CHAPTER 36

1K 13 2
                                    



Wajen ƙarfe sha biyu na rana, lokacin Ammar na bacci, wayarshi ta fara ringing. Cikin yanayin gajiya da bacci ya miƙa hannunsa ya ɗauki wayar. Buɗe ido ya yi ya duba screen ɗin wayar ya ga sabon sakatarenshi ne ke kira. Gyaran murya ya yi sannan ya ɗaga kiran.

“Mr. Ammar fatan dai ban takura ka?” Sakataren ya tambaye shi.

Ammar da har yanzu cikin yanayin bacci ya tashi zaune domin yin magana da kyau.

“A'a ba damuwa. Ya kake?” Ammar ya tambaye shi.

“Ka bar min ayyuka da dama kuma bani da mataimaki amma zan iya ji da komai ka sanni ai.”

“Na sani kanada ƙwazo, so tell me meke faruwa ka kira ni?"

“Euh wata mata ce ta zo neman ka, na ce mata baka nan but she insisted. Dan haka na ce ta jira har in yi maka magana ko ka zo yau.”

“Wata mata? Amma ban yi da wani yau zamu haɗu ba.” Ammar ya faɗa a hankali yana checking ƙwaƙwalwarsa dan ganin ko ya tuna ko mutum ɗaya.

“Kai gaskiya ban yi da wani zamu haɗu ba.” Ya sake faɗa.

“Eh, ta faɗa min baka san da zuwanta ba amma tana son ganinka da gaggawa domin ta ce is important.”

“Meye sunanta?”

“Hafsat Abubakar..”

Jin sunan da sakataren nasa ya faɗa ya sanya shi saurin wartsakewa daga baccin da yake ji kamar wanda ya sha double dose na coffee.

“Ka tabbatar cewa ta yi sunanta Hafsat?”

“Ban yi kuskure ba haka ta faɗa min, toh yaya ka zo ne?”

“Ina son zuwa amma ina tsoron kar ta ƙi  jira na domin har yanzu bisa gado nake.”

“Ina tunanin ta kange tana son magana da kai. Dan haka kana iya yin sauri. Na tabbatar zata jira ka.”

“Ok, ka ce mata gani nan tafe nan da wasu ƴan mintuna.”

Bai jira jin amsarshi ba ya katse kiran. Bai san ta yaya ya yi sauri ba amma cikin mintunan da basu fi ashirin ba sai gashi yana saka takalmi domin tafiya.

Gashi a takure yake lokacin da ya karaso kamfanin, bai iya wani ƙwaƙwaran tunani ba. Kusan sau uku yana maƙuwar zuwa ofishinsa. Knocking ya yi ya buɗa ya shiga ba tare da ya jira amsa ba.

“Ka ce ka yi sauri !” Cewar sakatarenshi.

“Tana ina?” Ya tambaya ba ɓata lokaci.

“Tana waiting room, zauna bari na kira ta.”

Zaunawa ya yi ba ɓata lokaci, ya ƙara gyara necktie ɗinshi sannan ya jira ta shigo. Ya kasa cankar wacce irin magana ta zo suyi. Tun bayan zuwan da ya yi gidansu bai sake bi ta kanta ba. Yayi tunanin wannan ce mafita domin ita ma haka take so. Jin ta zo neman shi alhali shine mutum na ƙarshe da zata so gani... ta bashi mamaki matuƙa.

Knocking ƙofar aka yi, ya bada umurni da a shigo.

A hankali aka buɗo ƙofar. Ji ya yi kamar komai na tafiya slowly. Ƙofa da ta buɗe.. ita da ta shigo.. yana nazarin abun kamar ƴan kallo a cinema.

Girgiza kansa ya yi domin ya dawo hayyacinsa. Babu shakka Hafsat ce a ofishinsa. A sanyaye ta ƙaraso inda yake. Duk da yanayinta ya nuna a takure take amma bai hana shi jin daɗin zuwanta ba... Daddaɗen kamshin turarenta ne ya baɗe masa hanci. Tana sanye da doguwar farar abaya mai jajayen maɓallai. A hannunta kuwa tana ɗauke da jaka biyu, abinda ya bashi mamaki kenan. Yana tunanin kamar daga kasuwa take.

“Zan iya zaunawa?” Ta tambaye shi.

Daburcewa ya yi kamar ƙaramin yaro, da ƙyar ya iya yi mata bismillah ta zauna kan kujera. Godiya ta yi masa, ba tare da ɓata lokaci ba ta fiddo wata ƙatuwar leda daga cikin ɗayar jakarta ta miƙo masa.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora