Yau Ammar da wuri ya tashi daga aiki. Zahara bata nan yanzu dan haka wahalar ji da ayyuka a kwanakin nan yake. Hakan ne yasa ya ɗauki tsohon sakataren mahaifinsa da ke aiki yanzu a wani kamfanin domin ya taya shi. Da yake sakataren yanada ƙwazo sai ya zamana Ammar ya samu isasshen lokacin ji da wasu matsalolinsa na in da cen.
Yanke shawarar zuwa gidansa ya yi domin yin magana da Hafsat da kuma ganin ko ta dawo hayyacinta. Saidai lokacin da ya je gidan ya yi mamakin ganin Afnan ita kaɗai. Bai yi wani mamaki sosai ba, shi yasa ya yi abinda ya yi domin hana ta tafiya a halin da take ciki.
Kasa ɓoye fushinsa Ammar ya yi, ya sa ran ko magana su yi kafin ta yi tafiyarta. Ya ji haushi sosai da yasa ya sauke kan kanwarsa Afnan.
“Ko ƙoƙarin tsayar da ita da kin yi ai..” Ya ce wa Afnan cikin ɗaga murya.
Afnan da ke saka takalmi domin komawa school ta yi saurin ɗagowa jin abinda ɗan uwanta ya ce. Da sauri ita ma ta ce :
“Ta yaya zan iya tsayar da ita idan kai ma ka kasa? Ba ƙaramar yarinya ba ce, na yi ƙoƙarin lallaɓa ta amma ko kula ni bata yi ba.”“Ai da sai ki kira ni ki faɗa min. Abinda ya kamata ki yi Afnan ! Bansan me yake damun ki cikin kai ba.”
“Ni ce ko kuwa sauke fushinka kake a kaina? Ni zan tambayi me yake damun ka, matar nan bata son tsayawa nan, ina ga ya kamata ka yi tunani kuma ka shafa mata lafiya. Ka cece ta, toh me kuma kake so bayan wannan? Ta yi maka godiya? Idan baka fahimta ba, bari na sanar da kai, wannan yarinyar ta tsane ka. Ya kamata ka daina ƙoƙarin shi-shige mata.” Afnan ta faɗa masa.
Kalamanta sun shiga kunnuwan Ammar kuma sun ƙara haura fushinsa.
“Ki tafi daga nan kafin raina ya ƙara ɓaci.” Ammar ya ce wa Afnan ƙasa da murya.
“Eh ai haka zaka ce..” Cewar Afnan saidai duk da haka ta yanke tafiya ganin adadin yanda ta fusata yayan nata.
Rufe kansa Ammar ya yi cikin ɗakinsa. Rai a yamutse. Ya kasa fahimtar me yasa ransa ke ɓaci har haka. Ba ƙaunar juna suke ba tun asali amma me yasa ji daga bakin ƙanwarsa ya fusata shi haka? Yasan tsakanin shi da Hafsat ba wata ƙwaƙwarar soyayya ke akwai ba, kuma hakan bai dame shi ba. Saidai yau Ammar yana jin wani sauyi a cen cikin zuciyarsa.
“Na tabbatar tausayinta ne kawai..” Ya faɗa cikin ransa.
Bayan duk abinda ya faru da ita, tabbas ya ji tausayin ta. Wannan yasa yake ƙoƙarin ƙulla wata sabuwar alaƙa da ita.
“Ko ma dai meye Afnan tayi gaskiya. Na taimake ta, shikenan yanzu. Ya kamata in mayar da hankali ga rayuwata da kuma Shari'ar ƴar uwata. Wannan ne yafi muhimmanci.” Ya faɗa.
Bayan wasu kwanaki, Ammar ya kasa manta Hafsat. Yarinyar nan ta ƙi fita daga cikin kwanyarsa hakan kuma ya kusan mayar da shi mahaukaci. Kamar wanda aka yiwa sihiri, hargitsi ne cikin kansa. Kuma babban abun, har yau yana tunanin iya tausayinta ne kawai yake ji. Wata rana, ya yanke zuwa gidansu Hafsat domin ganin yanda take. Idan ya tabbatar tana nan lafiya wata ƙila ya ɗan samu sukuni cikin ransa. Da wannan tunanin Ammar ya tafi neman Hafsat.
Mahaifiyar Hafsat tayi mamaki saidai tayi murna da ganin Ammar. Ƴarta kusan bata cin komai kuma kullum rufe kanta take cikin ɗaki, bata fitowa kuma ta daina zuwa wajen aiki. Kowa damuwar halin da take ciki yake, amma ita bata yi komai da zata kwantar wa da dangin nata hankali ba.
“Shigo ɗana, ya kake?”
“Lafiya lau nake Mama, fatan kuma haka?” Cewar Ammar yayin da yake bin bayan mahaifiyar Hafsat zuwa falo.
“Lafiya lau Alhamdulillah, ya momynka?” Ta tambaye shi.
“Tana nan lafiya.”
Ammar ya bata amsa a gaggauce da gudun kar ya tuna memories masu ɗaci.
YOU ARE READING
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
HorrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...