CHAPTER 35

599 25 4
                                    





Zahara bata san ina take ba, bata san wace rana ba ce yau ko wane lokaci ne yanzu, abinda ta sani kawai tana wani guri ne...a cikin duniyar nan. A razane take sosai da yasa bata iya yin wani ƙwaƙwaran tunani. Tsawon kwanaki take nan, a cikin wannan ɗakin, bata cin komai, bata shan komai kuma abinda yafi bata mamaki shine bata jin yunwa. Bacci kawai take yi idan ta tashi da ƙyar take iya yin wani tunani. Tunanin tafiya gida ko kaɗan baya zuwa kanta.

Wannan ranar, wani abu ya sauya... Wannan ranar koda ta farka, ta ji alamun mutum kusa da ita saidai bata tsorata ba. Kamar ƙiftawar ido wata mata ta bayyana a gabanta. Ta gane Aisha ce, matashiyar matar nan da ta haɗu da ita bakin kogi ƴar ƙawar mahaifiyarta da aka ce ta rasu. Duk da kiɗemewar da take ciki, Zahara ta fahimci ko wa ke bayan duk wannan. Da sauri ta duba hannunta, nan ta ga babu laya ɗaure a hannunta. Komai ya dawo mata a bayyane yanzu.

“Kin tashi?” Amriya ta tambaye ta tana zaunawa kusa da ita.

Zahara so tayi ta tashi ta matsa daga inda Amriya take amma ta kasa. Murmushin Amriya ya tabbatar mata da ita ce silar sandarewarta.

“Me yasa kike son yin nesa da ni? Me yasa kike gudu na Zahara? Alhali inada kirki kuma babu abinda nake so face farin cikinki.”

Zahara bata ce komai ba sai ma ƙoƙarin karanto addu'o'i da ta yi domin kare kanta tunda babu abinda zata iya da ƙarfinta. Lokaci guda wani kuzari da bata san da shi ba ya ziyarci Zahara, ta tambaye ta :
“Me kike so da ni Amriya?”

Murmushi aljanar ta yi, kafin ta fara ɓaɓɓaka dariya.

“Wayyoh nii!” Amriya ta faɗa tana ƙoƙarin tsayar da dariyarta. “Kawai ina son na nuna miki ne, na nunawa sauran babu wanda ya isa ya ja da ni. Idan ina son abu, ina samun shi. Kawai ina son ki gane ba zaki iya guje min ba kuma ko ba daɗe ko ba jima zan zo na neme ki. Kin so ki guje min kuma ki halaka ni amma gashi na dawo da ƙarfi fiye da da.”

Shafa fuskar Zahara Amriya ta yi. Ita kuwa Zahara da sauri ta ja baya.

“Tsoro kike ji? Ki daina ! Ba zan cutar da ke ba, ban taɓa cutar da wanda yake tare da ni ba.”

“Kin yi kuskure, bana tare da ke kuma ba zan amince ki tsare ni nan kamar wata fursuna ba...”

Dariya Amriya ta yi, ita kuwa Zahara bata iya jurar ganin yanda Amriya ke nishaɗi.

“Na ga ko motsi baki iya yi, kamar ɓera haka kike cikin tarko. Ni kaɗai ce wacce nake iya fitar da ke daga nan. Saidai kin ga ni... bani da burin barin ki ki tafi.”

Miƙewa tsaye Amriya ta yi ta shiga zagayen ɗakin da babu komai cikinsa, sai baƙaƙen labulaye kuma Zahara ta kasa fahimtar me ya kawo wannan tarin labuyen alhali babu taga ko ɗaya.

“Ban san dalilin da yasa baku son na zauna cikin rayuwarku ba... Ni kawai ina son a so ni ne kamar yanda ya so ni...” Amriya ta faɗa tana kallon bango.

Zahara cikin shakku, tayi amfani da wannan damar domin ƙara sani game da wannan aljanar.

“Waye shi?” Zahara ta tambaye ta.

Amriya da ta faɗa duniyar tunani, tuna wasu abubuwa na wannan mutumin ya sa murmushi ya ƙwace mata.

“Kin san wani abu Zahara, mu aljanu muna da saurin manta abu amma ni yau tsawon ƙarnika da dama kenan amma na kasa mantawa. Na so shi, so ba kaɗan ba... amma suka raba ni da shi.”

Son jin labari irin na Zahara, yasa take son jin na Amriya.

“Zaki iya min bayani, wata ƙila na fahimci irin yanda kike ji.” Zahara ta faɗa.

Wani mugun kallo Amriya ta watsowa Zahara. “Ta yaya ke bil'adama zaki iya fahimtar abinda ni aljana nake ji. Duk haka kuke, munafukai kuma masu son kai ! Kasancewar ku halittun da Allah yafi so, ba shi ke baku damar ku cutar da mu ba.”

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now