CHAPTER 45

603 10 2
                                    

Zahara ce ta farka daga bacci, a zahiri ba baccin tayi ba. Yanda ta baro wajen bikin Mr. Ammar ne yake ta dawo mata ba ƙaƙƙautawa. Zuwan da tayi cen tareda Maryam, tayi tunanin ta je da ƙarfin gwiwarta da tattare nutsuwarta guri ɗaya. Bata taɓa tunanin sake haɗuwa da Kamal zai yamutsa mata lissafi ba. Tsorata tayi ta baro gurin bikin ba tareda tayi bankwana da ango da amaryan ba. Akan hanyanta na dawowa gida babu irin zagin da bata yiwa kanta ba. Abinda tayi, hali ne na yarinya ƙarama amma za a iya cewa bata shiryawa haɗuwa da shi ba ne. Bayan duk wannan shekarun, tayi tunanin ta daina jin komai game da shi saidai da alamu ta yiwa kanta ƙarya. A bayyane yake bata jin sonshi kamar baya amma har yanzu akwai soyayyarsa a zuciyarta. Kuma gane hakan ba ƙaramin girgiza ta yayi ba.

Sosai Maryam ta ji haushin barin ta wajen bikin da Zahara ta yi, saidai dandanan ta fahimci sosai Zahara ke tsoron haɗuwa da Kamal kuma har yanzu tana son shi. Kuma sanin wanda Zahara ke so ya yi aure har matarsa gata da tsohon ciki yana tayar mata da hankali. Tsab hakan zai iya jagula rayuwan duka su ukun, saidai ba zata iya cewa ƙawarta ta binne soyayyar da take wa Kamal ba, domin hakan zai iya cutar da ita. Ba adalci bane hakan kuma bata cancanci wannan ba.

Tashi Zahara ta yi daga bisa gado domin shiryawa zuwa wajen internship ɗinta. Samun nasarar shiga makarantar aikin jarida ta ƙasar London na ɗaya daga cikin zaɓi mafi kyawu a rayuwarta. Har yau tana yiwa kanta tambayar ta yaya wannan ƙwarin gwiwar ya zo mata, wannan ƙwarin gwiwar na barin komai a nan, zuwa wata ƙasar da babu wanda ta sani babu wanda ya santa ta cigaba da rayuwarta. Duk da wani lokacin ta kan yi nadamar wannan zaɓi nata, a yanayi na tsanani, amma wannan zaɓi ya canza rayuwarta kuma yau tafi samun kwanciyar hankali cikin rayuwarta da aikinta. Haka iyayenta na farin ciki sosai na kyakkyawar matar da ta koma, wacce a shirye take ta tunkari duk wani abu da zai zo mata mai daɗi ko marar daɗi. Da fari basu amince ba, na tafiya ƙasa mai nisa wacce babu wani nata cen. Gashi kuma ga yanda Zahara take yarinya ce da ƙarancin wayo, dole iyayenta su tsorata da tafiya amma Zahara tayi ƙoƙari ganin ta shawo kansu. Yau gashi sun fi kowa farin ciki.

Makarantar da take yi London suka nemi da ta yi internship a wata ƙasar. Da tayi tunanin zuwa Faransa daga baya kuma ta sauya shawara dawowa nan gida Nijar tayi internship nata, daga nan ta yi amfani da damar ganin danginta da kuma ƙasarta. Saidai wani rashin sa'a internship ɗin baya wuce wata biyu, sai ta koma London ta ƙarasa karatun nata. Dan haka take tunanin amfani da wannan damar domin a cewarta bata san yaushe zata sake dawowa ba.

Zahara ɓata ranar tayi tana juyi bisa gadonta, har ta manta sun yi da Maryam zata je gidanta, zata dafa mata frikkadel. Tashi tayi domin ta shirya, doguwar baƙar riga ta saka da kuma hijab fari. Hakan ce shigarta tsawon shekaru biyu kenan. Abin farin cikin gareta, school ɗin su a London basu da matsala akan irin wannan shigar duk da wani lokacin tana jin idanu akanta. Amma koma meye ba zata fidda hijabinta ba domin shi ne identity nata.

Zahara tayi kwalliya sannan ta baɗe kanta da turare kafin ta ƙarasa saka kayanta. Kiran aminiyar tata tayi domin faɗa mata gata nan zuwa nan da ƴan mintuna. Ta iso ƙofar gidan Maryam bayan kamar mintuna sha biyar, tuni Maryam ta shirya diner.

"Yoh ina frikkadel ɗin?" Zahara ta tambayi Maryam da ke yankan albasa.

"Kamar yaya ina frikkadel ɗin? Ƙarfe sha biyun rana muka yi da ke, yanzu shiddan yamma ne, kar ki tunzura ni Zahara kin ji ko." Maryam ta faɗa da nuna alamun ɓacin rai a fuskarta.

"Duk da haka ai dai kin ajiye min ko?"

"Ki jira diner, na kusan gamawa. Ina girka afang ne."

"Ni dai frikkadel nake so, an jima rabon da na ci shi."

"Shikenan,jira bari na ƙarasa wannan sai na ɗumama maki."

Zahara zaunawa tayi bisa ɗaya daga cikin kujerun kitchen ɗin, tana kallon Maryam.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now