Ammar bai daina neman Salmah kowane lungu da sakon na garin ba. Haka bai daina kiran wayar ta ba da koda yaushe ake ce masa kashe take. Har kawar ta Khadija bata samun ta a waya. Wannan lamarin ba karamin tayar masa da hankali yayi ba, bai san me zai yi ba ko a ina zai neme ta ba. Gashi gobe zai koma company, bai san ko zai iya aje hankalin sa yayi aikin ba.Kafin yace zai aure ta, sai da ya fada mata shi bai damu da abinda tayi ba a baya, kuma har yanzu hakan yake tunani. Ya hadu da ita ya fara soyayya da ita, ta dalilin son da yake mata. Kara fadawa ma yayi sonta lokacin da ta bashi labarin rayuwar da tayi a baya. Eh tayi kura-kurai amma ta tuba ta daina, kuma Allah na son masu tuba.
Bai san ta yaya Mahaifiyar shi tayi wajen gano wannan sirrin da ya boye kasan zuciyar sa ba. Haka bai san ko Salmah zata yarda idan ya fada mata baida alaka da abinda mahaifiyar shi tayi mata, kuma zai yi iya kokarin sa ganin ya dawo da ita. Bai taba kaunar wata 'ya mace ba kamar yanda yake kaunar ta, kuma zai iya shiga mawuyacin hali idan ya rasa ta. Mahaifiyar sa, mahaifiyar sa ce ba yanda za'a yi ya iya saba mata, amma tana sa masa matsi ba kamar dan uwan sa ba. Shima yana son yin gidan kansa ya koma kamar Kamal, amma ba zai iya barin mahaifiyar su ita kadai ba. Mahaifin su mai yawan tafiye tafiye ne, ita kuwa Mommy ta daina aiki, kullum tana gida. Dama dama da cikin kannenta wata ta bata rikon 'yarta Anifa, wacce take yanzu tamkar kanwa uwa daya uba daya a gare su. Ba zai iya tafiya ya bar su su kadai ba a gidan. Wannan ne yasa ya tsaya amma yana ganin hakan kusa zuwa karshe.
Yanke shawarar neman taimakon yayan sa Kamal yayi, domin yana da hanyoyi da dama a wajen manyan mutane. Wata kila ya iya samo masa private detective da zai nemo masa inda take. Bai yarda da yan sanda ba, zasu bata masa lokaci ne daga karshe suce babu abinda zasu iya akan batan ta.
A cikin motar sa, kokarin kiran Kamal yake amma baya dauka. Bayan wasu yan mintuna sai gashi ya sake kiran shi.
“Hello..” Kamal ya fara magana.
“Hello bro ya kake? I really need you. Kana ina ne yanzu?”
“Ina gida, zaka zo ne?”
“Eh.” Ya bashi amsa kafin ya juya motar sa zuwa hanyar gidan Kamal.
Lokacin da Ammar ya karaso gidan, ya tarar da Kamal yana cikin painting wani zane.
“Salmah ta bata, na kasa samun ta a waya. Kuma na duba ko'ina ban ganta ba. Hankali na ya tashi. Bata kira ka ba?”
Ajiye brushes na zanen sa yayi, ya juyo yana fuskantar Ammar.
“Kaje gidan su ne? Ban sake ganin ta ba tun lokacin da kace na kai Zahara.” Cewar Kamal.
“Yaya Zarahan take? Ban je na ganta ba da duk wannan abun dake faruwa. Mom ta gano wasu abubuwa kan Salmah kuma hakan ba karamin tada kura yayi ba. Saboda hakan ne ta bata. Ni wallahi bansan abin yi ba.”
“Ka tambayi Khadija? Kaje gidan su? Ko kiran yan sanda muke yi?”
“Na duba ko ina na fada maka. Kuma bana son saka yan sanda a wannan lamarin. Na zo nan ne, ina son kayi min wani taimako.”
“Taimako? Zan iya taimaka maka wajen neman ta, amma bani da masaniya ko kadan akan inda take.”
“A'a ina son ka taimakamin wajen samun private detective.”
“Kana tunanin ta bace da gaske? Ba zamu iya jira na karin kwana daya ba? Ina da tabbacin tana son yin nesa da duk wannan ne, na wani lokaci, ina ganin ka daina daga hankalin ka haka. Rashin ganin ta yana da alaka da abinda ka fada min yanzu.”
“Wlh bro, ni ban san me zan yi ba yanzu.”
“Da farko, kayi kokarin samun nutsuwa. Mu karawa Salmah dan lokaci idan nan da zuwa gobe bata bayyana ba, sai mu sanar da yan sanda ko kuma mu nemi private detective.”
YOU ARE READING
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
HorrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...