SO KO WAHALA? PART 64

18 1 0
                                    

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EiQ3qtht0QSLRElOcqt3CP

[10/23, 10:39 PM] Mum Amnash: *HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                *NA*

*MARYAM M SANI (Mum Amnash)*
*WATTPAD:@mumamnas2486*

17/R-Auwal/1443 - 23/10/2021

*ANYA BAIWA CE Sabon ƙayataccen littafin sarauta mai cike da turka turka na shahararriyar marubuciya AMEERA ADAM #200 VIP400. ACCOUNT: FIRST BANK,AISHA ADAM 3090957579 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA 07062062624*

               6️⃣4️⃣

Da sauri ya sassauta riƙon da ya yi mata, hannu yasa yana ƙoƙarin ɗage doguwar rigar da ke jikinta. Ƙarar ƙwanƙwasa ƙofar da a ka yi ne yasa, ya saketa, a hankali ya ja jikinshi ya koma bakin kujerar ya zauna. Idanunshi a kanta, ya kasa gaskata abinda ya ji. A take idonshi ya cika da ƙwalla, kansa ya sunkuyar ƙasa cikeda tsabar ƙaunarta da tausayinta.

Ajiye tiren da a ka ɗoro masa filasan abinci ta yi, fuskar ta a sake tace "Ga abinci na zuba maka?"
"A'a kar ki zuba a ƙoshe nake, amma cike na ke da matsananciyar yunwar..."
"Ya isa haka, a gidan surukai fa ka ke."

Fuskarshi ɗauke da murmushi yace "Na manta shaf, kin san idan ina tare da ke, ni kurma ne, kuma makaho. Bana ji bana ganin komai sai ke Matata abar ƙaunata.

Wata irin kunya ce ta kamata, tafukan hannunta ta sa ta rufe fuskarta. A hankali ya miƙe, ya kamota ya zaunar da ita a kusa da shi, hannunshi ya ɗora a kan cikinta yace "Ki tabbatar mini da gaske ne ba mafarkin da na saba yi ba."

"Cikin hikima ta ubangiji Allah buwayi gagara misali ya azurtaka da samun rabo, sai dai kash!  Ya bayyana a lokacin da baka hayyacinka. Na sha sanar da kai a lokuta da dama, amma daga baya sai na gane baka cikin haiyacinka a tsahon watannin nan. An cutar da ni, an nisanta ni da mijina..."

Hannunshi yasa a gadon bayanta ya fara shafawa a hankali alamar rarrashi.  A hankali ta zare jikinta daga na shi, fuskarta a ɗan tsuke tace "Na fahimci kai babu abinda yake damunka, ni fa kalli ka ga yanda na koma" ta ƙare da shagwaɓe fuska. Murmushi ya yi yace "Na yi alƙawarin ninninka kulawar da zan baki, fatana ki yarda ki bini yau, da kin san me?"
"A'a"
"Ko gida ba za mu biya ba, sai dai su Aunty su ji mun koma kawai. Sa biyo mu da kayanmu. Wai anya ki na cin abinci kuwa?" Ya ƙare yana tattaɓa ƙashin wuyanta da ya ƙara fitowa.
"Ba sosai ba dai, to da wanne zan ji? Kewarka ko damun Bebinka, ko kuwa tsabar hayaniyar gidannan?"

"Ai ko dai ta ƙare daga yau, don ƙafata ƙafarki, idan ba haka ba tofa sai dai su Balaraba(ƙannenta) su nemi gurin kwana. Don..."

"Taɓɗijam! Lallai dole Aunty tace baka da kunya yanzu, idan ba haka ba..."

"Ki bini mu tafi salin alin karatun yankan jaki."

"To shi kenan, amma ina son ka yi mini alfarma, ko dai ka barni zuwa gobe, ko kuma ka bari mu tafi bayan la'asar."

Hannu ya sa ya dafe ƙirjinsa "Rufani ki saya, Maza su kai ni ba Mata ba. Ina zan ɗaukeki tafiya da yamma, gwara na haɗiye ƙwalamata na jirayi goben idan da rai da lafiya. Amma wallahi da sassafe zan zo."
"Ba damuwa."

  Ya daɗe sosai a gidan sannan ya fita, wajen abokansu a ka gaggaisa.

Kitso ta sa ƙanwarta Balaraba ta yarfa mata, har za a yi mata lalle ta ga ba za ta iya jurewa ba. Sai a ka yi mata iyya hannu.

Isa bai dawo wurinta ba, sai bayan Isha'i. Amma sai taƙi fita daga ɗakin Mama dole ya ƙaraso ciki har ɗakin Mama. Daga tsaye yace "Da fatan dai lafiya?"
"Lafiya ƙalau, kawai barci nake ji sosai." Ta ƙare da lumshe ido.

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now