CHAPTER 25

156 32 3
                                    




Watanni sun shude kuma abubuwa da dama sun faru.

Kamal har yanzu cikin bakin ciki yake tun lokacin da ɗan uwansa ya faɗa masa abinda mahaifinsu ya aikata. Kamal bai iya haɗa idanu da Afnan; babu wanda yake iya yin hakan duk da ƙoƙarin da suke yi wajen nuna kamar komai bai faru ba. Yayyun Afnan din sun yi mata alƙawarin cigaba da kallonta kamar a baya amma bata san kawai dauriya ce suke yi ba. Ba mai yiyuwa bane nuna kamar komai bai faru ba.

A ranar nan lokacin da Ammar ya kira family meeting kuma kowa yazo, har da Kamal da yake asibiti sai da ya nemi da a kawo shi gida. Ya gaji da zaman asibitin kuma wannan meeting din sai ya zamar masa wata dama, duk da ƙaguwar baro asibitin nasa ta ɓace lokacin da yaji gaskiyar dalilin kiran meeting din.

Ammar yazo da Afnan. Daddy kuwa sai muzurai yake, yana kallon Afnan cike da tsana. Yaso yayi wani wasan kwaikwayo a wurin kuma ya tari Afnan hannu biyu saidai hakan bai yiyu ba sakamakon tsanar da yake ji game da yarinyar. Abinda bai sani ba, Afnan ba zata bari yayi magana ba ko yin dramar da ya shiryo ba. Tana jin wani ƙwarin gwiwa a tattare da ita sakamakon kasancewar Ammar a gefenta. Ba zata ce bata jin tsoro ba, amma tana jinta cikin tsaro kuma a shirye take domin tunkarar wannan dodon.

Lokacin da Hajiya Karima ta dawo gida tareda ɗanta Kamal da kuma daya daga cikin nurses na asibitin, Mijinta da Afnan na zaune a falo babu yanayin alkhairi a yanda ta gane su, dandanan ta fahimci meke faruwa. Kuma ta fahimci lallai familynta bai gama rushewa ba.

Cikin yanayin ɓacin rai ta taimakawa Kamal ya zauna. Ta gaishe da mijinta bayan ta ba banza ajiyar Ammar da Afnan. Wuri ta samu ta zauna sannan ta fara magana
“Me ya kawo ku gidana?” Tace da Ammar da Afnan.

“Ki yarda naso kar na sake tako ƙafata cikin gidan nan.” Cewar Ammar.

Daddy da tun dazu yayi nisa cikin tunani yace
“Ɗanki ne ke zargi na da aikata wani abu marar dadin faɗa, har kunya nake ji na furta hakan.”

“Afnan, kin rantse sai kin wargaza min iyali ko? Bayan kin je kin yi karuwancin ki waje shine kike son ni ki zo bata min sunan ahali ko? Me na faɗa miki a baya?”

“Kin san da zancen kenan?” Cewar Ammar da mamaki. “Kuma shine baki ce komai ba?”

“Saboda ƙarya take, kawai tana son wanke kanta ne ta hanyar ɓata nawa gidan. Ba zan yarda da wannan ba!” Cewar Mommy.

“Wai meke faruwa ne?” Kamal ya tambaya da muryarsa ta marasa lafiya.

“Ba komai ɗana, bari na sa nurse ya kai ka tsohon ɗakinka domin ka huta.” Cewar mahaifiyar tasu.

“Ba komai? Wannan mutumin da muke kallo a mahaifinmu shi ya yiwa Afnan fyaɗe.”

Da farko Kamal bai fahimci komai ba, amma da maganar ta rasa illahirin ƙwalwarsa, waro idanu yayi ya kalli Daddy ya kalli Ammar.

“Rufe min baki.” Cewar Hajiya Karima. “Kar na sake jin ka ƙara faɗar irin wannan shirmen ƙanzon ƙuregen da bakinka."

Afnan ɓoye fuskarta tayi da tafin hannuwanta a bayan Ammar. Shi kuwa Daddy gefe yake kallo ba tareda ɗaya daga cikinsu ya canki abinda yake tunani ba.

“Tsaya Ammar. Wannan fa ba ƙaramar magana bace. Na kasa fahimta, kayi min bayanin abinda ya faru.” Cewar Kamal.

Ammar ya fara bashi labarin duk abinda ya sani da kuma yanda yayi ya gane gaskiya. Lokacin da ya ƙare, Kamal ya kalli Afnan yace
“Afnan, dagaske ne abinda ya faɗa?”

Afnan bata ce komai ba na tsawon wasu mintuna.

“Dagaske ne abinda ya faɗa?” Kamal ya ƙara tambayar ta wannan karon gyaɗa kai tayi alamar eh.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang