SO KO WAHALA? PART 12

41 5 4
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

           NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486
BLOGSPOT@mumamnash.blogspot.com

27/Shauwal/1442 - 7/6/2021

             1️⃣2️⃣

    "Ƙwarai na san ku na fita sosai , amma ban taɓa faɗawa kowa ba. Ni Isah, ba abinda zan ce mi ki sai ki ji tsoron Allah. Rayuwarki ce ,amma ya kamata ki bita da takatsantsan. Na san duk a ganinki zarginki mu ke ko ? Ba zargi ba ne , so mu ke ki kaucewa abinda zai sa a zarge ki . Ni saurayi ne , kuma duk wata shaiɗana da ake yi ina da labarinta. A cikin abokanmu akwai ƴan shan minti , ba aure za su yi ba amma za su gurɓata tarbiyyar yarinya da ka musu magana su ce ai ba wani abu ba ne. Bari na futo miki a mutum sak ! Na fi zarginki da soyayyar shan minti , idan kuma ba ita ki ke yi ba, to ki daina zance a mota. Maganin kar a yi kar a fara, da muguwar rawa gwamma ƙin tashi."

Bai jira amsarta ba ya shige ɗaki , ya barta ta na rusa Kuka, sai da ta ga ba sarki sai Allah, babu mai rarrashinta sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Mama.

   Washegari kuwa da wuri ta tashi , ta yi wanka   ta haɗa kayanta ko tashi daga barci ba su yi ba ta ɗau jakarta ta nufi tasha.  Kai tsaye ta hau motar Kaduna ta wuce gida , da ta isa ma ba ta shiga ciki ba ,ƙaninta ta kira ya kawo mata muƙulli ta buɗe ɗakinta ta kwanta .

   Sai bayan tafiyarta da kusan Awa ɗaya sannan Aunty ta shiga cikin gida, duk da ba ta ganta ba , ba ta tambaya ba ta gaida Mama ta juya .

Har ta kai ƙofa ta Mama ta ce "Halima ta na ɗakin ki ne ?" Da mamaki Aunty ta juyo ta ce "A ah ba ta nan , taɓɗijam! kenan fita ta yi to wallahi ta janyowa kanta , yanzun nan zan kira Uwarta ta ji iskancin da ta ke mana . Saboda yarinya na da kuɗi sun barta za ta lalace a banza , to ba a gidannan ba ato! "

   Mama ta ce "Kibari tukunna zuwa anjima, idan ba ta dawo ba sai a kira a tambaya ko ta koma gida. "

"Mama bari na kira yanzun , kinsan yanayin tsaron ƙasar ta mu ,amma da ya ke Ƴar kanta ce  ta nufi tasha tun Asiba . Saboda kawai na mata faɗa , zan faɗawa Uwarta kar ta ƙara zuwa gidannan . Idan kuma ta cigaba da zuwa to ni dai, ba ruwana da tarbiyyar ƴar ta." Fuuu ta fice ta nufi sashinta.

   Ta na shiga ta ɗau waya ta kira
Mamar su Leema, ba ɓata lokaci ta kora mata jawabin duk abinda ya ke faruwa ,sannan ta kashe wayarta ta yi ta mitarta ita kaɗai.

   Jujjuya wayar kawai Mama ta ke , daga baya ta miƙe ta nufi ɗakin Leema , a kare ta tarar da ƙofar, wannan ya tabbatar ma ta da dawowarta. A fusace ta tura ƙofar ,amma ba ta ga Leema ba , motsin da ta ji a banɗaki ya tabbatar mata da ta na ciki. Doguwar kujerar da ke ɗakin ta nufa ta zauna  , abin duniya duk ya isheta. Babban abin takaicin da ma al'ummar gidan wasu sun tsani Leema, amma tsoron Babansu ya sa ko da wasa ba sa nunawa , sai dai su yi a bayan fage. Yanzu idan Leema ta janyo musu masifa ai sun kaɗe har buzunsu. "Astagfirullah " ta furta a fili don har a zuciyarta ba ta yarda Leema za ta iya aikata wani mummunan abu ba . Ta dai fi yarda da masifar faɗa irin na Auntyn Kano... Fitowar Leema ce ya katse mata zancen zucin da ta ke yi.

    A gefen Mama ta zauna ta ce Mama ina kwana? Ban samu na shigo ciki ba raina ne a ɓace wallahi ." Muskutawa Mama ta yi ta ce "Ai Antin ta ku ta kirani , ta yi mini bayanin duk abinda ke faruwa a can Kanon. Haleema idan ba dama ki rabu da wannan mutumin Baban Mama , gari da yawa ai maye ba ya ci kansa ba. Ina dalilili da bakinki ki ka ce min rabuwa za ki yi da shi , saboda ya ci amanarki ya zaɓi wata ba ke ba. Amma taurin kai da tsabar ƙulafuci irin na yaran yau ya sa ki ka ƙara lallaɓawa ki ka koma wurin shi. Ina son ki sani , muddin ki ka jawo mana wani abin kunya to sai dai ni da ke mu bar gidannan kin fi kowa sanin halin Mahaifinki."

  Duk waɗannan maganganun na Mama ko ɗar ba su sa Leema ba ,don wanda ya yi nisa ba ya jin kira. Gyara zama Leema ta yi ta ce "Mama nasan a duk duniya kinfi kowa sanin halina, Mama sau nawa lokacin ina makaranta na ke kwana a wurin ƙawayena a hostel? Kusan kullum muddin lafiya ta ƙalau sai na fita aiki ko kasuwancina. Tun mutane na surutu har su ka haƙura ,yau aikin da na ke yi Mama wa ye ba ya mora? Mama ki toshe kunnenki kawai ki rabu da Antin Kano da na koma za mu shirya"

Ajiyar zuciya Mama ta sauke ta ce "Amma me ya sa ki ke zance a mota Haleema ,ki na da iliminki na addini dai-dai gwargwado kar fa ki faɗa tarkon Shaiɗan." Ƙara saukar da murya Leema ta yi ta ce "Ba fa koyaushe mu ke zancen a mota ba , kuma abinda ya sa na ke sakin jiki da shi saboda ya ƙaunace ni fiye da kowa ,in na ce kowa ina nufin kowa Mama har matarshi , tunda ita ma ba sonshi ta ke ba . Ba yanda za'ayi na yarda na zubar mu ku da ƙima a titi , nasan me na ke yi Mama yanzu fa na haura shekara talatin , ki kwantar da hankalinki insha Allahu na kusa aure kema ki huta." Dariya Mama ta yi "Ta ce Ja'ira ko kunya ta ba kya ji? Haleema ya batun kuɗinnan da mu ka yi da ke?" "Ai Mama da yaran can sun tashi ki turo ɗaya ya je ya ciro miki a banki." Leema ta ƙare ta na dariya ƙasa-ƙasa don tasan da ta bawa Mama wannan kuɗin magana ta wuce, sai wani lokacin kuma. Miƙewa Mama ta yi ta ce to , Allah ya yi albarka ya tsareku a duk inda ku ke , bari na ƙarasa ciki na dama koko . Ko za ki sha a zubo miki in an dama?" Sai da ta yamutsa baki sannan ta ce "An jima na nemi abinda zan ci kawai ". Ta haye saman doguwar kujera ta miƙe ko kaya ba ta sa ba, sai zanen wankan da ke jikinta.  Don banda Mahaifiyarta, babu wanda ya isa ya shigo mata ɗaki kai tsaye .

****************

   Dambu taliya, duk yanda Baban Mama ya so shawo kan Hindu abin ya ƙi yiwuwa . Babban abin takaicin duk sauran gaibu ne , Hindun dai ita ce tabbas ɗin , da ma ai sandar da ta ke hannunka da ita ka ke kai bugu.
Ajiyar zuciya ya sauke a fili ya ce "Mai son ɗan tsuntsu ,shi  ke binshi da jifa ya zanyi."

Uwar ɗakinta ya shiga , a ƙasa ya tarar da su ta na nunawa Mama haruffan Larabci . Ya na shigowa ta tattara kayan karatun ta zuba mata a jaka ,sannan ta sa mata takalmanta da hijabi . Ko kallonshi ba ta yi ba , ta zura na ta hijabin . Ta na ƙoƙarin bin bayan Mama ya ɗan sha gabanta ya ce "Kaina bisa wuyana , na yarda na yi laifi ki yi haƙuri." Murmushin takaici ta yi ta ce "Wannan tsohuwar magana ce, ta riga ta wuce, ka matsamin hanya na kai yarinya makaranta." Da sauri ya koma ɗaki ya ɗauko mukullin motarshi ya fita ƙofar gidan ya tsaya, ham ya danna mata ɗiiiittt, kamar za ta wuce ganin da Mama a kusa ya sa su ka shiga motar, ya ja su ka tafi.

   Islamiyyar a cikin unguwar ta ke ,ko tafiyar minti biyar ba su yi ba su ka isa makarantar. Sai da ya shigar da Mama har ciki sannan ya fito, ya shiga motar "Assalamu Alaiki gimbiyar mata" "Wa'alaikumussalam" ta amsa masa dariya na neman suɓuce mata ,amma sai ta dake...

  Ƙarar wayarsa ce ta katse su , "Hadiza" ya furta a fili,  a sace ya dubi  Hindu ,ga mamakinsa hankalinta na kan wayarta kawai .

Ɗagawa ya yi ya yi shiru , cikin isa da gadara Hadiza ta ce "Yunus na ga motarka a waje ,yau ba ka fita ba kenan?" Kamar mai ciwon baki ya ce "uhm" duk da ta yi mamakin yanayin amsar da ya ba ta ,amma sai ta dake ta ce "Ina son ganinka yanzu" Wata bazawar dariya ya yi ya ce "Kai tsaye haka , na ɗauka cewa za ki yi  kina nemana idan ina da lokaci . Manta da wannanma yau ba inda zanje , yanzu haka ina tare da sarautar mata , kinga ai sawun giwa ya ta ke na raƙumi . Amman kar ki sami damuwa ,insha Allah cikin week ɗinnan idan na sami lokaci zan leƙoki."

Taɓɗijam tashin hankali da ba'a sa masa rana , sakatoto ta yi da baki ,waya kange a kunne . Ta buɗe baki za ta yi magana ta ji ya ɗaga wani kiran, wata ƙatuwar ashar mai ƴaƴa ta ja ,ta yi jifa da wayar.

  Shi ya ma manta shaf sunyi alƙawari da Leema za su fita sai yanzu da ta kira, shi ya sa kafin ya katse kiran Hadiza ya ɗaga kiran Leema . Itama a fusace ta yi masa sallama ya amsa, kafin ta ce komai ya ce "Ki yi haƙuri Leema bazan sami zuwa wurinki ba gaskiya,ina tare da Hind, ko na ba ki Sarautar matan ku gaisa?" ƙitt ta katse kiran ta rushe da matsanancin Kuka . A fili ta fara sambatu "Na haƙura da kai Yunus ko kaine autan Maza, Allah ya isa bazan taɓa yafe maka ba." Ta zauna dafa'an ta na raira kukanta. Ita da duk a tunaninta ba wani son Hindu ya ke ba, sai gashi ya tsinkata a gabanta.

Allah ya gafartawa iyayenmu

*MUM AMNASH/ƳAR FARAGAI👌🖊️*

SO KO WAHALAOnde histórias criam vida. Descubra agora