SO KO WAHALA? PAGE 32

38 2 0
                                    

[8/4, 8:32 PM] Mum Amnash: *HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA😭❤️*
(FREE BOOK)
NA
*MARYAM MUHAMMAD SANI (MUM AMNASH)*
*WATTPAD@mumamnas2486*

23/12/1442 - 3/8/2021

3️⃣2️⃣

*MAI BUƘATAR Littafina na ƳAR HIZBA zai biya 200normal, 300vip, 400special ta wannan account no. 2083460164 Abubakar Abdullahi Zenith bank sannan a turo shaidar biya ta wannan number 07038826617 ko a turo katin MTN ta wannan number*

*SHAHARARRIYAR MARUBUCIYARKU AMEERA ADAM ZATA KAWO MUKU WANI SABON LITTAFIN MAI SUNA ANYA BAIWACE???DOMIN BIYAN KUƊIN KARATUN WANNAN LITTAFI normal group 200, vip 400 Za'a biya ta wannan Account ɗin FISRTBANK 3090957579 AISHA ADAM, SANNAN A TURO DA SHAIDAR BIYA TA 07062062624 Don Allah inkinsan zaki fitar mana da littafi mun yafe cinikinki*

Kwana suka yi tana zazzaɓi da amai, sosai hankalin Baban Mama ya tashi. Gari na wayewa ya ɗebeta suka yi Asibiti, Gwajin farko ya nuna tana da shigar ciki na sati huɗu, cike da farin ciki suka dawo gida.

Ruwa mai ɗumi ya dafa mata tayi wanka, sannan ta karya, dama bata fiye tsiri ba idan tana laulayi.

Da kanta ta bashi shawarar ya tafi da Hadiza don tsakani da Allah ba za ta iya binshi zuwa Indiya ba, don duk da tana cin abinci tana wahala sosai.

Ko da Hadiza ta ji abun da ya ke wakana, ba ƙaramin daɗi ne ya ƙumeta ba. Amma sai ta maze, tana jiran ya sanar da ita da kanshi da ita zai tafi.

Tun safe da ya shiga bai ƙara komawa ba sai gab da magriba, jiki na rawa ta haɗa masa ruwan wanka. Tana ta ƙiƙƙifta ido da karairaya.

Shi abin ma dariya ya fara bashi, amma sai ya ƙyaleta sai da ya gama komai, ya fice daga gidan sai da ya yi sallar Isha'i sannan ya dawo.

Da murmushi a fuskarshi yace "To ƴar anace, sai ki fara shiri tafiya ta tabbata da ke ƙarshen wannan sati." Cikin farin ciki tace "Na gode, amma kai a ganinka na damu da tafiyar ne har kake ce mini ƴar anace?"
Fuskarshi a sake yace "Ina tunanin ya kamata na je na yiwa ƙanwarki sallama kafin mu tafi, ko ya kika gani?" dariya tayi tace "Au wai sai ka nemi izinina? Ka daɗe baka je ba!" Ta miƙe a fusace ta shige ɗaki.

Yana gama cin abincin ya ɗau kujera ya fita ƙofar gidan ya zauna, jujjuya wayar hannunshi kawai ya ke yi, kamar ya kirata kamar ya ƙyaleta kawai sai ya danna kira.

A kwance take a kan kujera ta runtse idanuwanta kamar mai barci, jin sallamar Gambo ya sa ta miƙe da sauri ta faɗa banɗakin da ya ke cikin ɗakin. Tana jin sababin da Gambo ya kewa Mamanta a kanta, Inna (kishiyar Mamansu Leema)da ta fusata sai tace "Kai Gambo ka ishemu ka tafi ka dubo Haliman ka ɗau duk hukuncin da ya dace a kanta, wannan faɗan Gwaggo a kofa ka ke yi, tunda wanda kake yi a kanta bata kusa." Ta ja hannun Maman Leema suka shige ɗakunansu.

Wani irin takaici ne ya ƙume Gambo, kai tsaye ya wuce ɗakin Leema, da ƙarfi ya hau bugu, amman shiru ba a yi magana ba, buɗewa ɗakin ya yi ba kowa sai wayarta da ke faman ƙara alamun shigowar kira.

Wayar ya ɗauka, Baban Mama ne ya ke ta kira, ɗagawa Gambo ya yi sai ya ji ance "Haba Baby Leema, kiyi haƙuri Insha Allahu zan turo. Sai dai da matsala wallahi a ƙarshen satinnan zan tafi Indiya na samu aiki. Ba ki ce komai ba ko fushi ki ke?"

"Ba Haleema bace nine Gambo Ubanta, Yaro daga yau kar ka sake kiran Haleema tunda ba aurenta za ka yi ba. Haƙiƙa da zarar ka tafi Indiya ko wata biyu ba za'a cika ba zan ɗaura mata aure. Allah yasa ka tafi cikin nasara, kar ka ƙara kiranta!"

Duk yanda Leema ta so kar Gambo ya ji kukanta, bai yiwu ba don bata san lokacin da ta kurma ihu ba, jin yana ƙoƙarin gurgunta mata rayuwa.

Dariya Gambo ya yi yace "Hatsabibiya ai nasan kina cikin ɗakin nan, mai shegen taurin kai mu zuba ni da ke." Ya fice yana ta mita...

SO KO WAHALATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang