CHAPTER 33

809 30 6
                                    

AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story📖

By Malik al-Ashtar 🖋

CHAPTER 33

I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 33 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”

http://www.ashblogg.com.ng/2022/03/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-33.html

“Ƴata, na roƙe ku, ku dawooo min da ƴata.” Abinda mahaifiyar Zahara ke ta nanatawa kenan.

“Dan Allah Mama ki kwantar da hankalinki, Zahara zata dawo...”

Maryam ce ke ƙoƙarin lallashin mahaifiyar ƙawar tata amma ko ita bata yarda da abinda take faɗa ba.

“A'a ba gaskiya ba ne. Tsawon kwanaki kenan da ɓatanta. Na tabbatar wani abu ya faru da ita. Ilhamar uwa ba zata min ƙarya ba.”

Ƙoƙarin kwantar da ita kan doguwar kujera Maryam ta yi amma Mama na ta kokowa da iya ƙarfinta da yasa mutanen da ke falon gane bata son a taɓa ta. Mahaifin Zahara bai iya jurar ganin matarsa cikin wannan yanayin kuma bai san me zai yi ba domin ya rarrashe ta. Ya yi nema ko'ina cikin gari : wajen aikinta, bakin kogi amma babu labarin Zahara. Tunani na ban tsoro iri-iri na ta ziyartar ƙwaƙwalwarsa : Kidnapping, kisa, fyaɗe. Tunanin ƴarsa cikin halin rashin kariya kaɗai na ɗaga masa hankali. Babu wanda ya fahimci abinda ya faru. Wata safiya, ta tashi daga bacci, ta cewa ƴan gidan zata fita ta ɗan sha iska kamar yanda ta saba idan bata jin daɗi. Babu wanda ya yi tunanin ba zata dawo ba. Ta saba irin wannan fitar amma bata taɓa wuce awa biyu zuwa uku ba.

Hankalin kowa ya tashi. A ɗaya ɓangaren kuwa, Kamal ne ke bin lungu da sako na garin Maradi neman Zahara. Bai yi bacci ba tun jiya ga gajiya kuma ta fara haye masa. Accident ya kusan yi, nan ya fahimci ya kamata ya tsaya ya huta kafin ya cigaba da neman ta. Ba amfanin komai gajiyar da kai idan ba zai iya tsayawa ya yi tunani mai kyau ba.

Haɗa sauran kuzarin da ya rage masa ya yi ya nufi gidansa. Lokacin da ya isa ƙofar gidansa, ya tarar da ɗan uwansa da shi ma yanzu ya fito daga motarsa. Gaisawa suka yi a tsaitsaye kafin ya shigewarsa cikin gidan ba tare da yace komai ba. Bin bayansa Ammar ya yi. Ya san adadin yanda Kamal yake cikin ruɗu a halin yanzu. Rufo ƙofar ya yi bayan ya shigo, ya zauna kan kujera a falo. Bayan kamar rabin awa sai ga Kamal ya fito da alamu wanka ya yi amma bai sauya kayan jikinsa ba kuma har yanzu akwai alamar gajiya a idanunsa.

“Ka dawo hayyacinka Kamal, na tabbatar za'a gan ta.” Cewar Ammar.

“Na fara fidda rai akan hakan. Na neme ta ko'ina. Ba wani wuri take zuwa ba sosai, ban ga me zai sa a kasa ganinta ba. Hankalin mahaifiyarta ya tashi sosai.”

“Akwai al'ajabi a wannan lamarin !”

Kallon sa Kamal ya yi bai ce komai ba. Da sauri ya duba wayarshi ya ga missed calls da dama na Khadija sai dai ba ta ita yake ba, ya yanke shawarar sake komawa neman Zahara.

“Ko zaka taya ni ne?” Ya tambayi Ammar.

“No.. akwai wani guri da zan je.” Ya bashi amsa.

Kamal ya ga ɗan uwansa ba yanda ya saba ganin sa ba amma sai bai yi masa magana ba kuma ma baida lokacin wani binciken daban. A ɓangaren Ammar, yana ƙoƙarin shi da wasu mutanen Farouk gyara lamarin Hafsat.

“Shikenan.. ni na tafi.”

“Ka kula da kanka Kamal, ka ci abinci sannan ka huta.” Ammar ya bashi shawara.

Gyaɗa masa kai Kamal ya yi sannan ya tafi. Ammar ya isa wajen meeting ɗin cikin ƙanƙanin lokaci inda Farouk yake jira shi da mutanensa huɗu. Suna kusa da Hotel ɗin da Hafsat zata zo. Suna jira a nutse hankali kwance.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now