SO KO WAHALA? PART 60

31 4 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*
      
               NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)
*WATTPAD: @mumamnas2486*

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*

Shahararriya kuma haziƙar marubuciyar nan taku AMEERA ADAM ta sake zuwar muku da wani ƙayataccen littafi mai ɗauke da rikici da tirka tirka, ƙulle-ƙulle da makirci mai suna *ANYA BAIWA CE?* Anya Baiwace littafine na gidan sarauta, kuma littafin kuɗi ne. Ga mai buƙata zai same shi a farashi mai sauƙi kamar haka👇👇👇
Normal Group: #200
VIP GROUP: #400
ACCOUNT: First Bank 3090957579 AISHA ADAM
SHAIDAR BIYA TA: 07062062624
Amma don Allah don Annabi (S.A.W) idan kin san za ki fitar mata da littafi gwara a haƙura👏

8/R-Auwal/1442 - 14/10/2021

             6️⃣0️⃣

  Kai tsaye Leema Sabuwar Gandu ta nufa, don ta ɗokanta da ganin Isa. Duk da da mukulli a hannunta ƙwanƙwasa ƙofar ta yi, don ta yi masa bazata, ta ƙwanƙwasa ya yi kashi uku ba alamar za a buɗe. Ganin haka yasa ta ɗan matsa baya ta duba rariyar gidan. Gabanta ne ya faɗi ras! Ganin rariyar a bushe, babu ko alamun danshi ballantana gudanar ruwa. Jikinta a sanyaye ta ja ƙafafuwanta ta nufi gidan su Salaha, don tasan komai yake akwai a can za ta samu bayani.

"Assalamu Alaikum"
"Wa'alaikumussalam. A'a Sadiya ke tafe? Sannu da zuwa shigo daga ciki mana, kin tsaya kamar wata baƙuwa." Kaka ta ajje ƙyallen tatar da yake hannunta suka shiga ɗaki.

A gefen tabarmar karaunin da ke malale a ɗakin ta zauna, kanta a ƙasa tana murza zoben da ke yatsanta na kusa da ƙarami. Muryar Kaka ta tsinkaya tace "Sadiya ya mai jikin? Ko ba ki je Asibitin ba?"

Jikin Leema na rawa kamar mazari tace "Kaka waye ba shi da lafiya?"

"Eh to, bana ce ba gaskiya. Amma ki shirya mu tafi can gidan na ku, daga can sai mu ji me yake akwai, kin san gogannaki da shiririta bai faɗa mini ba."

Ajiyar zuciya Leema ta sauke jin ba Isa ba ne ba shi da lafiya. Ta ɗan samu nutsuwa kaɗan, duk da har lokacin gabanta na faɗuwa.

Salaha na dawowa daga aiken da a ka yi mata, suka kimtsa suka nufi gidan Mama.

Suna zuwa suka tarar da su Mama da Hajiyan Khamis za su tafi Asibitin. Ba ɓata lokaci suka nufi Asibitin. Suna gab da shiga Asibitin Hajiya tace "Haleema Mijinki ne baya ɗan jin daɗi, amma da sauƙi sosai shi yasa ba mu kira ki ba, gudun kar hankalinki ya tashi amma..." Ganin gaba ɗaya hankalin Leema baya kanta yasa ta ja bakinta ta tsuke. Khamis na tsayar da motar ta dubeshi da fuskarta mai ɗauke da matsananciyar damuwa tace "Wane ɗaki?"
"Male ward, Aminity room 4 ( Ɗaki na musamman a Ɗakin Maza)" Ba ta jira kowa ba, ta nufi ɗakin jikinta na rawa, don A.K.T.H ba baƙonta ba ne, ta saba zuwa tare da Baban Mama da su Dr Zayyad.

_____________________

  "Ƙudugis! Ƙudugis!! Ƙudugis"

"Hahahahahah! Boka Ƙudugis na yi maka barka da zuwa ya kai Bala, shu'umin bil'adama kura da fatar akuya, simu-sumu mugun micijin sari ka noƙe."

"Godiya na ke ya shahararren Bokan da ya gagari ƙananun ƙwari. Sun ja da kai sun barka, dakalin majina a hauka a zame ka hau mutum ka zauna daidai. Sai Boka Ƙudugis uban gidan jinnu da mutane. Gulbin barkono ka ke iya kar mace ƙauri. Gani zube a gabanka ya Ƙudigis, a ƙara taimaka mini kamar yanda a ka saba." Bala ya ƙare yana duban Boka ƙudugis, da ke hakimce a kan wani tattausan kilishi, da kuma faranti mai ɗauke da ƙasa a gabanshi.

Zane ya fara yi a kan ƙasar, ya yi ya goge, har Allah ya gajicceshi. Fuskarshi a murtuke yace "Bala ka cika son kanka da yawa. Me yaron nan ya yi maka ka ke neman saka rayuwarshi a masifa?"

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now