SO KO WAHALA? PART 61

29 5 4
                                    

[10/15, 5:53 AM] Mum Amnash: *HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

              NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)
*WATTPAD @mumamnas2486*

9/R-Auwal/1443 - 15/10/2021

           5️6️⃣1️⃣

TALLA! TALLA!! TALLA!!!

*Shahararriyar Haziƙar Marubuciyar Duduwa, Gudil da Sameeha wato MAMAN DR ta zo muku da wani sabon littafinta mai suna KISHIN KUSHEWA kishin kushewa littafin kuɗi ne da za ku karanta shi a fashin N100 kacal araha kayan baƙo. Ga mai buƙatar Biyan kuɗi ko ƙarin bayani zai bi ta nan👇👇👇👇*
KUƊIN KARATU: N100
ACCOUNT: Zenith Bank Umma... 2427145748
SHAIDAR BIYA KO KATI TA: 07065014495
  Da fatan zamu riƙe Amana da alƙawari👏

Suna shiga shagon suka zauna a kan dogon bencin da suka tarar da Rabi'u a kai yana ta faman zare idanu.

"Alhamdulillahi Allah ya dawo da ni lafiya daga tafiyar da na yi. Kuma na ga ƙoƙarin da ku ka yi wurin tafiyar da wannan shago, sai dai na fuskanci akwai gagarumar matsala a cikin tafiyar da shi, don haka ina buƙatar duk takardun da ke ɗauke da bayanan kasuwanci, tun daga ranar da na tafi har yau. Idan Allah ya kaimu magriba, a bawa Musa ya kawo mini gida. Na fuskanci aiki yana yi muku yawa, dole na nemi wani kafin Isa ya warware."

Sai da ya numfasa yana ƙare musu kallo sannan yace "Zan wuce, ko da mai ƙorafi."

Ganin ba wanda ya yi magana a cikinsu ya sa ya fita ya bar kasuwar.

Sosai ran Bala ya ɓaci, amma a zahiri wani shegen murmushi ya saki tuno ƙullun da zai ɗaura kuma ya tamke. Su Musa kuwa miƙewa suka yi suka cigaba da sabgar gabansu.

Tamkar wanda ya yi sartse aka zare masa ƙaya haka Isa ya ji lokacin da ya tashi daga barci. Kansa sakayau, sai dai rashin ƙarfin da yake ji kamar iska za ta bushe shi ya faɗi. A hankali ya yunƙura ya zauna, da sauri Yaya Kabiru ya ƙaraso ya kama shi yace "Za ka shiga banɗaki ne?"
"Eh Yaya"
Kafaɗarshi ya kama ya shigar da shi har banɗakin sannan ya fito ya rufe masa ƙofar don ya ga jikin da sauƙi.

Sai da ya ɗauro alwala sannan ya fito, da kanshi ya shimfiɗa darduma ya tayar da sallah. Sosai Yaya Kabiru yake mamaki, shi kanshi ya fara shakku a kan ciwon ƙanin na shi. Amma tsabar boko tasa ya basar kawai, yana ganin wannan duk abubuwan gargajiya ne da suka riga suka shuɗe.

Yana idarwa Aunty ta shigo, tare da Malam (Baban Salaha) a bayanta. Fuskar Isa ɗauke da murmushi yace "Malam sannu da zuwa."
"Yauwa, ya jikin na ka?"
"Da sauƙi sosai Alhamdulillah"
"Masha Allah, haka a ke so."

Ƴar ledar da take hannunshi ya buɗa ya ciro roba ƙarama ya miƙawa Aunty yace "Addu'a ce ya dinga shan kaɗan yana shafawa a dukka jikinshi, in da hannunshi ba zai kai ba a shafa masa. Idan kuma da ruwan zam-zam za a iya ƙarawa a kai."

"Madallah an gode, Allah ya saka da alkhairi Malam. Tun da ya ji sauƙi yanzu zan je gida na ɗauko ruwan zamzam ina da shi sai a ƙara. Allah ya saka da alkhairi, mun gode."

"Babu komai, Isa ai ƙanina ne."

Kan Yaya Kabiru a ƙasa yace "An gode." Murmushi Malam ya yi yace "Hala kai ne Yaya Kabiru?"
"Eh, ni ne."

Kan Isa a ƙasa cike da kunyar kar Yaya Kabiru ya kwafsa yace "Malam ina Hajiya Kaka?"
Aunty ce ta yi zaraf tace "Ai ɗazun nan suka tafi, sun daɗe a nan lokacin barci ka ke yi."

Shigowar Leema ɗakin ne ya katse musu zancen, cike da farin ciki ta ƙaraso ciki duk da jikinta ba ƙarfi sosai. Sai da ta gaida Malam da Yaya Kabiru sannan ta nufi Isa, fuskarta ɗauke da murmushi.

SO KO WAHALAOnde histórias criam vida. Descubra agora