AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)ᥣׁׅ֪ᨵׁׅ᥎꫶ׁׅꫀׁׅܻ 💞 ɑׁׅ֮ꪀׁׅժׁׅ݊ hׁׅ֮ᨵׁׅꭈׁׅꭈׁׅᨵׁׅꭈׁׅ ☠️ ꯱ׁׅ֒tׁׅᨵׁׅꭈׁׅᨮ꫶ׁׅ֮📖
By Malik al-Ashtar 🖋
HOME OF QUALITY WRITTERS ASSOCIATION
𝐂𝐇𝐀𝐏𝐓𝐄𝐑 𝟒𝟔
On Wattpad 👉 https://www.wattpad.com/story/270492485
For more Novels 👉 http://www.ashblogg.com.ngA hankali gajiya ta fara saukarwa Zahara. Ta sani cewa internship ɗin ta ba irin na tsayawa hutu ba ne amma yanzu, babu abinda take so da ya wuce ta ɗauki hutun sati guda tsabar yanayin wahalar aikin ya wuce tunaninta. Ga kuma matsi da take samu daga ogansu da bai barin ƴan koyo irin ta numfasawa. Shi yasa take iya ƙoƙarinta ganin bata saka ƙafar wando ɗaya da shi ba. Duk hakan ba sauƙi bane da shi da fari saboda tana ɓata kowacce daƙiƙa tana tunanin Kamal. Saidai daga baya ta samu, dan kar ta sawa kanta damuwa.
Dandanan komai ya fara tafiya. Tana zuwa wajen aiki, da ta dawo tana kamawa Mama girkin dare daga nan zuwa ƙarfe tara tana zuwa ta kwanta dan ta tashi da wuri. Bata ma samu lokacin ganin Maryam ko Habib ba. Yauwa maganar Habib, alaƙar da ke tsakanin su tayi ƙarfi yanzu ba a suffar soyayya ba, a matsayin aboki wanda ya cike wani gurbi a rayuwarta. Shi da Maryam sun goyi bayanta sosai lokacin da take London. Wani lokacin sai su ɓata awa da awanni suna magana ba tareda ta ji ta takura ba. A yanzu haka yanada budurwa Ramlat, babu ɓata lokaci suka kamu da son junansu, yanada ƙudurin idan ya dawo daga wata tafiya da zai yi ƙasar waje ya tura iyayensa gudansu.
Sanin cewa duka abokanta da kuma iyayyenta sun takura mata da ta yi aure. Maganar da suka yi da Mama ce ke dawo mata ba ƙaƙƙautawa.
“Zahara shekaru tafiya fa suke.” Mama ta fara koda Zahara ta saka ƙafarta a falo.
“Me kike son ki ce Mama?”
“Ya kamata ki yi aure Zahara, bana son ki koma tsohuwar budurwa.”
“Ba dan muna son yin aure ba, yake nuna a yi shi a take. Ba daga ni ba ne, har yanzu ban samu wanda ya dace ba ne.”
“Ni da Abbanki mun damu sosai akan gobenki. Muna tsoron ki mayar da hankalinki sosai a aikinki har ki manta da abinda yafi komai muhimmanci a rayuwarki.” Cewar Mama.
Dawowa Zahara ta yi ta zauna kusa da Mama.
“Mama, zan yi aure idan lokaci ya yi kuma na samu wanda ya dace. Kar ku damu, ni ba yarinya ba ce zan kula da kaina.”
“Kenan bakida saurayi yanzu?”
“Kai Mama..”
“Tambaya ce kawai, shikenan banida ƴancin yin tambaya akan rayuwar soyayyar ƴata?”
“Banida saurayi yanzu.”
“Zaku iya daidaitawa da...”
“A'a kar ki ƙarasa please Mama, ba zan yiwa Allah shishigi ba. Zan yi aure idan lokaci ya yi. Yanzu zan je na kwanta saboda zan je wajen aiki gobe.” Zahara ta faɗa tana miƙewa tsaye da niyyar tafiya.
“Mahmud yaron kirki ne, kyakyawa, ladabi ga kuma kuɗi.”
“Toh ke ki aure shi mana.”
“Ke bana son shashanci.” Mama ta faɗa da alamun rai a ɓace.
Dariya Zahara ta yi.
“Kin gani, ni zan je na kwanta please ki daina yi min maganar aure, bana so. Ki bar ni na ji da sha'anin soyayyata ni kaɗai.”“Ni mahaifiyarki ce kuma ba zan samu kwanciyar hankali ba har sai na gan ki ɗakin mijinki kuma kin samu ƴaƴanki.”
....
WASHE GARI A WAJEN AIKIN SU ZAHARA
VOUS LISEZ
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
HorreurLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...