Suna zuwa asibiti aka kwantar da shi. Sai da ta jira na wasu mintuna kafin aka ce ta shiga ta ganshi. Da ta shiga ta tarar wata nurse na saka masa ruwa. Nan take fada mata zai samu waware bayan anyi masa karin ruwan.
Zaunawa tayi kusa da shi.
“Ki je gida kafin dare ya kara yi sosai.” Ya fada da gajiyayiyar murya da alamun bacci.
“Tun dazu na kira Mama, tasan ina nan.”
“Ina son ki tsaya amma bana son ki tafi gida ke kadai bayan nayi bacci.”
“Ba zan tafi ba, kayi hutawar ka. Idan ka tashi zaka gan ni.”
“Kira Khadija ki ce mata taje gida. Duba cikin wayata zaki ga number ta.”
“Ok zan yi hakan daga baya. Ya jikin naka yanzu?” Ta tambaye shi.
“Abun mamaki na fara jin sauki. Ayyuka ne da dama nayi kwanan nan, kuma bana cin abinci sosai.”
“Iya wannan ne kawai?” Ta tambaye shi.
“Sai kuma wata matsala da ta taso gidan mu.”
“Ok zamu yi maganar daga baya, naga alamun bacci kake ji yanzu. Zan je na kira Khadijar ka.”
Dariya yayi sannan yace da ita.
“Wannan ba Zahara da na sani bace.”
Murmushi tayi itama sannan ta fita bayan ta dauki wayar shi. Kiran Khadija tayi. Ringing na farko ta dauka.
“Kana ina ne Kamal? Yanzu kusan awa daya da rabi kenan baka dawo ba.” Khadija ta fada rai a bace.
“Zahara ce.” Zahara ta bata amsa, haushi ne ya kara kama Khadija tace
“Me wayar Kamal take yi hannun ki?”“Yana asibiti ne."
“What? Me ya same shi? Sai da na fada masa ba idea bace mai kyau zuwa wajen ki a yanayin da yake ciki. A wace asibiti kuke?”
“Yace zaki iya tafiya gida, zaki iya ajiye makullen karkashin carpet.”
“Tambayar ki nake a wace asibiti kuke? Bana jin zan iya tafiya gida alhali bestie na yana kwance asibiti.”
“Ok, muna Shareef Hospital ta babban titin...”
Bata ma karasa magana ba, Khadija ta katse kiran. Zahara a ranta tace Kamal da kwashe-kwashen abokai yake, da alamu ba zasu jitu ita da Khadija ba.
Komawa tayi cikin dakin da Kamal yake kwance, ta tarar da nurse tace mata bata dade da fita ba yayi bacci, dan haka ta dan kishingida kan doguwar kujera kafin ya tashi.
Zahara na tunanin ta dan jima tana bacci domin dariyar da su Kamal ce suke yi ta tashe ta. Firfigit tayi ta tashi, nan taga Khadija har ta iso shima Kamal ya tashi daga baccin. Khadija na zaune bisa gadon kusa da Kamal. Kishi ne ya turnuke Zahara ganin kusancin dake tsakanin su.
“Sorry mun tashe ki?” Cewar Kamal.
“Ba komai, ban yi tunanin baccin zai dauke ni haka da sauri ba.”
“Zaki iya tafiya idan kina so, ni zan tsaya nan.” Cewar Khadija.
“No, na fadawa mahaifiya ta zan zauna nan.”
“Eh, amma kuma kin gaji.” Cewar Khadija. “Kar ki damu ni zan zauna, ba wani abu zan yiwa Kamal din ba.”
“Khadija...” Cewar Kamal yana harar ta.
“Ok, wasa nake."
“Ku je gida ku duka, ba zasu barku ku kwana nan ba.”
“Amma..."
ŞİMDİ OKUDUĞUN
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
KorkuLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...