Zahara ce tsaye a jikin madubin window tana kallon masoyan biyu dake wajen parking. Mr. Amar ne tare da budurwar sa wacce zai aura, ke ta shan firar soyayyar su. Zahara ba wai kishi bane take ji yayin kallon su, face wata murya dake ta maimaita mata a zuciya cewa wannan yarinyar ba finta kyau tayi ba. Dan haka ita ta cancanci wannan gurbi na auren Mr. Amar ba ita. Tunani take ta yanda zata yi ta bata wannan yarinya a idon Amar, amma ta kasa samun wata hanya domin bata santa ba kuma wannan karon ne ta fara ganin ta. Amma daga karshe yankewa tayi baka bukatar dalili kafin ka muzgunawa wani. Tabbatarwa kanta kuma tayi, ba wai wani abun zata yi mata ba, kawai zata yi yaki ne ganin ta maye gurbinta a wajen Amar.
"Lafiya kike ta faman murmushi?" Zahara taji an fada a bayanta.
Juyowa tayi taga Sarat ce da murmushinta na mugunta. Juyawa tayi ta cigaba da kallon masoyan da suka bar wajen parking din zuwa cafeteria. Sarat ganin sauyawar Zahara ta shiga dari-dari da ita, bama Sarat kadai ba duk wani ma'aikaci a kamfanin tsoron Zahara yake yanzu.
"Wai murmushin me kike haka?" Sarat ta sake tambayar Zahara tana mai matsowa ita ma tana leka window dan ganin me Zahara take kallo. Ganin Mr. Amar da budurwar sa dariyar keta ta kwace mata.
"Yanzu na gane dalilin kin kallo na da yake. Allah yasa na hakura da dadewa."
"Yeah, gwara da kika yi hakan.." Cewar Zahara ba tare da ta kalli Sarat ba.
"Please ko zaki kama min na gyara library? Hajiya Rabi ce ta shiga, tana ta matsifa wai sai na gyara."
"Ba zan iya ba, bana da ra'ayi." Cewar Zahara har yanzu hankalin ta naga masoyan dake kokarin shiga Cafeteria.
"You are so strange kwanan nan, sai nake ji kamar ba ke ba."
"Allah ko?" Cewar Zahara ba tare da ta fahimci me Sarat take fada ba.
"Eh, kamar an sauya ki da wata macen."
"Kawai dan nace ba zan taya ki ba?" Zahara ta fada wannan karon ta juyo tana fuskantar Sarat.
"A'a, ina maganar sauyin da kika samu ne, domin a da ba haka kike ba..."
"Toh wa ya sani ko ni wata ce ba Zahara da kika sani ba?" Ta fada da alamun ta fara kosawa da Sarat din.
"Ha, ai hakan ba zai yiwu ba, yanzu dai kin taya ni ko a'a ba wani lokaci ba gare ni?" Cewar Sarat.
Zahara matsowa tayi kusa da Sarat ba tare da ta daina kallon ta ba. Tsoro ne ya kama Sarat ganin irin kallon da Zahara ke yi mata mai ban tsoro. Baya-baya ta shiga yi, amma Zahara ta sa hannu ta kamo kuncin ta, ta matse. Yar karar wahala Sarat ta saki tsabar zafi.
"Kin san wani abu Sarat? Ki bini a sannu. Bana son zama muguwa a kanki, kar ki tilasta ni na zama. Kina jina?"
Kokarin kwatar kanta Sarat take amma ta kasa sakamakon karfin Zahara kamar ba na mutum ba. Kuka kawai ta iya yi domin kumatun ta suna mata zafi sosai.
"Sarat kin ji ni ko baki ji ba?"
Da sauri Sarat ta gyada kan wahala. Ita kuwa Zahara murmushi ta sakar mata kamar komai bai faru ba. Sarat tsoro ne fal a ranta. Kallon Zahara take tana shafa kuncin ta. Takaici na cinta a rashin wani katabus akan Zahara da tayi. Ba wai iya karfin dantse Zahara ta nuna mata ba, har da na kwarjini domin Zahara ta cika mata idanu ta yanda zuciyar ta ke wani irin bugu wanda yasa da dafen bango ta bar wajen Zaharar.
A bangaren Mr. Amar Yusuf
Ya hadu da Salmah ne ta dalilin yayan shi Kamal. A wata rana ne, da Kamal yake dawowa daga wata tafiya ta tsawon wasu watanni da yayi. Amar ya shirya domin zuwa airport dauko shi. Da zuwan sa ya tarar da Kamal yana magana da wasu yan mata guda biyu, abinda ya bashi mamaki Kamal bai cika yawan magana ba, indai ba akan aiki bane, kuma a lokacin yana da tabbacin ba maganar aiki bane yake da yan matan. Matsawa Amar yayi kusa da su kuma ya tabbatar da yayan ne nashi.
YOU ARE READING
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
HorrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...