“Ok, zan taƙaice : da farko zan je gidansu, zan nemi da mu je gidana irin yaushe rabo haka ne?”
“Eh." kamal ya bata amsa.
“Daga nan bayan mun je gidana, zan sanar da ku domin ku zo da malam? Amma zaku jira nesa kaɗan da gidan har lokacin da nayi muku alama?”
“Haka ne."
“Ba zan ce wannan plan ɗin ba zai yi ba, amma ina ganin ya yi sauƙi da yawa. Ba Zahara da na sani ba ce a baya, ba zata biyo ni ba ta sauki. Na tabbatar ita ce bata son zuwa inda muke, tana amfani da Mama ne kawai dan kawar da zargi.” Cewar Maryam.
“Haka ne abinda Maryam ta faɗa. Wannan aljanar da hankalinta. Ta san cewa muna shirin yiwa Zahara Ruqya. Zata iya yin komai ganin ta hana mu.” Cewar Ammar.
“Kuna tunanin ban san da duk wannan ba? Duk da sauƙin wannan plan ɗin, shi kaɗai ne mafitar da na samu domin samun Zahara. Me zai hana mu jaraba mu gani. Bamu da wani zaɓi. Ko wannan plan ɗin ko kuwa mu kutsa cikin gidan nasu.”
“Shikenan... Zamu jaraba wannan..” Cewar Maryam.
“Eh amma ya kamata...”
Ringing wayar Ammar ce ta katse abinda Kamal zai ce.
“Salmah..?” Ammar ya faɗa bayan ya ɗaga kiran.
Kallon sa Kamal ya yi yana tunanin yaushe kuma Ammar ya shirya da Salmah amma alamu sun nuna shi kanshi cikin mamakin kiran nata yake fiye da ɗan uwan nashi.
“Kamar yaya tana hospital? Me yake faruwa ne?"
“Lafiya Khadija take?” Kamal ya tambaya hankali a tashe. Miƙewa ya yi da niyyar karɓar wayar amma ɗan uwan nashi ya yi masa alama da hannu ya dakata.
“Ok gamu nan yanzu yanzu.”
Kamal bai jira Ammar ya kashe wayar ba, ya dirar masa.
“Ina Khadija ? Waye a asibiti?”
“Tana asibiti, ta zubar da jini sosai.” Cewar Ammar.
“Ta.. ta yaya hakan ta faru? Mu je asibitin yanzu-yanzu.”
“Eh, tana Ɗan Katsina Hospital.”
“I'm sorry Maryam amma ya kamata in je duba ta. Zan kira ki idan komai ya daidaita ok?”
“Kar ka damu Kamal, take your time. Ina fata ta samu lafiya da gaggawa.” Maryam ta faɗa kafin ta ɗauki jakarta ta tafi.
Bayan ƴan mintuna suka isa asibitin. Kamal a ruɗe yake da har ya rasa abun yi, ɗan uwan nashi ne ya je reception domin jin inda Khadija take.
“Yaya ake ciki?” Kamal ya tambaye shi.
“A halin yanzu tana ɗakin agaji amma za a fiddo ta a kaita room 26 cen ƙarshen corridor.”
“Abun ƙwarai ne kenan? Gaskiya a tsorace nake." Cewar Kamal.
“Kar ka damu na tabbatar zasu kula da ita da kyau.” Ammar ya tausasa shi.
“Eh amma idan fa ta rasa baby. Tana fa farkon cikin ne... This situation is very abnormal.”
“Kar ka yi mummunan tunani. Fata na gari zamu yi ! Na tabbatar komai lafiya. Salmah tana waiting room mu je mu same ta...”
“Okay."
Kawai Kamal ya bar maganar ne amma ya tabbatar akwai wani abu da ke faruwa. Yana tsoron a ce Amriya ce silar duk wannan. Ya lura dukkan rayuwarsu tana juyi ne a farfajiyar wannan aljanar. Abu ɗaya da zai cece su a halin yanzu shi ne Ruqya da yin cikakken imani da Allah.
ESTÁS LEYENDO
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
TerrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...