SO KO WAHALA? PAGE 70

24 1 0
                                    

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EiQ3qtht0QSLRElOcqt3CP
[11/13, 8:12 PM] Mum Amnash: *HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)
WATTPAD:mumamnas2486

6/R-THANI/1443 - 12/11/2021

                  7️⃣0️⃣

Jimami Malam ya aro ya yafa a fuskarshi, sannan yace "Kayya! Kaka kasa dakatar da su na yi. To kuma...sai a ka yi sa'a ma izinin fara zuwa taɗi suka tambaya. Kin ga cikin ruwan sanyi idan Salaha ta ƙi shi, babu ruwanmu. Kuma Isa ba zai ga baƙinmu..."

"Kai rufewa mutane baki! Sai faman zuba ka ke kamar kabare, ka cika ɗan karen surutu da faɗi ba a tambaye ka ba kamar waziri aku."

Sai da Kaka ta nisa cike da takaici sannan ta ɗora "Ni kai tsaye ai cemaka na yi ka ce an yi mata miji a ƙauye. Ka ga tunda suna da hankali, ai ba za su yi nema cikin nema ba. Amma da yake kai zabo ne, sai ka kasa faɗa musu. Amma babu komai, ba a ƙin ta mutum. Nama san Salaha babu yanda za a yi taso wannan balaƴaƴƴan."

Shi dai Malam zare jikinsa ya yi ya fita rumfur waje. Hankalinshi a kwance ya zaro hula ya cigaba da ɗinkinshi.

Su Gambo kuwa baki har kunne suka labartawa su Mama abinda ya gudana tsakaninsu da Malam. Su  ma sun ji daɗi sosai, dama haka suka zata daga wurin Malam ɗin. Sai dai tantamarsu ɗaya, kan zancen Karatun Salaha ne, wannan kuma dole sai Kabiru ya zo.

Washegari da Safe lokacin ya je ma'aikatarsu, Hajiya ta kirashi. Cikin nutsuwa suka gaisa, sannan ta kwashe duk yanda su Gambo suka yi da Baban Salaha ta sanar mi shi.

Ɗan jim ya yi bai ce komai ba, sai da Hajiya tace "Kana ki na kuwa?"
"Hajiya gaskiya ni a yanzu bana son auren mace wayayyiya sosai. Kuma karatun da yarinyar take so, bai zama lallai ta iya shi ba, saboda yana da wahala. Hajiya zama Likita a baki ne yake da sauƙin faɗa, amma a aikace ba ƙaramar magana ba ce. Hajiya indai har sai ta yi karatun mai tsaho ina ganin gwara na haƙura da ita, don babu amfanin baɗi ba rai. Ina da kuɗi da rufin asirin da zan riƙeta daidai gwargwado. Ni a ra'ayina na fi son ta zauna kawai a gida, ta gudanar da duk sana'ar da take so, amma banda dogon karatu."

"Ikon Allah! Wai na kwance ya faɗi. To kai mene ne dalilinka na ƙin ta yi karatu? Mene ne laifin mace ta yi ilimi mai zurfi? Matarka ba ta aiki? Kai ma ba ɗan bokon ba ne? Na gane saboda ita Salaha ƴar Malam Shehu ce, ayyuhal faƙara'u dangin babu shi yasa za ka killaceta a gida kamar kazar gidan gona. Ku kuma ku ci gaba da warkajaminku iya son ranku ko? Shi kenan Kabiru, duk abinda ka faɗa mini, ni na jawa kaina. Batun Salaha da yamma zan sa Mustafa ya kai ni na basu haƙuri. Dama an faɗa, ko shekara ɗari ka yi ba ka ga mutum ba, to idan ka ganshi tambaye shi wani abu banda halinshi. Dama kowa ya yi mamakin yarda da ƙarin auren da ka yi farat ɗaya, ashe kace mu jiraka ka zagayo ta bayan fage, kasan kitimurmurar da ka ke ƙullawa. Ka gaida iyali."

Kafin ya furta komai ta gimtse wayar. Hannunshi ya ɗora a kai cike da tashin hankali. Tsam ya miƙe ya fara kai wa da komowa a cikin ofishin. Shi dai har ga Allah, yarinya yake son aura ɗanya shakaf kamar Salaha, amma kuma idan ya barta ta fara dogon karatu wataƙila samun lokutanta gareshi ya zamo taƙaitacce. Ada ya yi tunanin auren mace mai ƙarancin shekaru matsala ne, amma a yanzu ko da batun shi da na Salaha ya ruguje to tabbas zai nemi wata macen ya aura, ko ba komai gida biyu maganin gobara..."

Turo ƙofa tare da sallamar abokin aikinsa ce tasa ya koma mazauninsa. Ranar haka ya yini a wurin aiki, banda saƙawa da kwancewa babu abin da yake.

Cike da mamakin ƙarfin hali irin na Kabiru Hajiya ta figi gyale ta shiga wurin Mama. Babu abin da ta rage mata, dangane da abinda Kabiru ya faɗa. Sai da Mama ta ɗan yi jim, sannan tace "Hajiya ni nafi tunanin ƙila baya samun hankalin matarshi ne sosai. To shi ne yake son ya yi amfani da damar ƙara auren ya cike gurbin da ya rasa. Kin ga idan ya ji itama za ta yi boko dole hankalinshi ya ɗugunzuma."

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now