SO KO WAHALA? PART 1

238 18 2
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*SO KO WAHALA ?*

               *NA*

*MARYAM MUHAMMAD SANI (Mum Amnash)*
WATTPAD mumamnas2486

             ▶️1️⃣

5/Shauwal/1443 - 17/5/2021

*Assalamu Alaikum a madadin ɗaukacin Admins da member's na HAƊAKA WRITER'S muna miƙa saƙon barka da sallah ga ɗaukacin musulmim duniya. Allah ya karɓi ibadunmu ,Allah ya maimaita mana,Allah ya gafartawa magabatanmu ya musu rahama da mu da su baki ɗaya*🤝🤝🤝

     "Ka cuce ni ka yaudareni  ba ka da abinda za ka cemin Azzalumi maha'inci , ka je na barka da... maha..liccinmu." Jagwaɓ ta zube a ƙasan tayal ɗin da ke ɗakin, a lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka.

Gaba ɗaya ƴan ɗakin hankalinsu ya dawo kanta, ɗaya daga cikin ƴan rukuninsu ce ta ƙaraso ta ɗagata ta zaunar da ita a gefen gadon da ya fi kusa da su . Ta kama hannunta tace "Sis Leema don Allah ba don ni ba ki kwantar da hankalinki, komai ya yi zafi maganinsa Allah. Karki manta muna ƙasar da tafi kowacce ƙasa  tsarki da aminci, me zai dameki ? Ko ma mene ne nasan bazai rasa nasaba da Baban Mama ba . Abinda ya fi dacewa da ke ,ki miƙe ki shiga banɗaki ki ɗauro alwala mu wuce Harami, insha Allah ko mene ne zai daidaita ."

Ba tace komai ba ta zare hannunta daga na sista Zahra, ta miƙe tsaye tana share hawayen da ke zuba a kan fiskarta .Alwala ta ɗauro kai tsaye suka nufi Masallacin Harami .

Sai da suka kammala ɗawafi sannan suka koma gefe ɗaya na masallacin. Nafila su ka yi raka'a biyu   ,sannan Haleema ta ƙara miƙewa kamar jela tabi Zahra tabi bayanta, da ƙyar ta hangota tana kutsawa ta cikin mutane har ta isa dai dai inda ta ke so.

Hannunta ta ɗaga sama tana kuka tana addu'a tun Zahra na jira har ta gaji , don ko hangota ba ta yi,duk da cinkoson da sauƙi,  ba kamar da rana ko ƙarshen dare ba don dare ya tsala sosai. Ƙofar da su ka saba haɗuwa ta nufa ta zauna ta na jiranta ,har sai da gyangyaɗi ya fara kamata sannan ta fito su ka tafi.

Kamar a ɗazu , babu wanda ya ke magana har su ka isa masaukinsu. Magani Zuhra ta miƙawa Leema ta karɓa ta haɗiya,sannan ta kwanta jikinta zafi rau da zazzaɓi, ba jimawa barci mai nauyi ya ɗauketa . Tagumi Zahra ta rafka tana kallon jarumar ƙawarta da soyayyaya ta mayar lusara kuma wawiya , gaba ɗaya ta rasa wace irin soyayya take wa Baban Mama, SO KO WAHALA?...... Ƙarar wayar Leema ne ya katse tunaninta. Miƙewa ta yi ta nufi wayar da ke yashe a gefen gadon ,  Aunty Salama da fitowarta daga banɗaki kenan tace "Mun ga banu , wallahi tun da ku ka fita ake kiran wayarnan da mabanbantan lambobi, ƙarshe sai da na ɗaga nace kun fita amman bai bar kira ba ƙarshe na gaji na ajje mata wayar anan . Ko ba'a faɗa ba nasan Baban Mama ne, wannan mutum da shegen nacin tsiya ya ke."  

   Murmushi kawai Zahra ta yi jin faɗan da Aunty Salma ta ke, kafin ta ɗaga wayar ta katse , ta buɗe baki za ta yi magana kiran ya ƙara shigowa. Tsaki Aunty Salma ta ja tace kin ji ba SO KO WAHALA? Allah ya sauwaƙe ta tada sallarta.

Ɗaga wayar Zahra ta yi da sallama "Assalamu Alaikum" Bakin shi har karkarwa ya ke yace "Waalaikumussalam don Allah ina Halima ta ke? Ki bata wayar nan ba don ni  ba don Allah, ta saurareni  ina da magana mai muhimmanci da zan faɗa mata ki taimake ni don Allah..." Katse shi Zahra ta yi don taga alamar bazai bata damar magana ba tace "Baban Mama ka tsaya ka saurareni ka ji , Haleemar taka tana kwance tasha magani ta yi barci. Sannan karka manta , mu fa munzo ƙasa mai tsarki ne da niyyar Aikin Hajji haɗe da aikin kula da lafiyar al'ummar jaharmu. Don Allah ka tsahirta mana da kiran waya kabarmu mu yi aikinmu da ibadarmu lafiya . Sannan don Allah ko kun yi waya nan gaba kar ka ƙara faɗa mata abinda zai ɗaga mata hankali a ƙasar da ba tata ba , ko mai ya ke akwai ka bari idan ta koma ƙasarta gaban iyayenta sai ku ƙarasa na gode." Ƙitt ta kashe wayar gaba ɗaya ta sanyata a caji , sannan ta ɗora alwala ta tada sallar  ta.

    Baban Mama kuwa wayar ya bi da kallo ,lokaci guda ya fashe da kuka ya na sambatu "Kinsan ina sonki Haleema , ki fahimce ni don Allah, ki bari mana idan na auri Hadizar kema sai na aureki daga baya , ni meye laifina?"
"Kai ko ka ke da Laifi Baban Mama ,don na fiskanci ba ka cikin haiyacinka , a yanda na ji kana furtawa a yanzu Kishiyoyi har biyu ka ke son yi min ko? Tom ba laifi ka je ka yi , ka ƙara azama da dagiya . Ni na yi nan ,komawa zan na ƙara matsewa don naga Asibar da saura." Hindatu (Matar Baban Mama) ta faɗa tana komawa ɗakin kwananta.

Baban Mama kam zama ya yi ya cigaba da kukanshi haiƙan.......

ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU

MUM AMNASH🖊️

SO KO WAHALADonde viven las historias. Descúbrelo ahora