CHAPTER 44

357 12 2
                                    


«Aure ya ɗauru.» ita ce magana ta farko da Ammar ya faɗa koda matarsa ta ɗaga kiransa. Murmushi a fuska, hawaye a ido ta ce

“Alhamdulillahi Mr. Ammar.”

“Fatan dai baki gajiyar min da kanki ba sosai?” Ya tambaye ta.

“Na san a gajiye nake amma bana jin gajiyar, na ƙagu na gan ka.” Hafsat ta ce masa.

“Na fiki ƙaguwa, muna kan hanya. Zamu iso nan da wasu awanni.”

“An ƙare shirye-shirye nan ma, baƙi kawai ake jira.”

“Good, sai mun iso kenan."

Hafsat ta katse kiran sannan ta kalli ƙawayenta.

“Ba na ce ku fita zan yi waya da mijina ba?”

Dariya ƙawayen nata suka yi suna tafawa.

“Har wani sheƙi kike in kina waya da shi.” Wata cousin ɗinta ta faɗa.

“It's normal, mijina ne.” Hafsat ta faɗa tana dariya kafin tayi ƙoƙarin sauka daga bisa gadon domin ta ƙarasa kwalliyar.

“Yayi, mun fahimta cewar kinada miji. Kuma haka bamu manta ko waye shi ba.” Cewar wata ƙawarta.

Da kyau Hafsat ta ji abinda ƙawarta ta faɗa amma gudun tayar da rikici a rana mai muhimmanci irin yau yasa ta yanke yin kamar bata ji me ta faɗa ba.

“Yaya kwalliyar ta yi?” Hafsat ta tambayi Safiyya.

“Eh ta yi, kin yi kyau masha Allah. Sai jiran zuwan baƙi. Ruky please ko zaki iya zuwa ki duba buffet idan komai na tafi yanda ake so?”

Wani kallo Ruky ta yi mata kafin ta amsa

“Cikina ke ciwo, ba zan iya ba.”

“Idan ba zaki iya motsawa ba, zai fi ki komawar ki gida.” Cewar Safiyya.

“Shikenan zan je na ga idan komai na tafiya da kyau.” Ruky ta faɗa.

Tsuki Ruky ta yi kafin ta fice daga ɗakin.

“Ita kuma wannan meye matsalarta?” Safiyya ta tambaya.

“Na sanar mata, ni dai ba zan tayar da jijiyoyin wuya ba ranar aurena, miƙo min takalmina.” Hafsat ta cewa Safiyya.

“Zan daidaita mata zama idan bata dawo hayyacinta ba...”

“Bana buƙatar wani rikici Safiyya. ki barta da ƴan matsutsanta. Daman hakan bai wani dame ni ba. Tun asali haka take, ba yau ba ne zata canza. Mu fita sha'aninta shi zai fi.”

Ruky bata sake dawowa ɗakin ba, sai wani sabon babi mai daɗi ya buɗe a ɗakin. Lokaci na tafiya, har baƙi sun fara zuwa. Amarya da ƙawayenta na tarbon su hannu biyu, haka aka yi ta yi har zuwan ango Ammar. Koda suka ga juna, suka rungume juna. Ƴan uwa da abokan arziki suka shiga tafi da neman sai an yi kiss. Nauyi Hafsat ta ji tana ƙoƙarin suɓucewa daga jikin Ammar amma shi kuma yayi amfani da wannan damar ya kai bakinsa jikin nata.

Sun ɗau ƴan mintuna koda ya sake ta Hafsat cikin raɗa ta ce

“Oh my god, wallahi na ji kunya ba kaɗan ba.” Ta faɗa cikin kunnen mijinta.

“Mata da miji muke yanzu, babu wata kunya da zaki ji. Ke tawa ce ni ma naki ne.” Ya ce da ita.

“Mu je falo mu jira sauran baƙin.” Cewar Hafsat.

Party ya fara armashi kowa ya zo ana ta nishaɗi. Amarya da ango suna ta kai kawo domin gaishe da hira da baƙi.

Kamal da Khadija suna ta hira hankali kwance. Yana jin daɗin partyn da kuma kasancewarsa kusan matarshi.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now