CHAPTER 3

835 52 9
                                    

A WANI KAUYE MAI SUNA NA'IYA

Duka mutanen kauyen sun taru a bakin wata babbar bishiyar kuka. Yara da manya kowanne ya halarta kamar yanda aka bukata. Da ka kalli fuskokin su zaka san a tsorace suke, hatta da yara ma da ba fahimtar meke faruwa ba sosai suke. Addu'a mutanen kauyen suke ta yi ganin wannan tashin hankalin yazo karshe.

Wani tsoho da suke kira da MALAM SHEHU ne ya mike yana kokarin maido hankalin mutanen kauyen kansa.

"Ku saurare ni da kyau,bayan watanni da na kwashe ina bincike, daga karshe na gano inda Amriya take." Cewar Malam Shehu cikin daga murya yanda kowa zai jishi.

Wannan maganar kuwa da yayi, ta kara ninka tsoron da mutanen kauyen ke ji. Tsoro hade da yar nutsuwa ce ta ziyarci kowannen su. Ko ba komai yanzu suna da sa ran za'a kama Amriya kuma wadanda suka bata ta sanadiyyar ta su dawo.

Wata sanda da shi kadai yake iya daukan ta tsabar nauyi, Malam Shehu ya buga a kasa. Daga sandar nan da yake iya yi, yana da nasaba da karfin tsafin dake gare shi. Karar wannan sanda yasa kowa na kauyen ya nutsu baka jin ko motsin kuda. Malam Shehu ya cigaba da cewa :

"Wannan hatsabibiyar aljanar ta zalunci kowanne daga cikin ku. Kowa a kauyen nan babba da yaro yasan irin abinda ta aikata. Ni, Malam Shehu nayi alkawarin ba zan barta ta sha ba cikin sauki."

Nan fa wani surutun ya sake barkewa a wajen, wasu na murnar abinda Malam Shehu zai yiwa Amriya, wasu kuwa na ganin ba karamar kasada ta rasa rayuwa bace ja da wannan aljanar. Domin da yawa daga cikin su sun san wacece Amriya da abinda take iya yi. Ta wargaza rayuwar da yawa daga cikin yan kauyen nan na Na'iya : Kashe-kashe, sace masu dukiyoyi da albarkatun gona, da fitowa mutane dan ta haukata su ga duk wanda tsautsayi ya kaishi ya fito karfe taran dare.

"Kun tabbata zaku iya wannan sadaukarwar saboda wannan kauyen? Amriya batada digon tausayi ko kadan. Ba zata yi sanya ba wajen kashe mu baki daya. Kun fi kowa sanin wacece ita." Cewar wani tsoho daga cikin mutanen kauyen. Sai da Malam Shehu yaja dogon gemun sa kafin yace :

"Wata kila Amriya tana da karfi sosai, amma ku sani ba ni kadai bane a wannan yakin. Zan je birni kuma zan dawo da ita nan. Ku yarda dani."

Malam Shehu baya jin tsoron Amriya, domin yasan yanada aljanu wanda zasu taya shi yakar ta. Sa'ar dake gare shi ita ce, Amriya ba wai mutane kadai ta zalunta ba. Tana da makiya da dama anan, haka ma a duniyar su. Da yawan aljanu burin su ganin mutuwarta. Malam Shehu shine wanda suke tunnin zai kawo karshen wannan hatsabibiyar anan duniya.

"Ka nemota Malam, tunda ta tafi 'yata ta haukace baki daya. Kowa a kauyen nan tsoron 'yata yake yanzu, alhali a da tafi kowacce yarinya kyau da farin jini a kauyen nan. Naje wajen duk malammai da bokayen makotan kauyen mu amma abu daya suke fada min, Amriya ce kawai zata iya warkar da ita. Dan Allah Malam Shehu ka taimaka mini."

Cewar Wata mata da kowa a kauyen yasanta saboda haukan 'yarta. Durkushe take gaban Malam Shehu tana rokon shi da iya karfinta da ya taimake ta. Kowa a wajen yaji tausayin ta.

"Ni, 'yata ta 6ace kimanin watanni uku. Hauka ta fara kafin daga baya ta gudu cikin daji. Tun daga wannan ranar babu wanda ya kara jin labarin ta, kuma mutane suke tsoron zuwa wannan dajin."

Wata matar ce tazo bayan ta farkon, tana bada labarin kowa sai girgiza kai yake dan tausayawa. Kowa yasan yanda 'yarta da ta bace take da nutsuwa ga hankali. Kyakyawa ce sosai yarinyar ga kuma manema aure da dama. Har ma ana shirye-shiryen auren ta. Sai dai aka wayi gari aka ganta ta canza, tana biyar maza, daga baya kuma ta koma tana kwana ita kadai waje, alhali lokacin kowa na cikin gida gudun haduwa da Amriya. Daga nan yarinyar ta fara hauka, tana duka da jifan duk wanda yabi ta inda take, har wata rana aka wayi gari ta shiga daji. Bata kara dawowa ba.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now