SO KO WAHALA? PAGE 39

33 3 8
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

             NA

*MARYAM MUHAMMAD SANI (Mum Amnash)*
WATTPAD@mumamnas2486

15/Almuharram/1443 - 24/8/2021

         3️⃣9️⃣

   Kasa magana kawai ya yi ya tsaya yana kallonta, ga mamakinshi sai ya ga ta harɗe hannunta tana jifansa da wani  murmushi. A ƙufule yace "Da gayya ki ka aikata hakan kenan?"
"Ko ɗaya nima na manta da kayan ciki (under wears) a cikin kayan, da na tuna  da na cire, amma tunda na manta ai ba damuwa sai ka wanke kawai."

  Kallonta kawai ya tsaya yi, ya rasa me zai ce mata ya huce haushi kawai sai ya tsugunna ya hau dirje mata kayan. Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama ya ɗaura alwala. Har ya fita ya dawo yace "In kin ga dama ki fito ki shanya" bai jira amsarta ba ya fice da sauri. Dariya tasa kawai ta fito tsakar gidan, a zuciyarta kuwa faɗi take 'Tukunnama Isa baka ga komai ba tunda kunya gareka ni bamu haɗa hanya da kunyar ba ballantana ma na santa.'

Sai bayan sallar magriba sannan Mama ta dawo, bata cewa Leema komai ba suka cigaba da hirarsu.

  Tunda suka idar da sallar Isha'i yake zaune a gefen Masallaci, wata irin kunya ya ke ji, amma yasan Leema babu abinda zai dameta, don ta saba wankin ƙananun kayanta a tsakar gida, ta shanya abinta a igiya. Tun yana jin kunya har ya daina, don yasan Leema bata da seti sosai, tunaninta yana sikiracin (fatsi fatsi).

Da sauri ya waiwaya jin an dafashi, ganin Kamsusi ne yasa ya ƙara ɗaure fuskarshi tamau. Dariya Kamsusi ya yi yace "Ango, Ango, Ango mai shirin jin daɗi. Ni sai naga har ka fara ƙyallin amarci, shegen sama mu muna can muna ƙoƙarin haɗa maka gagarumin biki, amma da yake kai ɗan iska ne kana neman bamu kunya. Sai an yi magana ka ce baka son ta, bayan anma gama komai, kai mutumin ɗazu nayi dariya fa. Da alama kai fa irin Mijin tace ɗinnan za a yi, yi na yi, bari na bari. Wallahi ban yi tunanin za ka iya yin wuf..."

Tamkar mai shirin tada kabbara ya ɗaga hannayensa sama yace "Kamsusi na barka da Allah, wallahi ni ba abinda nayi mata. Ai nasan ko kowa bai yarda ba kai za ka yarda dani, ko kuwa?"

Wata shegiyar dariya Khamis ya yi yace "Ina mutumin! A nan fa ba batun shaida, wa zai hanaka kai da Matarka, wallahi ka gwangwaje a ɓagas ka samu, muma da za a mana haka ai da barkanmu."

A fusace ya miƙe zai bar wurin Khamis ya biyo shi yace "Haba Abokina wallahi tsokanarka na ke, ai ni nasanka ko zaka shekara ɗaki ɗaya da mace babu abinda zai faru. So ina ganin zan yiwa su Hamisu magana mu kai ka wurin Hajiya Bilkisu mai magani, don kar a zo a ji kunya. Don fankan-fankan bata kilis..." Kafin ya ƙarasa tuni Isa ya yi gaba. Haka ya bishi har cikin gidan, yana ƙwala masa kira.

----------------------------------------

   Ko da Baban Hadiza ya dawo a ka sanar dashi babu abinda yace sai "Allah ya kyauta!" Dama shi kyanwar Lami ne babu abinda ya yi masa zafi, Hajiya ke juya gidan.

Cikeda Masifa Hajiya tace "Wai kai Malam me yasa ka ke haka ne? Mutumin nan ya daki ƴar ka da ciki, amma ba zaka ce komai ba? To wallahi ya yi kaɗan, ko uwarshi taci ƙarya ta kwana da yunwa, ballantana shi karan kaɗa miya. Ofishin ƴan sanda zan je, daga nan a miƙa mu Kotu ko mu tafi Hisba. Don ni ba sallamammiya ba ce da zan zauna wani ƙaton gardi, mai zubin namijin agwagwa ya raunata min ƴa ba. Tunda da zarar ta mutu, wata zai aura mai idon ƙyalƙyala uban son mata."

Fuskar shanu Hadiza tayi tace "Haba Hajiya, to koma me ya yi mini ai ni na jawo, ko kin tambayeni abinda ya haɗamu? Ki yi ta zagar mini Miji don kinga yanzu mun dawo nan, da muna Indiya ai kullum cikin shi masa albarka ki..."

A fusace ta buge mata baki tace "Sannu sallamammiya, tattabara uwar aure da soyayya. maza ki yi mini shiru kafin na danna miki zagi, indai namiji ne ga ku ga shi. Namiji ko Gyatuminka ne ba zaka shaideshi ba, don wataran zai danƙarawa Gyatumarka harbin da ya fi na kunama zafi."

Baban Hadiza kuwa bai ƙara bi ta kansu ba ya shuri takalmanshi ya fice yana gunaguni.

  Da ƙyar Hindu ta shawo kan Baban Mama, don sai da ya huce sannan ta nuna masa illar abinda ya yi. Dole ƙanwar na ƙi ya shirya suka nufi gidansu Hadiza biko.

Cikeda farin ciki Malam ya tare su ya yi musu iso har  cikin gidan. Kuma bai yi ƙasa a gwuiwa ba, ya hau bawa Baban Mama haƙuri, sosai Baban Mama ya ji kunyar karamcin Dattijon kirki Surukinsa.

Hajiya za ta tsaya iyayi da falsafa, Hadiza ta katseta tace "Hajjaju ai ni zan bashi haƙuri, Baban Mama don Allah ka yi haƙuri, bazan ƙara ba."

Murmushi kawai ya yi, shima ya bawa iyayenta haƙuri sannan ta ɗebo takalmanta ta biyo shi. Suna fitowa ƙofar gida Hindu tace "To sai da safenku." Ba ta jira amsarsu ba ta wuce gidanta, suma suka nufi nasu.

A fuska sam Baban Mama bai nuna mata wani abu ba, amma a zuciyarshi shi ya san tanadin tsiyar da ya yi mata.

-------------------------------

   Aunty ce ta dubesu tace "Kamsusi ban san yaushe za ku yi hankali ba, tunda ɗan uwanka ya yi aure kai ma ai sai ka lalubo wata ko Bazawara ce mu ganganɗa mu kai ku, ko bakinmu ya huta."

"Yauwa Auntynmu dama zuwa nayi mu tattauna, don Allah wane kalar kaya ya kamata su saka. So nake ya fito kamar ranar ɗaurin aure, shegen sama da ya gayyacemu bikin Leema si da damu za a yi..."

Katse shi Aunty tayi tace "Baba suda uban zance, zauna musan abinyi, bikinnan jibi ne fa to a ina ma za ku sami wata babbar riga?"

  Fuskar Kamsusi a washe yace "Yo Aunty ai iya kuɗinka iya shagalinka, kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan kwano. Ready made (Ɗinkakkun kayan siyarwa) zamu siya, har hula da komai ma duk a daren nan za mu siyo fa."

"Sa kai ai yafi bauta ciwo, da wani ya saka ku wallahi da sai kun jaza masa ciwon kai. Ku shiga ciki ku tambayi Amaryar, in ka fito ka same ni a ɗaki. Saura ka zauna kayi ta zuba kamar nunanniyar kanya."

Dariya kawai ya yi ya shige cikin gidan yana kwazozo "Amarya, Amarya, Amarya mai maganar sikari."

Isa kuwa ƙin shiga ɗakin ya yi, sai da Kamsusi ya haɗa shi da Mama sannan ya shiga, fuskarshi kirtif kamar kunun kanwa. A gefen gadon Mama ya zauna, Leema kuwa tana can lungu maƙure kamar gaske.

Duk yanda Kamsusi ya so su zaɓi kalar da suke so ƙi suka yi, da yaga za su ɓata masa lokaci kawai sai yace "Kar ku zaɓa ɗin, idan an kaiku gidanku kar ku zauna. Tsabar wulaƙanci kun mayar dani kamar wani ƙwallo, mtss!" 

Har ya miƙe zai fita Isa ya riƙo hannunshi yace "Fari da golen (zaiba)" Dariya kawai Kamsusi ya yi ya wuce ya barsu a ɗakin. Sai da ya shiga ɓangaren Aunty suka ƙara tattaunawa sannan ya fice.

  A daren ranar suka je shagon sayar da kaya suka zaɓi irin wanda suke buƙata, a ka kalmashe musu ƙasan wandon da hannun rigar. Da ya ke Kamis yasan duk awon kayan Isah, shi yasa bai ƙara bi ta kansa ba.

   Washegari tun sassafe Kamsusi da sauran Abokansu suka bazama ƙarasa shirye shiryensu.

Zuwa Azahar suka kawowa Aunty katinan Dinner da za su yi, don ta rarraba duk da dai an bugo a ƙurarren lokaci, wasu sai dai a buga musu waya. Zuwa bayan Azahar kuwa ta ja gyalenta ta fita rabon kati.


----------------------------

  Inno kuwa gudun kar allura ta tono garma yasa ta kasa zuwa dubo Baban Mama, da safe ma sai ya da biyo ya gaggaisa da ƴan Kamaru  sannan ya wuce Asibiti wurin Dr Zayyad, don zaman gidan ya isheshi.

Duk yanda Inno taso ta yi masa zancen garar kasa yi tayi, yana ficewa kuwa ƴan Kamaru suka ce Allah ya karsu sai ta fito da sauran abincin an dafa, don ba zasu zauna da yunwa ba . Dole ƙanwar naƙi ta ɗauko taliyar ta miƙa musu, kan kace kwabo suka yi dafa duka mai romo romo, suka zauna suka warɓi abarsu.

Inno kuwa banda mandiri babu abinda zuciyarta take yi, ta rasa ta ina za ta lalubi bakin zaren, sai dai ta zauna ta yi girim tamkar an aiko mata da manzon mutuwa.

  Ta tayar da sallah kenan ta ji an kwaɗa sallama, wani irin bugawa ƙirjinta ya yi tace "Na shigesu Aunty a gidannan?" Sai kuma ta ƙara tayar da kabbarar sallah tayi ta jero su ba tare da tasan raka'a nawa take yi ba.


ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU

MUM AMNASH🖊️

SO KO WAHALAМесто, где живут истории. Откройте их для себя