SO KO WAHALA? PAGE 35

32 3 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA😭❤️*

          NA

MARYAM MUHAMMAD SANI
      (Mum Amnash)

INA YIWA ƊAUKACIN MISULMIN DUNIYA BARKA DA ZAGAYOWAR SHEKARAR MUSULUNCI , ALLAH YA HAƊAMU DA ALKHAIRAN DA KE CIKINTA. ALLAH YA RABAMU DA SHARRIN DA KE CIKNTA, ALLAH YA ZAUNAR DA AL'UMMAR MUSULMI LAFIYA A DUK INDA SUKE, ALLAH YA YAFE MANA KURAKURANMU YA MANA RAHAMA. ALLAH YA JI ƘAN MAGABATANMU YA MUSU RAHAMA, ALLAH YA IYA MANA ABINDA BA ZAMU IYA BA.

             3️⃣5️⃣

    Washegari da safe Dr Zayyad ya kaimasa Akwatinsa, da sauran kayan da Leema tayi masa. Dambun nama da cake kawai ya rago masa, sauran kuwa suka sha shagalinsu da shi. Bai ɓoyewa Hindu ba ya sanar da ita Leema ce ta bashi, ta karɓa ta raba har Hadiza amma da aka kai mata sai tace bata ci, suka haɗa a nasu suka cinye.

  Sai yamma liƙis sannan ya dawo hannunsa ɗauke da manyan ledoji, a falon ya ajiye ya shiga ciki.

Sai da ya kammala komai sannan ya cewa Hindu "Ɗau ledar nan guda ɗaya ki buɗe, ki duba idan da abinda bai miki ba sai na canzo miki."

Cike da farin ciki ta hau bubbuɗa kayan, atamfofi ne masu matsakaitan kuɗi, ƴan dubu shida da ɗari biyar zuwa dubu takwas guda Biyar, Shadda biyu, Leshi biyu sai mayafi biyu takalma biyu sai setin jaka guda ɗaya.

Godiya ta fara zuba masa tare da addu'o'in fatan alkhairi. Da mamaki ya dubeta yace "Kayan faɗar kishiya ne fa, kuyi haƙuri..." Katse shi tayi tace "Wallahi mun gode Allah ya ƙara buɗi na alkhairi. Ai kayi ƙoƙari, dududu yaushe kayi wancan auren. Da ka shawarce ni ma da kala biyar kayi mana."

Tsuke bakinshi ya yi, cike da mamakin tsabar murnar aurensa da take yi. Ya rasa dalili, anya ba abinda Hindu take shiryawa. Shi kaɗai yasa dariya tunowa da dalilin da yasa Hindu ta ƙagu ya yi auren nan.

Da mamaki ta dube shi tace "Dariyar fa ta meye? Ni bama wannan ba, ka bani kuɗin ɗinki don kar lokaci ya ƙure." Bai ce mata komai ba ya zaro kuɗi a aljihunsa ya ƙirgar mata dubu ashirin yace "Gashi nan ku yi maleji har kuɗin kayan ciki (under wears). Yauwa zan ƙarawa Hadiza akan wanda na baki saboda ban siyo mata jaka da takalma ba.Tunda tana da su, sai taje ta zaɓo kalar da take so, nasan halinta yanzu sai tace ba irinshi ta ke so ba."
"Eh gara ka bata ta siyo kawai,  Insha Allah anjima zan je na kai ɗunkunanmu. Kamar ka manta da Mama a sayayyar nan, ko don ta gudu gidan Inno ne?" "Haba dai ina sane Insha Allah, zuwa gobe zan siyo mata. Kema ya kamata mu ƙarasa siyayyar haihuwar nan tunda ko yau za ki iya haihuwa. Kar ki haihu ranar biki a ce kishina ne ya tada naƙud..." Ganin yanayinta ya canja ya sa ya ɗau ledar Hadiza ya fita zuwa gidanta.

  Tasha kwalliya ta garari, cikeda karairaya ta tare shi, ta karɓi ledar hannunshi ta ajje sannan ta ɗauko masa ruwa. Sai da ya sha, sannan ya yi mata bayani haɗe da ban baki.

Amma sai ta tashi ta hau bala'i, tausayinta ne ya kamashi, ya miƙe tsaye ya isa wurinta ya rungumeta, fizgewa ta hau yi hawayen baƙin ciki  na zubo mata. Da ƙyar da suɗin goshi ya rarrasheta, amma ta rantse yafi sau shurin masaƙi ba za ta koma India ba, don a ganinta raina ƙoƙarinta ya yi shi yasa zai ƙara aure.

Washegari da wuri ta nufi gidansu, a zaure ta tarar da Babanta har ƙasa ta tsugunna ta gaishe shi ta wuce cikin gidan.

  Ba ita ta baro gidan ba sai yamma liƙis, tana zuwa ta ɗaura girki don itace da aiki.

  Duk abinda tace ta na so, bata Baban Mama ya ke, ba don komai ba sai don ya kwantar mata da hankali saboda cikin da yake jikinta.

  A daren ranar naƙuda ta kama Hindu, gashi ba a gidanta ya ke ba, ganin ba za ta iya daurewa ba yasa ta kira shi a waya, nan da nan kuwa ya zo suka nufi Asibiti, ko awa guda ba su yi ba ta haifi ɗanta namiji, basu dawo ba sai da gari ya waye.

Kwana biyu da yin haihuwar Leema ta zo barka, murna a wurin Hindu kamar ta goya ta, saɓanin Hadiza da ko kallonta ba ta yi ba.

Shirye-shiryen biki sun kankama, don baƙi har sun fara sauka a gidansu Leema. Wasu kuma a dangin nasu duk a Kano suka sauka, sai ana gobe yini za su tafi.

Su Aunty manyan yayye tuni ta ɗau akwati tayi gaba ita da Isah, Mama kawai suka bari sai baƙi a gidan.

Ranar biyan buƙata rai ba abakin komai ya ke ba  inji ƙuda, sosai Leema ta buɗe bakin jaka komai wada-wada a ke yinshi. Dai-dai da kayan ɗaki, gara, abincin da za a ci duk ita ta tanada, sai ƴar gudummawar da ƴan uwa da abokan arziƙi suka babbata. Wanda bai yi ko rabin abinda ta kashe ba. Likitoci da Nurses ɗin zariya ma ba a barsu a baya ba, sun haɗo maƙudan kuɗaɗe sun bata, abin dai sai son barka.

  Kwata-kwata Isah ya kasa zama, duk wasu shirye-shirye da shi a ke yi, shi yasa mata da maza kowa Isah.

  Faɗar irin shagalin da aka yi ɓata baki ne, yau ya kama Alhamis, kuma Juma'a za a ɗaura Aure, gidansu Leema ya ɗinke da jama'a don ƴan Kano ma duk sun iso.

   Sosai Leema ta yi kyau a cikin shigar shaddar da tasa, sai sheƙi ta ke yi sai dai ta ɗanyi rama. Duk ta daɗa bushewa.

  Ƙarfe goma su Baban Mama suka iso, har da waliyyanshi suka zo don su ɗan huta kafin a tafi masallacin Juma'a inda za a ɗauro Auren a can.

   Tun kafin Azahar Leema ta fito suka fara ɗaɗɗaukan hoto da mutane, ƙarasowar Ango tasa wurin ya ruɗe da hayaniya. A ka cigaba da ɗaukan hotuna cike da farin ciki. Saboda wasu kai tsaye za su juya Kano da an ɗaura.

  Ana idar da sallar Juma'a waliyyan Amarya da wakilan Ango suka matsa kusa, Gambo shi ne waliyyin Amarya, mijin Inno kuma wakilin Baban Mama.

Ana shirin ɗaura Aure aka kira Malam a waya, kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya fita ya ɗaga. Hankali a tashe ya dawo cikin Masallaci ya buga tsalle yace "Malam Liman a dakata, wallahi tallahi ba za a yi wannan ɗaurin Auren ba ba tare da an kawo mana takardar gwaji ba, a na meye haka kurum za a lilliɓo kura da fatar akuya a liƙawa ɗa na. Ato Allah mun tuba a kan me?.."

Cikin fusata Gambo ya miƙe amma ko mai ya tuna kuma sai yace "Wannan ai ba wani abun damuwa bane" Russunawa ya yi ya bawa Limamin da zai ɗaura auren haƙuri, sannan ya miƙe ya fita ya samu duk wani mai faɗa a ji a dangi ya sanar da shi.

Ƙaramar magana sai ta nemi komawa babba, kafin kace me mutane sun hau ya maɗiɗi da zancen.

  A ƙufule Dr Zayyad da Dr Lukman suka ja Baban Mama suka sa shi a mota suka fita daga masallacin. Kuka ya ke sosai har da shessheƙa, takaici duk ya ƙume Dr Zayyad cikin tsawa yace "Dallah ka rufe mana baki, ni dama tun farko banga wata marmora ba a auren wannan yarinyar, mugun nacinka yasa ka dage sai ita. To yanzu ga irinta nan ai, ina so na sanar da kai wallahi idan ka kashe kanka da damuwa kai kayi asara zaka bar marayun ƴaƴa biyu, ga wani kuma a ciki da bai zo duniya ba, uwa uba Inno da ƙannenka. Yunus ina so a karan farko ka ɗauko jarumta ka aza a kanka, kar ka manta mahaifinka ya mutu kuma ka cigaba da rayuwarka lafiya ƙalau. To wace ce Leema?"

MUTANENA KAR KU MANTA GOBE DA DADDARE, ZA'A FITAR DA LINK ƊIN ZAƁENMU TUN DAGA DAREN LARABA HAR ALHAMIS DA DADDARE SANNAN A RUFE, INA NEMAN ƘURI'UNKU

ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU

MUM AMNASH🖊️

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now