SO KO WAHALA? PAGE 33

39 2 0
                                    

[8/5, 9:54 PM] Mum Amnash: *HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*
            NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(MUM AMNASH)
    

          3️⃣3️⃣

*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*

_*Ƴan uwa kamar yanda kuka sani sunana MARYAM MUHAMMAD SANI (Mum Amnash) na shiga gasar marubuta sunan littafin nawa KOWA YA RAINA TSAYUWAR WATA... Ina fatan fans ɗina, ƙawayena, ƴan uwa da abokan arziƙi za su shiga su zuba min ƙuri'u a ranar Alhamis mai zuwa. Hanyar dangwala ƙuri'ar mai sauƙi ce, zan baku link a ranar zaɓen, ta nan za ku shiga google kai tsaye ku dangwala ku fito. Don Allah ku taimaka ku shiga ku zaɓe ni sannan ku tayani yaɗawa da zarar na saki link ɗin nasara ta taku ce ƴan uwa*_

       "Haleema" ya kira sunanta a sanyaye, Kanta a ƙasa ta amsa "Na'am" sai da ya cire hannunshi daga farantin kayan marmarin da suke gabanshi sannan yace "Ba ke kaɗai ki ke cikin matsala ba, ni kaina a cikinta na ke. Amma na miƙa komai na fauwalawa Allah. Soyayya wata irin halittace mai shiga ƙirji farat ɗaya ko a hankali, tana mamaye zuciya ba tare da tsammani ba. Ni ba mutum bane mai zurfafawa a so, na kanyi ƙoƙari wajen yaƙar zuciyata kan hanata zurmewa a soyayya. Ma'ana idan tayi ruwa rijiya idan ba tayi ba masai. A karon farko na saki jiki a soyayyar Jameela (ƴar duma-duma) amma farat ɗaya Mahaifinta yace na fito, shi aurar da Ƴar sa zai yi."

   Sai da ya numfasa sannan ya ɗora "Gaskiyata na faɗa mishi, na kammala karatu ina neman aiki amma duk da haka nakanyi taɓe taɓen lantarki, radio har wayoyi na kan gyara. Kafin na rufe baki yace wannan ba sana'a bace na koma na nemi abinyi, ba zai bawa ragwon Maza ƴar sa ba. A duk kalamanshi kalmar Ragwon Maza ita tafi komai ɓata min rai, idan na tuna kalmar ƙirjina har suya ya ke, suyar da ko rabinta banji ba a kan rabuwa da ƴar shi."

  Ganin ta lula duniyar tunani yasa ya tafa hannuwanshi a kusa da fuskarta, tayi firgigit! Ta dubeshi tace "Ina jinka" Da murmushi a fuskarshi yace "Za dai ki ji ni, Haleema komai na rayuwa haƙuri a ke da shi, ina son ki sani Baban Mama yana sonki matuƙa. Amma a cikin so akwai sadaukarwa da kawaici sannan da yakana. Yunus yana da hawan jini, Haleema mai zai hana ki sadaukar da soyayyar da ki ke yi masa don ya zauna lafiya ya kula da matanshi, Mahaifiyarshi da ƴaƴanshi. Ba za ki taɓa zama mai cikakken imani ba sai min sowa kanki abinda kike sowa ɗan uwanki Musulmi."

Hawayen da suke ƙoƙarin zubo masa ya mayar sannan ya ɗora "Rabuwa da masoyi akwai zafi, ɗaci raɗaɗi a wasu lokutan har da cire tsammanin samun rayuwa mai inganci a gaba. Amma da zarar ka miƙa komai ga Allah sai kiga ya wuce tamkar ba a yi ba. Ina son gobe ki kirawo Yunus idan ya zo ki tabbatar masa da Idan har bashi da halin aurenki kin haƙura da shi. Wallahi matuƙar ya na sonki to zai tsaya tsayin daka ya aureki, idan hakan bai samu ba ki gwada wani daga cikin manemanki. Wasu abubuwan ke koya maka darasi a rayuwa, yanzu haka na rarraba CB ɗina zuwa ma'aikatu da dama, duk aikin da na samu zan rungumeshi da hannu bibbiyu. Idan ban samu ba zan yi ƙoƙari na tuntuɓi Mum Amnash ta sanar dani dabarun da zan bunƙasa harkokin gyare gyaren kayan wuta na. Duk yanda rayuwa ta juyo to sai ka karɓeta a yanda ta zo."

   Hannayenta biyu ta sa  ta kamo hanneyensa ta haɗe da nata tace "Na gode sosai Ɗan uwana, haƙiƙa ka farkar da ni daga dogon baccin da na tafi, har na gagara farkawa. Ƙaramin misali yau ina Haseen ɗina? Ya mutu ya barni a wannan duniya mai cike da ƙalubale da hargitsi mabanbanta masu tarin yawa. Isah"

Bai amsa mata ba ya zare hannayenshi daga nata yace "Leema ki ƙara kulawa, ki daina yarda kina haɗa jiki ko hannu da kowanne namijin da ba muharraminki ba, ko da kuwa ni ne. Wannan ba wayewa bace taɓewa ce, ki kula sosai don na fuskanci har yanzu da sauranki." Ya ƙare zancen da murmushi a fuskarshi, haka kawai ya ji kaso 50 na damuwarshi ya tafi, ko don ya amayar da abinda ya dame shi ne?

SO KO WAHALANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ