SO KO WAHALA PART 3

54 5 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

             *NA*

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486

        ▶️3️⃣

10/Shauwal/1442- 22/5/2021

       ASALIN LABARIN HALEEMA

     Haleema Bukari ƴa ce ga Alhaji Abubakar Mai nasibi. Mahaifin Haleema ɗan asalin Jahar Kano ne . Sana'arshi ɗaya Fatauci daga wannan gari zuwa wannan garin. A ƙarshe Allah ya zaunar da shi a Jahar Kaduna.

    Tsayawa lissafa adadin matan da Alhaji Bukar Mai nasibi ya aura ɓata lokaci ne .A taƙaice sai da ya Auri mata biyu kafin ya Auri Babarsu Leema . Bayan nan ne kuma ya yi ta aure-aure kafin daga bisani ya haƙura ya zauna da matansa ukku Babarsu Leema,Hajiya Babba uwar gida sai  Umma Amarya. Ƴaƴan babansu leema talatin da biyu,biyu sun rasu saura talatin cif a raye Maza sha takwas sai mata sha biyu.

    Alhaji Bukar ba shi da matsi ga ƴaƴansa ,musamman mata. Ko daga aji uku na ƙaramar sakandare yarinya ta sami miji aurar da ita ya ke. Mazan kuwa da yawa ba su yi dogon karatu ba iyakacinsu sakandare ,su ka fara neman kuɗinsu.

   Tun da leema ta tashi yarinya ce mai ƙwazo ,da  neman na kai. Sai dai a lokacin da ta ke ƙulafucin karantar nursing , karayar arziƙi ta kama Babansu . Kusan ƴaƴansa ne ma ke riƙe da gidan .

   Da daɗi ba daɗi ,haka Leema ta daure har ta kammala karatunta . Ba ɓata lokaci ta sami aiki a Asibitin Zaria .

Ba ƙaramin farin ciki ahalin Leema su ka shiga ba, musamman ƴan uwanta na ɗakinsu . Sun ɗora duk burinsu a kan Leema da kuma ƴar sana'ar da mahaifiyarsu ta ke yi.

     Sam a tsarin Leema ba tunanin aure a kusa a wurinta . Saboda a cewarta ba ta son damuwa , ƙanwarta Saudat kuwa ƴaƴanta ukku da cikin na huɗu . Duk wata buƙata da mahaifin Leema ya ke da ita, kai tsaye zai tambayeta. Kuma ta masa ba ɓata lokaci, shi ya sa su ka ɗau son duniya su ka ɗora mata.

    Son kuɗi irin na Leema bai barta ta tsaya ga aikinta ba kawai, ta na business sosai da sosai. Don har lefe ta ke haɗawa bashi ko kuɗi hannu. Tana kuma harkar furnitures kayan kitchen ,a taƙaice dai Leema komai da ruwanka ce. Don a ganinta albashinta baya isarta. Haka ta yi ta shiga adashi ,har jarinta ya kai 1.5 miliyan ɗaya da rabi. Tafi zuwa Kano sarin kayanta ,don sam ba ta jin wahalar zuwa kano musamman daga zaria .

    Kullum idan ta je Kano a gidan Yar Mamanta ta ke sauka, sai ta gama saye sayenta sannan ta koma gida.

Kaf a ƴaƴan Yayar Mamanta sun fi shiri da Auntin Kano , don ita mace ce mai faɗa sosai sai dai tana da kirki. Kuma a nan gidan iyayenta ta ke da zama ,saboda kula da mahaifiyarta. Da ƙyar mijinta ya yarda ,da ya ke matafiyi ne. Kuma ɓangarenta daban a gidan . Shi ya sa sau tari idan Leema ta je a ɓangarenta ta ke sauka.

   HAƊUWAR LEEMA DA YUNUS(Baban Mama)

    Zaune ta ke a shagon Muttaƙa , tsaki ta ƙara ja ta na miƙewa a lokaci guda tace "Muttaƙa gaskiya na gaji da jiran kayannan. Tun ɗazu na ke tambayarka sai ka cemin wani ya kusa isowa. Tun farko sai da na tambayeka akwai kayan kace min akwai, da kasan babu ai bai kamata kasa na baro Zaria ba."

Sai da Muttaƙa ya nisa sannan yace "Na yarda na yi kuskure don Allah Dr Leema(duk ƴan kasuwar haka su ke kiranta Dr) ki tsaya . Ban taɓa tunanin za ki rigasa isowa ba." 
"Shi kenan Muttaƙa ba komai, gobe na dawo na karɓa don sauri na ke yanzun". Ta zari jakarta ta nufi ƙofar da sauri . Karo ta yi da mutum shi ya sawo kai ita kuma ba ta lura ba , tsugunnawa ta yi ta tattaro masa takardunsa da wayarsa da su ka zube ,ta miƙa masa ta bashi haƙuri .

Da sauri Muttaƙa ya ƙaraso ya ce "Subhanallahi Oga ayi haƙuri, Dr Leema ki tsaya ga kayan sun iso." Sai da ta ɗan yamutsa fuska,ta taɓe baki sannan ta koma gefe .

Wannan mutumin ne ya dubi Muttaƙa yace "Ka yi haƙuri, mota ta ce ta ɗan ban matsala shi yasa ban ƙaraso da wuri ba." Muttaƙa ya ce ba komai Oga da ma rabin kayan Dr leema ce za ta karɓa , ta daɗe ta na jira har za ta tafi sai kuma ka ƙaraso." Ya ƙare zancen ya na nuna Leema da fuskarta ke murtuke alamun ta ƙosa . Cikin Mamaki wanda aka kira da Oga ya ke duban yarinyar,don kuɗin rabin kayan da yawa. Bai dai ce komai ba ya ɗauke kansa ,ya cigaba da rubuce-rubucensa.

Ba a ɗau lokaci ba aka ware mata na ta kayan ,yaran shagon su ka fitar mata da su bakin titi.

Wani abin takaici tafi minti talatin a gurin ba ta samu abin hawa ba ,don yamma ta yi. Gefe guda ta samu ta jingina jikin wata mota.

Ƙarasowar su Muttaƙa wurin ne ya sa ta matsa daga jikin motar, ba ta jin me su Muttaƙa su ke faɗa ta dai ji su na ƙyalƙyala dariya . A take ta tsargu, ranta ya yi mugun ɓaci.

A tare su ka ƙaraso wurin Muttaƙa ya ce "Dr har yanzu ba ki sami mota ba ko? Ki shiga Oga ya sauke ki mana." A fusace ta juyo.............

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU

MUM AMNASH🖊️

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now