta. Washe gari, tayi shirin zuwa office. Yau sai da ta dan dauki lokaci tana shiryawa domin har yanzu barcin bai sake ta ba. Tana jin kamar barcin minti biyar kawai tayi, shi yasa tana zuwa ta tarar da Mr. Ammar har yazo. Kuma ta tarar da ya bar mata tulin aiki. Jakarta ta ajiye ta nufi office din sa domin gaishe shi.

“Kin zo? I hope kin samu bacci mai isar ki?” Mr. Ammar ya fada kuma ta gane akwai zolaya cikin maganar sa.

“I apologize for the delay..” Ta fada cike da jin kunya.

“Kar ki damu Zahara, amma ina son files din nan da ke bisa desk dinki su zama cikin shirin kafin yamma.”

Aikin yana da yawa kuma zai yi wuya ta karasa shi kafin yamma, amma wace ita tayi masa gardama a yanayin da yake ciki. Dan haka wucewa tayi ta hado masa coffee din shi sannan ta hau aiki.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now