Wani yanayi Zahara take ji... Wani yanayi na daban, ba zata iya faɗar ga irin yanayin da take ji ba. Kawai tana ji a jikinta akwai abinda ke shirin faruwa ko ya faru. A da idan tana jin irin haka ta san Amriya ce ke zuwa ko ta zo, amma yanzu tafi kowa sanin Amriya ta yi nesa da ita idan har da mugun nufi ne. Dan kar ta cigaba da tunanin abun yasa ta karɓi yin girki a hannun Mama.
Texte message ta gani na ɗaya daga cikin abokan aikinta yake tuna mata walimar da aka shirya gobe. Saidai Zahara ta riga da ta bashi amsarta, ba zata iya zuwa ba. Maryam ce ta yi ta takura mata da sai ta je ko Allah ya sa zata haɗu da wani a cen, ta juya babin «Kamal» baki ɗaya, saidai ko da ta ce hakan, Zahara a ranta ta ce bata sani ba idan tana son rufe babin... Daga ƙarshe dai ta yanke shawarar yi saidai furanni, ƙayatattun ƙananun kalamai da kuma chocolates ɗin da yake aiko mata suna sa koda yaushe ta yi ta tunaninsa. Kuma babban abun shi ne bata son kwata-kwata ya daina, duk wannan abubuwan da yake mata suna saka ta farin ciki. Kowa a wajen aikin nasu yasan da wannan aiken, kowa ya san cewa kullum sai an aikowa da Zahara da saƙo har ma suka fara wasar cankar me wannan ɓoyayyen saurayi nata zai aiko mata gobe.
Zahara ta san wannan abun ba mai ɗorewa ba ne, ya kamata ta yi masa magana a yi ta ta ƙare kafin yanke hukunci. Saidai ko ita kanta bata san ta yaya zata kawo ƙarshen wannan lamarin ba. Ta kasance a tsakiyar matsatsi biyu ne : Auren Kamal da kuma zama kishiyar Khadija ko mantawa da babinsa ta cigaba da rayuwarta. Maryam da a koda yaushe take bata shawarwari masu kyau ta ce ba zata iya mata zaɓi a madadadinta ba. Maganar da suka yi ce ta dawo mata yanzu
“Ni ba zan iya ce miki ki je ki yi aure ba, kuma ba zan iya ce miki ki manta da Kamal ba alhali nafi kowa sanin har yanzu kina son sa. Ba zan iya yi miki zaɓi a madadinki ba, ni abinda kawai nake so shi ne farin cikinki. Ina son ki kasance cikin farin ciki kuma ban sani ba idan wannan matar zata bar ki ki zauna lafiya ba idan kika auri Kamal.”
“Shikenan ba zan yi aure ba kenan?” Cewar Zahara.
“Zahara ni ba ke ba ce, kuma ke ma ba ni ba ce. Zan ƙara faɗa miki ba zan iya cewa kar ki yi aure ba. Kin fi kowa sanin irin son da kike wa wannan mutumin, idan kina son shi ki yi faɗa a kanshi, yanada ƴancin auren mata huɗu. Idan kina tunanin ba zaki kasance cikin farin ciki ba idan kin aure shi, ki manta da shi kawai. Ko ma dai meye, ki yi tunani mai kyau ki yanke hukuncin da zai kawo miki farin ciki mai tsayi.” Shawarar da ƙawarta ta bata kenan.
“Yanda nake jin kina magana, ina jin kamar kin fi son na manta da shi.”
“Eh amma ra'ayina baida muhimmanci, domin rayuwarki ce.”
“Ohh...It's hard .. really hard. Bugu da ƙari bana son barin rayuwata ta London, ina jin daɗin zamana a cen ba kaɗan ba.”
“Ba zaki koma rayuwa gaba ɗaya a cen ba dai ko?”
“A'a ko kaɗan idan na koma bai wuce na yi shekara uku zuwa huɗu na kammala karatuna da kuma ƙarasa ƙwarewar aiki a cen sai na dawo.”
“Idan kin yanke shawarar ba wa Kamal damarshi, na tabbatar zai goyi bayanki, na san yana son ki.”
“Kina ƙara rikita ni Maryam, mu bar zancen kawai.”
Ƙyalƙyacewa da dariya Maryam ta yi.
“Shikenan na yi shuru kuma na bar ki kiyi tunani. Rayuwarki ce, babu wanda zai ce miki ga yanda zaki yi ta.”
Girgiza kai Zahara ta yi, ta yanke shawarar yin sauri ta gama girkinta da wuri. Hirarsu ta ƙarshe ta ɗan saka ta murmushi kuma ta kwantar mata da hankali.
«Maryam tanada baiwar warkar da ita koda bata kusa da ita.» tunanin da take yi kenan.
Zuwa ƙarfe biyu ta gama girkinta. Ta kira Mama, Mama ta ce ta bari zata zuzzuba abincin hakan kuwa ya yiwa Zahara daɗi da ta yanke shawarar zuwa ta cigaba da gyara file ɗinta kafin monday. Yau muna Juma'a amma da yake babu abinda zata yi, shi yasa take son ta rage lokaci.
ESTÁS LEYENDO
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
TerrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...