CHAPTER 37

358 12 2
                                    

Kamal ne zaune gaban Zahara da ke bacci cikin tsanake amma shi ya kurawa bango ido. Yana tuna maganarsu shi da Khadija.

“Ki faɗa min idan kinada wani abu a cikin wannan lamarin Khadija.” Kamal ya roƙe ta.

“Abinda kawai zan iya cewa zata fi samun zaman lafiya idan kun rabu da ita.”

Taku ɗaya Kamal ya yi zuwa inda Khadija take, abinda yake tunani ne ke ƙoƙarin tabbata. Tsoron abinda ke faruwa ya dabaibaye shi, tsoron kar ya kasa yin wani kataɓus gaban wannan hatsabibiyar aljanar.

“Please Khadija, ki faɗa min duk wani abu da kika sani nayi miki alƙawarin zan yi komai ganin na tseratar da ke koda zan rasa raina ne.”

Nadama sosai a fuskar Khadija, duk abubuwan da ta faɗa ba ita ba ce, ba ita ke controlling kanta ba.

“It's nice all that but babu abinda zai canza. I'm sorry.” Ta faɗa kafin ta juya ta yi tafiyarta.

Kamal da har yanzu yake cikin ruɗu, bai iya hana ta tafiya ba. Yana tambayar kanshi idan Amriya bata shiga jikin duka matan biyu ba. Sun sauya daga yanda ya san su, wani abu na faruwa. Wani abu na faruwa akan idanunsa ba tare da ya iya taɓuka wani abu ba.

Motsin Zahara ne ya dawo da shi daga duniyar tunani, miƙewa ya yi ya nufi inda take. Lokaci guda ta shiga motsawa da sauri. A hankali ya kai hannunsa kan goshinta, ya ji shi da zafi alamun zazzaɓi ne gareta, ba tare da ya ankare ba Zahara ta buɗe idanu. Da iya ƙarfinta ta ture hannun Kamal tare da tashi zaune tana susar kai.

“Sannu..” Kamal yace da ita.

Juyowa Zahara ta yi ta ƙura masa ido amma bata ce komai ba.

Sauran da ke falo da suka ji alamun ta tashi, Ammar ya nufi cikin ɗakin da sauri.

“Ta farka?” Ammar ya tambaya.

“Eh..saidai.. ban sani ba.. bata cewa komai.” Cewar Kamal.

“Yunwa nake ji.” Zahara ta faɗa da siririyar murya tare da komawa ta kwanta kamar komai bai faru ba.

Afnan, Kamal da Ammar suka shiga kallon-kallo... bata cikin hayyacinta. Ba Zahara da suka sani ba ce, wannan wani yanayi ke gare ta mai ban tsoro. Kamal alama yayi musu da su fita. Suka dawo dukansu falo.

“Ina ganin ya kamata a kirawo malami, na fara tsorata da wannan lamarin.” Cewar Afnan.

“Haka ne, akwai wani abu da ke faruwa amma kamar yanda nace a jira har iyayenta su zo. Ba mu ne zamu yanke wannan hukuncin ba !” Cewar babban yayan nasu.

“Kanada gaskiya, amma halin da take cikin yanzu tafi buƙatar malam da gaggawa, hankalin mahaifiyarta zai ƙara tashi sosai idan ta ga ƴarta cikin wannan halin.

“A'a.. na kira Maryam. Tana kan hanya, na tabbatar zata kira iyayenta dan haka a halin yanzu ba zamu yi komai ba, mu bar komai a hannun iyayenta.”

“So... maganata ake ne?”

Ƙaramar muryar suka ji kamar daga sama. Dukkansu sun san Zahara ce. Tana tsaye bakin ƙofar ɗakin. Ta cire mayafin da Afnan ta saka mata, kowa na iya ganin askin da ke kanta. Yanzun askin har yafi abun tsoro ganin yanzun ta dawo normal.

Kamal ya nufi inda take dan ganin yanda take ko tana buƙatar wani abu.

“Kaga ka tsaya da tambaya ta ya nake, hakan ya fara ɓata min rai. Ni yunwa kawai nake ji yanzu, babu wani abun da nake buƙata bayan wannan. Idan ba zaku ban abinda zan ci ba, ni zan yi tafiyata gida.” Ta faɗa da wani yanayi da basu santa da shi ba.

Lokaci guda kuma ta fara murmushi.

“Sorry guys.. bana ɗan jin daɗi ne amma da gaske yunwa nake ji.” Ta sake faɗa tana ƙoƙarin saita nutsuwarta.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang