SO KO WAHALA? PART 56

31 6 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                 NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)
*WATTPAD: @mumamnas2486*

5/ R-Auwal/1443 - 3/10/2021

              5️⃣6️⃣

  A can ƙuryar shagon suka zauna a kan kujerun roba. Alhaji ya dubi Isa yace "Malam Isa dama na tambayi Musa wanda ya gyara mini na'ura mai ƙwaƙwalwata satin da ya wuce, sai yace mini kai ne, to jin haka sai na ga abun ya zo gidan sauƙi. A taƙaice dai na yaba da tunaninka da hankalinka, don na binciki komai game da kai."

Cike da mamaki Isa yake duban Alhaji, jin har da bincike a kanshi kamar ya taɓa kayan wani.

"Isa idan ba zan takura maka ina son ka dawo shagon nan da zama. Abubuwa marasa daɗi suna faruwa na almundaha da ha'inci a wannan shagon. A da kuɗaɗen da suke ɓata basu da yawa amma a jiya, an samu ɓatan wayoyi masu matuƙar tsada, wanda ba na raba ɗaya biyu ɗauka a ka yi."

Kan Isa a ƙasa yace "Alhaji idan da zai yiwu da na'urar naɗar hotuna masu motsi (cctv camera) ka sa a asirce. Da ita ne kawai za ka ga abinda ke gudana a shagon ba tare da matsalar komai ba."

"Wannan ma dabara ce mai kyau, sai dai ko da na saka ta to akwai sauran rina a kaba. Don tilas ne na nemi mai kula da ita, da kuma wanda zai dinga shigar mini da duk bayanan da suka shafi cinikayyar da a ke yi a wannan shagon a wata na'ura daban. Isa ba harkokin waya kaɗai nake yi ba, ina wasu harkokin a Kasuwar kwari da sabon gari. Shi ya sa za ka ga ba kullum na ke ratsowa nan ba."

Sai da ya numfasa yana nazartar Isa sannan yace "Malam Isa ba zan takura maka ba, duk shawarar da ka yanke insha Allahu babu matsala."

Kan Isa a ƙasa yace "Alhaji ba naƙi ba ne, amma na shigo wannan Kasuwar ne don na dogara da kaina. Na yi karatu har digiri na Biyu, na yi difloma a fannin na'ura mai ƙwaƙwalwa, amma zan sanar da Mahaifiyata da Auntyna, duk abinda suka zartar zan sanar da kai."

Murmushi Alhaji ya yi yace "Na gode sosai Malam Isa. Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
"Ameen" ya amsa a taƙaice, sannan ya fita daga shagon

  A tsakiyar teburansu ya tarar da Jabir fuskarshi a sake yace "Sannu da jira Malam Jabiru." Ya zauna a gefen bencin.
"Yauwa, amma dai ka daure ka koran bayani, na gaji da jira."
"Ka cika wutar ciki, kome ka ke so ka ji, za ka ji. Amma sai ka jirani na ɗanyi waya." Ya ƙare yana dannawa Leema kira.
"Assalamu Alaikum" ta yi sallama cikin rausayar da murya.
"Wa'alaikumussalam Zaujaty, ya ki ke?"
"Lafiya ƙalau."
"Ki yi haƙuri tun ɗazu na so na kiraki, amma abubuwa sun mini yawa."
"Babu komai, nima nasan kana cikin hidima ai. "
"Bari na kira Malam sai ya turo miki Salaha ta yi miki cefane."
"Shi kenan na gode." Kafin ya ƙara furta wani abu ta katse kiran. Wayar kawai yake jujjuyawa yana shafa sumar kanshi da bata da yawa. Fuskarshi ɗauke da murmushi... "Kai Romiyo uban soyayya ba ka ji ba"  da murmushi a fuskar Isa yace "Ban ji me ba"
"Bana son latsi, don Allah ka ban labari."
"Gaskiya Jabir ka cika matsala, bari na faɗa maka don yanda ka baza kunnuwan nan idan ban baka sanar da kai  ba babu zaman lafiya. Kamar yanda na faɗa maka ina da Mata bamu daɗe da aure ba. Don na ga kamar kana zargina."

Dariya Jabir ya yi yace "Ai gwara da ka warware mini, don na yi mamaki nutsattsen mutum kamarka a ce yana bunburutu ai tsari ya lalace."

Dariya Isa ya yi yace "Saura ku, Allah ya fitar da jaki daga duma." Taune leɓenshi na ƙasa Jabir ya yi yace "Ai abin rabo ne, muma nan kusa jirginmu zai ɗaga Insha Allah."

Kai tsaye ta nufi ƙofar jin kamar bugawa a ke yi. Salaha ce a tsaye tana wasa da bakin hijabin hannunta. Matsa mata hanya ta yi tace "Shigo mana, gwara da ki ka zo da wuri don tuwo nake son yi."

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now