HAFSAT
Wajen karfe bakwai lokacin da ta fara jin gajiya a jikinta. Daren jiya yana daya daga cikin darare mafi bakin ciki a gare ta. Tamkar kwalwarta ta shirya da gangan ta dinga nuna mata cin mutunci da ta gani jiya. A ranta tace ita ta jawa kanta, bata san dalilin da yasa take manta waye Ammar ba, wanda tun suna yara ya tsane ta, toh me zai sa wani abu ya canza yanzu?
Tana jin kunya idan ta raya a zuciyarta taji dadin wannan kiss din da yayi mata. A jiya tasha kuka cikin dan sahun da ya kawota gida. Ba wai tana kukan damuwa bane kawai, har da kukan haushi da takaici. Ba shi kadai take jin haushin sa ba, har da kanta. Wannan yanayin da take ciki ya sake tabbatar mata da irin galabar da Ammar yayi a kanta. Babu wani namiji da ya isa ya sata a wannan halin bayan shi. Ta kasa gane abinda take ji game da shi, idan ma sonshi take, shi ba sonta yake ba. Kuma dab take da yin hauka koda sunyi auren, koda kuwa auren wasa ne.
Tana tunanin lokaci yayi da iyayen su zasu fahimci ba mai yiyuwa bace tsakaninta da Ammar.
Da wannan tunanin tayi bacci jiya. Yanzu da ta tashi, taga baccin da tayi bai wuce na awa biyu ba. Ba wai dan ya isheta ba, ta tashi ta shiga wanka. Bayan ta fito, ta shirya tayi sallah sannan ta sauko kasa wajen mahaifiyarta dake karyawa.
Koda ta sauko, Mahaifiyar tata ta shiga yi mata fada.
“Saida fa na fada miki kece zaki yi girki yau. Tun karfe bakwai ya dace ki tashi dan ki fiddo nama. Kin fi kowa sanin lokacin da yake dauka kafin ya daskare sannan a soya.”
“Please Mama, kaina ne ke yimin ciwo. Ban yi bacci ba jiya.”
Tashi Mami tayi ta karaso inda Hafsat take tareda kallon idanun Hafsat da suka yi ja.
“Meke faruwa? Me ya hana ki yin bacci?”
Bata sani ba ko ya dace ta fadawa mahaifiyarta amma sanin halin da ake ciki shi yafi. Bayani tayi mata kan wulakancin da Ammar yayi mata da kuma korar karen da yayi mata daga gidan dan uwanshi. Wajen kiss ne kawai ta cire bata fadawa Mama ba.
Akasin abinda tayi tunani, cikin sanyin murya Mama tace
“Me kike son ayi yanzu kenan? Kinsan wannan auren yanada muhimmanci a family nan. Alakar ki da shi na sani da wahala, amma kema baki ganin ya kamata ki dinga jurewa? Kiyi kokarin fahimtar shi da kuma rarrashin sa? Maza kamar yara suke, saida rarrashi. Tattalin su kawai ake, yanzu zaki ga ya sauke duk wani aji nashi, yana miki biyayya yanda kike so.”
“Ina ga baki fahimta ba Mama. Mutumin nan ba sona ne baya yi ba, ya tsane ni ne. Ki yarda da ni abinda yayi min jiya, kalilan ne akan wanda ya shirya min idan na aure shi. Ina son taimakon baba da kamfani, haka ina son lafiyar kwalwarta kuma na cancanci namiji mai sona ba wanda yake kamanta ni da karya ba.”
“Kenan kina nufin ba zaki aure shi ba?” Mama ta tambaye ta da mamaki.
“Shi da kanshi ne ma ba zai amince da auren ba.”
“Mahaifiyarshi zata ji da wannan, ke dai ki fada min idan kina son auren.”
“Koda Mahaifiyar shi tayi abinda zai amince, nice zan wahala..”
“Kiyi tunani da kyau, kar ki watsawa mahaifinki kasa a ido. Kinsan iya adadin yanda ya kwallafawa abun nan rai.”
“Mama kinsan ina sonku, kuma bani da kamar ku a duniyar nan. Zan iya yin komai a kanku amma wannan gobena ce, kuma kin fi kowa sanin haka. Idan har na aure shi, zan kasance daga ni sai shi a cikin gidan, babu wani da zai kawo min dauki.”
“Hafsat me kike son na cewa mahaifinki? Yanzu ki barni inyi magana da mahaifiyar Ammar, zamu nemi mafita tare.”
“Mafita kawai ita ce a bar zancen auren nan, domin farin cikina ne a hatsari.”
YOU ARE READING
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
HorrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...