Sarat ta yanke shawarar tunkarar Ammar. Sai da tayi kokowa akan hakan sau ba adadi kafin ta yanke wannan shawarar. Ta ɓata dare da rana tana tambayar kanta idan yiwa oganta maganar aure ba zai sa shi ya gudu ba domin duka su biyun basu san wanne suna zasu baiwa alaƙarsu ba.
Idan da ta ita ce, bata ƙi su cigaba da rayuwarsu a haka ba, ba tare da tayi masa zancen aure ba, amma yanzu da mahaifiyarta ta shigo zancen, wani labarin ne kuma daban. Kuma mahaifiyarta ta sanar da ita cewa tayi kuka da kanta idan wani abu marar kyau ya biyo baya. Tana son itama a kirata matar wani, amma tana tsoron yi masa maganar dan kar ya gujeta kuma ta rasa shi gaba ɗaya.
Jiya tayi magana sosai tsakanin ta da mahaifiyarta. Tana son jin takamaimai makomar alaƙar ƴarta. Ta tambayi Sarat idan eh ko a'a wannan saurayin yana sonta ne da aure, saidai ko ita ƴarta bata san amsar wannan tambayar ba. Sai lallaɓa mahaifiyarta tayi akan wannan satin zata ji daga Ammar.
Dan haka Sarat ta yanke shawarar yi masa magana yau. Sasai take cikin zullumi. Tana jin tun ranar da mahaifiyarta ta rutsa su a gidanta, Ammar yake wasan ɓuya da ita. Amma yau ta ɗauki ƙwarin gwiwarta hannu biyu ta tsara musu inda zasu haɗu.
Bayan ta sauka daga aiki, ta jira shi bakin motarsa kamar yanda suka tsara. Bayan wasu mintuna Ammar yazo. Suka shiga kallon juna na wasu daƙiƙu kafin ogan nata ya yanke shurun ta hanyar jin yanda take. A sanyaye Sarat ta amsa sannan ta shiga motar bayan ya buɗe. Cikin motar shuru kowanen su yayi, babu wanda ya iya cewa ƙala. Wannan yanayin sabo ne gare su kuma yanayi ne mai cike da takura. Sarat yi tayi kamar hankalinta na ga wayarta shi kuma Ammar ga tuƙinsa.
Bayan sun ƙaraso hotel, suka wuce sama. Sarat bata nadamar zaɓar wannan wurin domin tana ganin nan ne zasu samu damar yin magana a nutse.
“So, how are you?”
Muryar Ammar ta dawo da ita daga duniyar tunani. Taji daɗi da shine ya fara magana.
“Fine, kai fa?" Ta bashi amsa.
“Komai lafiya, sai wasu ƴan matsaloli na cen da in da ba za'a rasa ba amma kin san ni, a koda yaushe ina managing situation.” Cewar Ammar.
“Yayi kyau, na lura tsawon watanni kenan bamu yi magana ba." Cewar Sarat.
Kallonta Ammar yayi sannan yayi murmushi.
“Nima yanzu nake lura gaki gani.”“Ni nafi tunanin kana guduna ne tun ranar da mahaifiyata tace kazo ka nemi aurena."
“Ba gudunki nake yi ba, akwai wasu matsaloli ne da nake son gyarawa kuma da gaggawa. Har barin zuwa aiki nayi akan hakan."
“Kenan baida alaƙa da maganar aure?”
Ammar bai bata amsa ba. Bai gudunta haka kuma baya son aurenta. Bai san ta yaya zai faɗa mata ba ba tare da ya cutar da ita ba.
“Kina ji, a halin yanzu akwai abubuwa da dama a gabana, aure shine na karshe a list ɗina. Amma nayi miki alƙawari zan yi tunani a kai kin ji ko? A halin yanzu zan ji da kaina ne da kuma familyna.”
“Kenan..baka ce a'a ba..? Da gaske zaka aure ni?"
Wannan karon ma Ammar bai amsa mata ba amma Sarat ko a jikinta. Taji abinda take son ji. Yace zai yi tunani, zai iya auren ta kenan. Sosai ta cika da murna ta yanda bata lura da shi yanayin da yake ciki ba. Shi kuwa yayi hakan ne domin ya ɗauke mata hankali na wani lokaci kafin ya samo hanyar da zai bi ya datse wannan alaƙar tasu ba tare da wata matsala ba. A halin yanzu kula da ƙanwarsa Afnan shine a gabansa.
A BANGAREN KHADIJA
Har yanzu bata dawo daidai ba tun bayan wannan mafarkin da tayi. Tun wannan daren, bata sake kwana ita kaɗai ba. Tana iya yi ne kawai idan Salmah na nan. Mafarkin yayi mugun tsorata da yasa har yanzu bata samu kuzarin faɗawa Kamal cikin da ke gare ta ba. Amma yanzu jin ta ɗan samu sauki ta shirya musu haɗuwa a wata babbar restaurant domin yi masa maganar. Bayan abinda ya faru, bata son sanar da shi kai tsaye a kowanne irin wuri, tana son sai ta ɗan saki jikinta kuma ta manta da abinda ya faru. A yanzu, Khadija ta yanke biyewa zuciyarta da kuma ƙin bai wa maganganun Amriya muhimmanci.
YOU ARE READING
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
HorrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...