CHAPTER 2

954 42 0
                                    

Kowa a offishin yaji irin karar da ta fito daga corridor, hatta Mr. Kamal da shigowar sa kenan. Haka ma Mr. CEO duk da nisan dake akwai tsakanin offishin sa da corridor yaji wannan karar. Saving aikin da ya fara a computer yayi tare da fitowa da sauri domin ganin meke faruwa. Yana fitowa yayi kicibus da yayan shi Mr. Kamal da shi ma karar ce ta fito dashi.

"Karar meye wannan?" Mr. CEO ke tambayar dan uwan sa. Shi kuwa daga masa kafada kawai yayi a matsayin amsa.

Nufar inda suke tunanin karar ta fito suka yi. Tun daga nesa suka tsinkayi kamar alamar mutum a kwance. Sai da suka karasa Amar ya gane Zahara ce. Tambayar kansa yake abinda ya faru da har ta tsinci kanta a nan. Tsoro ne ya kama shi ganin ya tabata bata motsa ba. Durkusowa dan uwan nasa yayi tare da taba jijiyar hannunta kafin yace :
"Suma ne tayi."

Ajiyar zuciya Amar yayi, cak ya dauke ta ya nufi office din sa da ita. Shi kuwa dan uwan sa ya tsaya tattare takardun da suka zube a kasa.

Aje sakatariyar tasa Amar Yusuf yayi kan doguwar kujerar da ke a offishin nasa. Kokarin tayar da ita ya shiga yi a hankali amma bata tashi ba. Dan uwan sa ne Kamal Yusuf ya shigo, ya ajiye takardun bisa desk din Amar kafin ya samu kujera ya zauna. Amar kokarin kiran likitan su yake domin yayi gaggawan duba Zahara, amma ya dakata sakamakon ganin ta fara motsi. Kokari take ta tashi zaune da sauri yazo ya taimaka mata ta zauna.

A bangaren Zahara kuwa, har yanzu hankalin ta bai dawo jikin ta ba, bata iya tuna komai ba. Razanar da tayi yasa ta manta a wajen aiki take.

Sunan Mama ta kira tana murza idanun ta. Tana kallon wanda ke a gaban ta, da har yanzu dishi-dishi take ganin sa. Sai dai lokacin da ta fara dawowa hayyacin ta, ta fahimci hannuwan da ta taba yanzun ba na Mama ba ne. Daga kanta tayi anan tayi arba da fuskar Amar wato ogan ta. Da sauri tayi baya tana mai tashi daga kujerar. Kamal da ya mayar da hankalin sa ga wasu takardu ya dan juyo ya kalle su.

"Dan..dan..dan..Allah..ku..kuyi hakuri, ban..bansan me nake..yi..ba anan." Zahara ta shiga i'i'na tana bada hakuri ba tare da tsayawa ba.

"Suma kika yi, shi ne na kawo ki nan. Lafiyar ki kuwa?" Cewar Amar.

"Dan..Allah..kayi hakuri, ba da gangan..."

Wai hakuri take badawa da suman da tayi? Kamal ya fada a zuciyar sa tare da sake kallon su karo na biyu.

"Me yasa kike bani hakuri? Ba fa da gangan kika yi ba. Toh saboda me ma zaki yi karyar suma? Zauna ki huta, bari na kirawo doctor." Amar ya fada da sigar umarni amma Zahara ta cigaba da bashi hakuri.

"Kayi hakuri, ban so in takura ka ba."

Kamal da ba shiga lamuran mutane yake ba, yaji halin Zahara ya takura shi yace :

"Bayar da hakurin ya isa haka, ki jira ya kira doctor idan kuma ba zaki iya aikin ba ki tafi gida." Ya fada da kakkausar murya da alamun an takura shi.

Wannan ne karon farko da ya fara yi mata magana tun zuwan ta kamfanin nan. Ya fada mata hakan ne yana kallon ta cikin ido. Hakan kuwa ya tsorata Zahara ba kadan ba. Allah yayi mata dabi'ar bada hakuri ba tare da ta tsaya taji ita ke da laifi ko kuwa. Bata son tashin hankali ko kadan shi yasa da abu ya hada ta da mutum take kokarin su rabu lafiya.

"Kina son na kira likita ne ya duba ki? Ko zaki tafi gida ki huta. Zan samu wani sai ya karasa aikin naki." Cewar Ogan nata.

Juya Zahara tayi tana fuskantar shi tare da cewa zata iya cigaba da aikin nata.

"Bana son na kara tarar dake a kasa. Na yarje miki, zaki iya tafiya idan baki jin dadi."

A cikin ranta, babu abinda take so kamar zuwa gida, amma bata son taje bayan takurawar da tayi masu. Gashi kuma tana da aiki da yawa, kuma tana son kammala documents din da ya bata dazun. Tunawa tayi da har takardu zata kai a dakin meeting. Amma bata sani ba ko tana da kuzarin da zata kara tunkarar wannan corridor ba. Har yanzu tana tuna abinda taji lokacin da hannun nan ya taba ta. Lokacin da ta juyo bata ga kowa ba. Alhali ita tasan hannu ya dafa ta.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Onde histórias criam vida. Descubra agora