Karo na farko bayan lokaci mai tsawo, yau taji tana son tafiya makaranta. Kwanakin nan da tayi cikin gida yasa tayi tunani sosai akan halin da take ciki, kuma hakan ya bata damar kula da kanta da kuma na ƙwaƙwalwarta amma rufe kai kullum a gida ya fara isar ta.
Kwance take bisa gado, tana tuna lokutan baya masu daɗi tare da ƙawayenta. Tun bayan abinda ya faru, tayi nesa da kusan duka mutanen da ta sani. A lokacin tana jinta cikin ƙazanta da ba zata bari ta shiga mutane ba. Kwanan nan kuwa da ta gane bai dace ta tsani kanta ba, son komawa school yazo mata...
Tana tsaka da tuna rayuwarta ta baya lokacin da bata da wata damuwa.. sautin tafiyar ɗan uwanta Ammar ya dawo da ita duniyar zahiri. Knocking ƙofar yayi tazo ta buɗe masa, bayan ya shigo ɗakin sun gaisa ya samu guri ya zauna. Sosai ɗan uwan nata ke kula da ita. Bata da fargabar komai idan yana kusa da ita. Bayan sun taɓa hira, Afnan ke faɗa masa tana son komawa school.
“Kina son komawa school?" Ammar ya tambaye ta yana fiddo ido tsabar mamaki.
Afnan ganin yanayin ɗan uwan nata yasa ta ƙyalƙyace da dariya sannan tace
“Akwai ka da abun dariya, fita fa kawai nace zan yi, amma duk ka tashi hankalinka haka."“Dole in tashi hankalina, ai wannan labari ne mai daɗi ! Ina nufin.. idan kin ce kina son zuwa school, saboda kin samu lafiya kuma kin shirya ! Ko ba haka bane?"
Gyaɗa masa kai Afnan tayi.
“Naji daɗi sosai da sosai." Cewar Ammar. “Zan iya samar miki malami nan gida idan kika ji ba zaki iya ba."
“A'a ! Ina son jarabawa, zan sanar da kai, idan na ga ba zan iya ba. Nayi alƙawari !”
“Kin tabbatar?" Ya tambaye ta.
“Eh, na tabbatar."
“Cool, toh yaushe zaki fara zuwa?"
“Daga gobe." Ta bashi amsa. “Friends ɗina zasu yi min bayanin abinda nayi missing. Na tabbatar ba zan sha wahala ba."
Washe gari Afnan, tayi sammakon tashi, domin shirin zuwa school. Farin ciki da fargaba take ji lokaci guda. Ta kasa daina yiwa kanta tambayar ta yaya zata yi idan taje gaban ajinsu. Ƙoƙarin ƙin yin tunanin tayi a halin yanzu.
Wannan karon cikakkiyar shigar hausawa tayi akan da da take cin gayunta. Tayi tunanin yin wannan shigar ba zai janyo hankalin mutane ba kanta, saidai koda Ammar ya sauke ta bakin ƙofar school ɗinsu, idanu suka yo kanta.
« Me yasa tayi irin wannan shigar? »
« Me yasa ta ɓace aka daina ganinta? »
« Ya naga tayi rama? »
« Wata ƙila ciki tayi »
« Wata ƙila wani makusancinta ta rasa. »Wannan kallon ƙurallar da ake yi mata ya biyo da irin waɗannan tambayoyin. Afnan ta ji ta a takure, ƙafafuwanta suka fara rawa. Cikin ikon Allah, wata ƙawar Afnan mai suna Azima da take zuwa kullum a makare sai gata ta ɓullo. Afnan ma tayi tunanin zuwa da wuri zai sa abinda yake faruwa yanzu kar ya faru.
“ƘAWATAAAAAA." Azima ta ƙwalla ƙara tare da rungume Afnan da ta kusan kada ta.
“Mahaukaciya, me yasa kika ɓace tsawon wannan lokacin ba labari? Hankalina ya tashi sosai wlh. Har nace sai na hukunta ki idan kin dawo, amma yanzu murna ba zata barni ba.”
“Ai kin bari nayi magana ko.” Afnan ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace kanta daga jikin ƙawarta.
“Toh ina sauraron ki. Bani labari." Cewar Azima.
“Yanzu muje wani guri inda babu hayaniya, na gaji da idanun mutanen nan."
“Shikenan muje."
“Kowa tambayar inda kike ake, har Anwar ma." Cewar Azima.
YOU ARE READING
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
HorrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...