SO KO WAHALA? PAGE 29

37 2 1
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                  NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486

BISMILLAHIR-RAHMANIRRAHIM

  *Assalamu Alaikum gareku masoyan littafan Mum Amnash, insha Allah bayan sallah babba da sati ɗaya zan fara wannan littafin na ƳAR HISBA  bazance komai ba akai, amma insha Allah zai ƙayatar. Littafin na kuɗi ne za'a biya kuɗin karatu naira #200 normal group, #300vip posting sau biyu a rana, Waɗanda ke son special kuma #400 a dinga tura musu ta pc. Za'a tura kuɗin ta wannan Account 2083460164 Abubakar Abdullahi  Zenith Bank, sai a tura shaidar biya ta  07038826617 ko a tura katin MTN ta wannan number*

      
       2️⃣9️⃣

   Likita na shigowa ya tarar da Inno sai tisa lissafi take, kamar wasu kuɗaɗe masu Uban yawa ta samu, yace "Mama lafiya ta samu ko?" Sai da ta zuro ƙafafuwanta ƙasa sannan tace "Ƙwarai da aniya Yaro, ko ba ka zo ba, dama ina shirin a kirawo mi ni kai, don so nake yau-yau na koma gida." Murmushi Likitan ya yi, yasa magwajin auna hauhawar jini ya auna jininta(Blood Preasure B.P) Cikin fara'a yace "Gaskiya zan tambayi Yunus wane irin magani ya baki da kika miƙe cikin ƙanƙanin lokaci haka, muma a bamu mu dinga bawa marassa lafiyarmu." Sai da Inno ta adana kuɗinta a kaja (Jakar da tsofaffi ke ɗaurawa a ƙugu kafin su sanya zani) sannan tace "Ɗannan ko ka tambayeshi bazai faɗa maka ba, don abin sirri ne, ka rubuta mana sallama mu tafi kawai." Ba ɓata lokaci a ka sallamesu suka koma gida.

Duk wani tsari na Baban Mama ya baje, don duk ƴan kuɗaɗen da yaso tattalawa don kar wani watan ya zo musu da matsala tofa sun tasamma ƙarewa. Shiyasa kawai ya cigaba da yin komanshi gaba gaɗi.

  Ana fara yin salary Idris mai kanti ya isheshi da waya, ana sa masa kuɗi ya tura masa dubu ɗarinshi. Sauran kuɗin kuma shawara ya farayi kan abinda ya kamata yayi, tunowa da sauran dubu Hamsin ɗin da Mijin Aunty ya ke bi yasa ya turawa Aunty dubu Hamsin ya yi mata bayani, yace "Aunty ga kuɗin Yayanmu ki bashi, Inno ce bata da Lafiya kusan kwananta uku sannan aka sallamota. Don Allah ki bawa Hadiza Haƙuri ba kuɗi a hannuna." Cikeda tausayawa Aunty tace "Na gode sosai Yunus don Allah ka yiwa Inno sannu insha Allah anjima da yamma zan zo na dubata, ba wata damuwa zan faɗawa Leema." Godiya yiwa Aunty sannan ya kashe wayar.

  Ko da Aunty ta faɗawa Leema bata wani damu ba, don ita a ganinta rashin lafiya ta kori komai.

BAYAN SATI ƊAYA

   Leema dai a karo na biyu ta ƙara shiga halin ha'ula'i don ɗaukar wani Alhaji Mansur ne, kuma ma'aikacin Banki ne, rana ɗaya aka rage ma'aikata har da shi a ciki. Da yake yana kasuwanci sai ya cewa Leema ta bashi kuɗinshi ya ƙara jari ya biya kuɗin haya dubu ɗari biyu. Haƙuri ta bashi don Mutumin kirki ne, gudun kar ta kunyata a canfa Adashinta yasa ta tambayi Zahra ƙawarta kan ya zatayi.

Sai da Zahra ta mata faɗa sosai sannan tace "Kawo kunnenki ki ji" Ƙus-ƙus ta yi mata sai kuma suka kwashe da dariya.

   A ranar Leema ta nufo Kano, sauran tsarin Zahra ta gama shirya musu komai don ta kira Yayarta Zubaida, tsohuwar Uwar dashi ce, da ta san kan tsiya. A ranar sukaje da Leema ta nuna musu gidan Hadiza da gidan Hindu tace "Aunty Zubaida a cikin ɗaya daga cikin wannan gidajen za'a sameshi, nasan mai zance masa, mu tafi kawai." Haka suka juyo suna ƙulla abinda za su gabatar a gobe.

Washegari kuwa da wuri suka hawo Adaidaita sahu, amma Aunty Zubaida bata fito ba juyawa tayi ta koma bayan sun tabbatar Baban Mama na gidan Hadiza.

   Baban Mama na zuro kai gabanshi ya faɗi ganin wani gabjejen ƙato, tsayuwarshi kawai ta isa ta tabbatar maka da tsagwaron rashin mutuncinsa, don kanshi duk tabon ɗinki ne, da alama dai ruƙaƙƙen ɗan daba ne a da, tsayuwarshi kawai abar kallo ce don ya harɗe hannayensa ta baya ne, ƙafarsa ɗaya ya jefata gaba ta wani karkace , ɗayar kuma tana baya. Buɗe baki Baban Mama ya yi ganin tare suke da Leema a tsaye.

SO KO WAHALATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang