Bata taɓa tunanin ganin mutumin da take tunani kwana biyu a ƙofar gidansu ba. Abu na farko da ta so tayi shine ta maida ƙofa ta rufe kamar bata ganshi ba. Saidai a daidai lokacin wani ƙwarin gwiwa ya ziyarce ta.
“Me kazo yi nan?" Zahara ta tambaye shi.
Kamal bai san takamaimai abinda zai yi ba, duk da haka yace
“Ya kike Zahara?"“Lafiya lau daƙiƙu kaɗan baya nake, excuse me now akwai inda zan je." Ta faɗa kafin ta rufe ƙofar gidansu. Ta gabansa ta bi da niyyar tafiya amma ya riƙo hannunta.
“Zahara, please ki saurare ni, ki bani mintuna biyar dan Allah. Idan ba gaggawa bane ba zan zo nan ba."
“Ba so kake ka tafi ba? Kayi tafiyarta kafin raina ya ɓaci kuma ka yarda ba zaka so gani na rai a ɓace ba."
“Ni da Khadija zamu..."
Katse shi tayi.“Ni bana son jin komai, ba zan saurare ka ba dan haka kayi tafiyarka kuma kar ka sake dawowa nan ko kuma ka ji maganganun da ba zasu yi maka daɗi ba..."
“Shikenan ba zan yi maganata da Khadija ba, babban abinda ya kawo ni nan shine Amriya." Kamal ya faɗa.
“Meye Amriya?" Zahara ta tambaye shi da mamakin ta inda ya ɓullo.
Dawowa Kamal yayi suna fuskantar juna sannan yace :
“Ina tunanin tana nan...tana ƙoƙarin tarwatsa min rayuwa da kuma ta Khadija. Ba wai ina faɗar haka ba ne domin neman uziri a gare ki amma ina tunanin ita ce silar sa inyi nesa da ke. Ita ce silar rashin lafiyar da nayi ta yi. Ina tsoron ta cutar da ke, da ni da kuma bab...da kuma dangina."“Bravo... Ka zo ne ka bani wannan labarin kawai dan na yafe maka? Ɓata lokacinka kake, ni ba sakarya ba ce Kamal."
Tafiya Zahara tayi kafin ta waiwayo.
“Da ka samo wani labarin ba wannan ba, tsoho ya riga yayi maganin Amriya kuma wannan layar tana nan koda zata dawo. Yanzu ka koma ka sake ƙirƙiro wani labarin da yafi wannan sannan ka dawo mu gani ko zan yarda da kai." Ta faɗa kafin tayi tafiyarta ta bar Kamal tsaye jiki a sanyaye.
Jiki a sanyaye, yanzu ya fahimci adadin yanda Zahara ke fushi da shi. Abinda yayi mata ba ƙaramin laifi ba ne, daidai idan tayi fushi. Shi ma zai iya shiga wannan yanayin idan Zahara tayi nesa da shi babu wata ƙwaƙwarar sheda.
Ya kamata ya nemo hanyar da zai yi mata bayanin komai cikin kwanciyar hankali kafin ya makara. Ba zai taɓa yafewa kanshi ba idan har Amriya ta cutar da ita.
ƁANGAREN AMMAR
Tun da sassafe ya tashi domin kai Hafsat gida. Ya yiwa ɗan uwansa alƙawarin kula da ita da kyau. Kuma ko babu wannan alƙawarin, ba zai yi komai ba wanda zai cutar da Hafsat. Ya ga halin da take ciki jiya, kuma koda basu jituwa, ya damu da halin da take ciki kuma yana son sanin abinda ya faru da ita.
Bayan ya iso ƙofar gidan Kamal, ya yi knocking ƙofa. Bayan wasu mintuna... yana ta jira amma babu wanda yazo ya buɗe masa. Ƙara nocking yayi, wannan karon sai ga Hafsat ta buɗe masa.
Bai yi mamakin ganin yanda fuskarta duk ta kumbura ba.
“Da sauki jikin naki?" Ya tambaye ta. Ji wata banzar tambaya kuma. Ya faɗa a ransa.
Saidai Hafsat bata bashi amsa ba. Juyawa tayi ta koma cikin ɗaki, kafin ta rufe ƙofa Ammar yace :
“Ni ne zan mayar da ke gida, idan kin shirya ina falo." Ya faɗa mata.
A matsayin amsa, Hafsat ta rufe ƙofar ɗakin da ƙarfi. Ammar yaji kamar sun yi musayar hali. Da fari shi ke yin duk abinda zai yi ganin yayi nesa da yarinyar nan amma yanzu ita ce ke gudunsa. Shi ma ba wani son su zama friend yake ba lokaci guda, saidai yana binta a sannu ne ganin abinda ya faru da ita. Daga ƙarshe sai da ya fara nadamar sakar mata fuska da yayi.
ВЫ ЧИТАЕТЕ
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
УжасыLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...