SO KO WAHALA? PART 14

40 2 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

           NA

MARYAM MUHAMMAD SANI (Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486
BLOGSPOT@mumamnash.blogspot.com

5/Zulƙida/1442  -  14/6/2021

  ASSALAMU ALAIKUM MASOYA DA MARUBUTANMU NA DAWO, INA MATUƘAR GODIYA GA ƊAUKACIN WAƊANDA SU KA HALARCI  BIKINMU ,DA WAƊANDA SU KA MANA ADDU'A ,ALLAH YA BAR ZUMUNCI NA GODE .

     1️⃣4️⃣

    A lokacin da rayuwa ta yiwa Baban Mama da Hindu daɗi , to a wannan lokacin rayuwar mutune uku ke cikin garari da neman mafita .

   A ɓangaren Leema ba ƙaramin namijin ƙoƙari ta yi ba wajen danne son Baban Mama, duk da yanda zuciyarta ke azalzatarta . Amma ta yi alƙawarin ba za ta zo Kano ba sai ya nemeta, kuma ko da kasuwancinta ya kawo ta a ranar za ta sayi komai ta ke so, ta juya Zariya.

   Dr Zayyad kuwa sai da ya nutsu ya zurfafa tunani, sannan ya gane shima son Leema ya ke. Abinda ya fi ɗaure masa kai ba ta da kwalitis ɗin irin macen da ya ke ra'ayi . Amma tsabar janyo jidali da ɗaukarwa kai dala ba gammo, zuciyarsa ta jajiɓo masa abinda ya fi ƙarfinshi. Ba ɓata lokaci ya yanke shawarar komai zai faru ya faru.

***********
 
   "Ke kuwa Hadiza ko ƴar kunyar nan ba kya ji , ƙemadagas akan yaron nan nema kike ki koyi fitsara eyee" Sai da ta ɗana bakinta sama sannan ta ce "Haba Hajiyata ,wallahi tsoro na ke yi kar ya dawo ya ce ya fasa aurennan shi yasa. Amman tunda ina da ke ai an gama komai wallahi , Hajjaju Makkatu" ta ƙare zancen da wata malalaciyar dariya . Mayafi Hajiya ta ja ta ce "Kinga miƙe mu je da zafi-zafi akan bugi ƙarfe , ba a bori da sanyin jiki.

   Abida da ke laɓe a bakin ƙofar da sauri ta shige lungun da ke gefen ɗakin ta wayance da share-share.

   Hajiya ta ce "Ke Abida za mu fita da yayarku , ba daɗewa za mu yi ba, ki tabbatar kin gyare gidannan, sannan idan kinji mu shiru to ki ɗaura girki idan na dawo sai na karɓeki ."

Da fara'a ta ce "To Hajiya sai kun dawo Allah ya bada sa'a ." "Ameen" ta ce su ka nufi waje . Da ƙafa su ka gangara har gidan Malam Labaran cikin sa'a  ba su tarar da wani layi ba sosai .

Layi na zuwa kansu su ka yi wuf su ka shiga. Kallo ɗaya Malam Labaran ya yi musu ya ɗauke kai. A ɗage ya ce "Me ke tafe da ku?" Gyara zama Hajiya ta yi ta ce "Ƴata ce Hadiza ta samu mijin aure, to amma matsaloli masu yawa na sako kai daga ɓangaren matarshi da kuma wata hatsabibiyar yarinya . San..."
"Ya isa hakanan me yasa kika fiya ƙorafi da yaws ne? Ke yarinya matso nan na tambayeki." Cikin rawar jiki ta matsa kaɗan , taɓe baki ya yi sannan ya ce "Ya sunan matar tashi da ita ɗaya yarinyar" Baki na rawa ta faɗa mishi . Bai ƙara ɗago kanshi ba ya duƙufa zane-zane a kan ƙasar da ke kan ƙaton faifan da ke gabanshi . Ya zane ya share ,sai da ya yi har sau ukku sannan ya dubi Hadiza ya ce "Tun da na fara abu ɗaya na ke gani , tabbas akwai aure  tsakaninku , sai dai kuma akwai ƴar matsala ita ma ɗaya yarinyar da ki ke magana akwai yiwuwar ya aureta sai dai ba ni da tabbas. Yanzu me kike so ayi ,shin kina son a rabashi da Matarshi sannan a rabashi da ɗaya yarinyar ma'ana na musu farraƙu ko me kikeso a yi?" Cikin karkarwar jiki Hadiza ta ce , idan ba za ka damu ba ka bari na yi shawara tukunnah daga baya sai na zaɓi abinda zan yi musu . Amma yanzu ka yi mini aikin da zai ƙaunaceni fiye da kowa."

Wata ƙatuwar dariya ya yi , sannan ya miƙa mata wani shimfiɗeɗen carbi ya ce ɗauki ɗaya . Ba ɓata lokaci ta zaɓi ɗayan , murmushi ya yi ya ce kin dace . Magani ƙwaya ɗaya jal ya bata ya  ce "Gashi nan ki tabbatar kin zuba masa a abinci ya ci, da zarar ya ci magana ta ƙare. Ku tashi ku bani waje ,idan kin dawo kya biya kuɗin . Jiki a sanyaye su ka nufi gida.

    Tun da su ka koma su ke shawarar yanda za'ayi a zubawa Baban Mama maganin , amma abu ya faskara . Duk sun san Abida ita kaɗaice ke shiga wurin Hindu sai dai kuma ba ta tare da su .

   Ta ƙofar labule ta ke leƙensu ,tsaf ta gama jinsu ,wani murmushi ne ya suɓuce mata, ta tura kanta ɗakin.....

ƊAN KAƊAN NE PLS KUYI MANAGE ,WALLAHI INA TYPING INA GYANGYAƊI MU HAƊU GOBE ,SAI NA ƊORA INSHA ALLAHU

ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU

MUM AMNASH🖊️

SO KO WAHALAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin