“Hello, ko ka samu labarin abinda ke faruwa?” Kamal ya tambayi ɗan uwansa Ammar.
Yanzu ya gama waya da mahaifiyarsu, wacce bata yin ƙasa a gwiwa wajen sanar da shi duk wani motsi na mahaifinsu.
Wannan karon, Kamal bai san ya zai tarbi wannan labarin ba. Yana so kawai adalci ya yi halinsa kuma ya girbi abinda ya shuka. Bai so wannan abun ya same shi ba.
“Adalcin Allah ne.” Ya faɗa a ransa.
“Are you here?” Daga wancen ɓangaren Ammar ya tambaye shi.
“Eh Ammar, sorry na yi nisa ne cikin tunani.”
“Na sani, na yi magana har sau biyu amma da alamu baka ji abinda na faɗa ba. Wane labari ne kake magana? Fatan dai ba wani mummunan labari ba ne?”
“Unfortunately yes, yanzu Mom ta kira ni. An ɗaga shari'a domin daddy bai da lafiya. Ya kamu da prostate cancer, yana mataki na huɗu.”
Ya zamana kai tsaye ne ya sanar da shi wannan labari, amma ba yanda ya iya bayan wannan. Dole ya faɗa masa domin ya fahimci abinda rashin lafiyar mahaifin nasu ke nufi.
“Ban yarda da wannan zancen ba. Na tabbatar wani makircin ne nasa ne dan ya gujewa hukuncin da ke jiran sa.”
“Kana tunanin haka ne?” Kamal ya tambaye shi.
“Na tabbatar!”
“Bana tunanin Mom zata yi ƙarya. Kuma ta faɗa min zata zo nan gidana yau. Ina so ka zo kai da Afnan domin ta yi mana bayanin komai a fayyace.”
“Kamal..”
“No Ammar, ina tunanin wannan abun ya isa haka. Mahaifiyarka ce, ba zaka iya cigaba da fushi da ita har abada ba.”
“Ni zan iya zuwa amma bana tunanin zan iya zuwa da Afnan. Bana tunanin ta shirya arangama da Mom. Ta cutar da mu sosai.”
“Ka yarda da ni kowa ya cutu a wannan labarin. Ina jiran ku ƙarfe biyar na yamma a gidana. Ya kamata mu yi magana a yi ta ta ƙare.”
“Za mu gani.” Ammar ya faɗa kafin ya katse kiran.
Koda Ammar ya katse kiran. Maryam ta kira shi. Tun jiya yake gwada kiran ta. Tsawon kwanaki kenan yake tunanin yanda zai yi wa Zahara magana. Daga ƙarshe, ya yanke shawarar yin magana da Maryam. Yana son yin magana da ita amma bai sani ba idan ita Zahara tana son maganar da shi. Ya yanke fara sharar fage da Maryam.
“Hello Kamal, sorry ina busy ne jiya.”
“Oh na fahimta, fatan dai ban takura ki ba?”
“No, I am available a yanzun shi yasa na kira ka. Yaya kake? An jima ban samu labarinka ba.” Ta ce da shi.
“Lafiya lau, ina nan. Ina ƙoƙarin gyara wata ƴar matsala ne amma na kira ki ne domin jin labarin Zahara kuma na tambaye ki wani abu.”
“Ina jin ka.”
“Kina tunanin zan iya zuwa na ga Zahara? Ina nufin... Ina fata ba zata damu ba sosai? Ban san me zan yi tunani ba, ina ɗari-ɗarin zuwa ganin ta. Ko ta yi maganata tun bayan da ta dawo hayyacinta?”
“Na tabbatar zata ji daɗin ganin ka, ko ba komai kana daga cikin mutanen da suka taimaka mata.”
“I don't know, ina shakka sosai.”
“Me kake ji wa tsoro?”
“Na yi mata laifi sosai, ina son zuwa na ganta amma ina tsoron ta ƙi sauraro na.”
“Idan baka gwada, ba zaka fita daga shakku ba. Ka je ka ganta ku yi magana.”
“Kinada gaskiya, zan saka rana mako mai zuwa sai na je.”
CZYTASZ
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
HorrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...