SO KO WAHALA PAGE 28

34 3 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

           NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
*WATTPAD@mumamnas2486*

*Watsapp link* https://chat.whatsapp.com/Gty1kpVjvrb2myAy87gOou

1/Zul-Hajj/1442 - 10/7/2021

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

      2️⃣8️⃣

  "Hadiza kuka ba naki ba ne, kamata yayi ki faɗa mini dalilin da yasa ki ka kirani, don wallahi ko izinin mijina ban nema ba na fito." Hajiya ta ƙare zancen tana gyara lulluɓinta, Share hawayenta ta yi tace "Hajiya ashe Baban Mama yaudarata ya yi ba wasu manyan kuɗi a hannunsa, Hajiya lefenma da ya haɗomin kuna zuzutawa da kuɗin bashi aka haɗo, in taƙaice miki kusan komai na bikin da bashi aka yi shi..." Cikin kiɗima Hajiya ta dafe ƙirji tace "Bashi!" Hadiza tace "Ƙwarai bashinma a wurin budurwarsa ya karɓa, don kawai ya zubar min da mutunci, itama kuma wai aurar ta zai yi nan da ƴan watanni." Ta ƙare hawaye na bin kuncinta.

"Abida tayi gaskiya, ta faɗa mana yafi sau shurin masaƙi mutumin nan  ba shi da kuɗi  sai rufin asiri, amma muka ƙi yarda, to yau ga abinda ya faru. Ko mu da muke Ayyuhal faƙara'u dangin babu ba mu ci bashin kowa ba muka yi miki kayan ɗaki. Allah ya sauwaƙe ya rabamu da bashi, da badon ba a saurin yanke ƙauna ba daga rahamar Ubangiji,  tabbas da na ce daɗin da muke hari ta wajenki ba zai samu ba."

Baki a buɗe Hadiza tace "Hajiya to ya zanyi?" Sai da Hajiya ta miƙe tsaye sannan tace "Addu'a, sannan ki koma Makarantar da kike koyarwa ki cigaba da ƙarɓar ƴar dubu ashirin ɗinki, idan ba haka ba ko fiyowotan (pure water)da zaki bawa baƙi sai kin rasa." Har ta fara takawa ta dawo baya tace "Kar ki  yarda ki sake komawa gurin wani Malami ko da Malam Labaran ne, don duk kusan Malaman nan na zamani ance macuta ne, kissarki da iya mu'amala su ƙwace ki, kiyi ƙoƙari ki kanainaye Uwarmijinki..." Katse Hajiya ta yi tace "Wa! wai Babar Yunus to ai Hajiya ta fimu son abin duniya, don itama ido a kwabo ce. Idan kika ga yanda take karrama wannan shegiyar budurwar tashi, sai kinyi mamaki."

Gaba Hajiya tayi tace "Ai ko ni banga laifinta ba, yaushe za ka riƙe wanda ba citta ba data a hannunshi, Allah ya fitar da ku. Idan kuɗin Adashin sun samu kya zo gidan mu tattauna, na barki lafiya." Ta fice da sauri, a ƙofar gidan suka yi karo da Baban Mama ko gaisawar kirki ba suyi ba, ta wuce da sauri. Da kallon mamaki ya bita har sai da ta kusa shiga gida sannan ya shiga cikin gidan riƙe da ƙaramar leda a hannunshi.
     
  Jin ya doka sallama ba'a amsa ba ya sa ya shiga Falon kawai, lintsim ya faɗa kan kujera don a gajiye yake sosai, hakan ya yi daidai da fitowarta daga banɗaki.

Fuskarta a tsuke tace "Haba Yunus ai sai ka dinga zama a hankali, kar ka ɓirman kujera, kujerun zamani da ba wani kwaliti garesu ba."

Dariya yayi sosai yace "Sai dai idan kujerun naki ruɓaɓɓu ne, ke ni ba wannan ba, na kwaso ta maguwa(yunwa) zo ki gani" ya ƙare yana ɗaga ledar hannunshi sama, da sauri Hadiza ta ƙaraso don ta ɗauka wata didimarce(kayan daɗi) a ledar.
Buɗe ledar ya yi sai ga rabin kabeji da ƙaramar kwakwanba har da tumatir guda uku, miƙa mata yayi yace "A gidan Hindu na samo, da har za ta yankamin nace ta barshi don naga unguwa za ta tafi. Ki yanka min ki wanke tas, don Allah ki kulamin da kayana kar ki kwashe ki cinye, kinsan lalurata likita ya hanani naɗar carbohydrate (Abincin da yake ƙara ƙarfi, kamar :shinkafa, tuwo, doya, garri da sauransu) sai na haɗa da ɗan ganye."

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now