SO KO WAHALA? PAGE 37

36 2 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                  NA

*MARYAM MUHAMMAD SANI (MUM AMNASH)*
*WATTPAD @mumamnas2486*

            3️⃣7️⃣

Da sauri ta isa kusa da Isa ta miƙar da shi tsaye, amma sai ya koma ya zauna daɓas. Ranta a ɓace tace "Wai me ya ke faruwa ne? Na ji zancen nan a baibai, gara a fayyace min abin da yake faruwa don..."

"Dama nasan ko kowa bai bamu matsala ba ke sai kin bayar, ina son ki sani uwar da ta haifi Isah ita tasa na ɗaurawa ɗanta aure da Halima ba wai gaban kai na na yi ba. Ki faɗi alkhairi ko kiyi shiru, maimaita zance bashi da wani amfani." Yana ƙarewa ya fice abinshi ba tare da ya ƙara kallon kowa ba.

Cike da tsananin mamaki ta bi bayan Gambo da kallo, kai ta gyaɗa da sauri ta bishi tana mita.

Tiris ta yi ganinshi tsaye tare da Baban Mama, da mamaki take bin Yunus da kallo, a yini ɗaya ya rame, sannan ya sanya baƙin gilashi a maimakon farin da ya saba sawa, a wurin Dr Zayyad ma ya karɓa don ya ɓoye asirin halin ƙunci da tashin hankalin da ya ke ciki. Cikin sanyin murya yace "Aunty sannu da dawowa, Aunty kin ji yanda Allah ya yi damu ko Aunty? Haƙiƙa na ƙara saduda da wannan rayuwar, duk soyayyar da muka yi ta tashi a banza, ta tashi a tutar babu. Aunty..." 

Jikin Aunty a sanyaye tace "Yunus shigo daga ciki, magana ba zata yi wu a waje ba."

Bin bayanta ya yi yana goge hawayen da ya ke zuba a idanunshi, wata irin faɗuwar gaba da tsinkewar zuciya ya ke ji amma sai ya daure ya ci gaba da maimaita Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. A take ya ji faɗuwar gaban ta yi sauƙi sai mutuwar jiki.

Sanin gidan cike ya ke da jama'a yasa ta buɗe musu ɗakin Leema, suka shiga ciki.

  Kansa a ƙasa ya shiga, a gefen kujera ya zauna yana murza zoben azurfar da ya ke hannunshi. Cike da tausayawa Aunty tace "Yunus da gaske ka haƙura ka sadaukar da soyayyarka? Me yasa baka kirani kafin ka yanke hukunci ba? Baka tsoron halin bala'in da za ku shiga? Yunus baka kyauta min ba wallahi. Abinda na ke son tambayarka shin da saninka aka mayar da auren Halima ga Isah? Wallahi bazan ɓoye maka ba banyi farin ciki da hakan ba, ai kowacce ƙwarya da abokin burminta, kuma sai hali ya zo ɗaya ake abota. Kai da Leema kun fi dacewa don ɗabi'unku sun dace da riƙaƙƙen ra'ayinku na wayewa da tsantsar boko."

Cikin sanyin muryar da ta sameshi a yau, cike da raunin zuciya yace "Aunty ki yi haƙuri, duk abinda ya faru babu wani mai laifi a  cikinmu. Tunda al'amarin nan ya faru na ke furta Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Don ita Allah maɗaukakin sarki ya umarcemu da faɗa a duk lokacin da masifa ta faɗa mana. Rashin Leema masifa ce a gareni Aunty, Addu'a da koyi da abinda Allah da ma'aiki suka umarta yasa na samu salama, a cikin zuciya da ƙwaƙwalwata har da gangar jiki na. Da badon addu'a ba da tuni ina kwance a asibiti, ina son Leema amma haƙuri da juriya su suka fi cancanta na azawa zuciyata. Idan har na jure wannan masifar ta ɗan lokaci xe zata wuce, ko mu manta ko kada mu manta ƙaddara ta riga fata. Aunty nasan kina da ilimi da fahimta a ganinki auren Leema shi yafi ko barinsa? Mene ne makomar ƴaƴan da za mu haifa idan suka zamto da Amosanin jini (Sicle cell). Maganin kar ayi kar a fara, dukkan tsanani yana tare da sauƙi. Aunty nasan Isa zai kula da Leema sama da yanda zan kula da ita, zai zame mata bangon jinginarta a kan dukkan lamuranta, ina musu fatan alkhairi da fatan dacewa duniya da lahira. Ki sanar da ita ina musu fatan alkhairi ita da Mijinta, sannan ƙofa ta a buɗe ta ke idan tana neman taimakona a kan komai na rayuwarta." Ya sanya hannunshi a aljihu ya zaro hankici ya fara share fuskarshi da hawaye ke malala daga idanunshi. Wani irin ɗaci ya ke ji a maƙogaranshi, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" ya ke maimaitawa a fili. Hankalinsa ya mayar kan wayarshi da take faman haske tun ɗazu, alamun shigowar kira.

SO KO WAHALANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ