SO KO WAHALA? PART 52

30 6 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)
*WATTPAD: @mumamnas2486*

14/Safar/1443 - 21/9/2021

5️⃣2️⃣

Zama ya yi a gefen gadon, hannunshi dafe da kanshi da ya fara sara masa. Sai da ya ɗau kusan daƙiƙu biyar sannan ya ɗago ya watsa mata idanunshi da suka yi ja. Kanta ta sunkuyar ta zame ta zauna dafa'an a ƙasan tayal ɗin da ke ƙasan ɗakin. Bakinta na rawa tace "Isa...don...don Allah ka fahimce ni. Wallahi ban yi hakan don na ɓata maka rai ba, sai..."

Hannu ya ɗaga mata yace "Ba sai kin ce komai ba Haleema nasan kina da ƙwaƙƙwaran dalilin yin hakan. Aiki, Kasuwanci da sauran hidindimu ko? Da kyau ki shirya ki tafi Zaria ki cigaba da aikinki. Idan kin samu lokaci ko a ƙarshen wata-wata sai ki dinga leƙoni. Allah ya bada sa'a ya bada nasara."

Da sauri ya ƙarasa kimtsawa ya nufi waje, da sassarfa ta bishi "Isaah" ta kira sunanshi a hankali. Juyowa ya yi ya tsareta da ido, har zai juya sai kuma ya tako ya zo dab da ita yace "Na yi mantuwa, Haleema zan tunasar da ke a matsayinki na ƙanwata ba Matata ba, ki sani shekarun haihuwarki sun kusa ƙarewa, saɓanin na Mijinki da yake kan ganiyarsa. Babu tilas a shawara, ra'ayinki ne ki bi, ko ki tankwaɓar. Sannan kar ki wani damu babu wanda zai ji wannan maganar kamar yanda na yi haka." Ya ɗora babban ɗan yatsansa da na kusa da shi a kan leɓensa ya ja, bai ƙara kallonta ba ya fice da sauri ya bar gidan.

Hawaye ne ya zubo mata a kuncinta, kalamansa na dawo mata, wani irin ƙunci take ji a zuciyarta. Danasanin auren ƙaramin yaro take, amma ya za ta yi ƙaddara ta riga fata.

Sai da ta ci kukanta ta more sannan ta nufi madafa, ruwan zafin da ta ɗora ta sauke, ta kashe gas ɗin ta koma falo ta kwanta don tasan ko ta zuba abincin ba za ta iya ci ba.

Sai da ya fara shiga gida suka gaisa da su Mama da Aunty, sannan ya zagaye bayan layinsu gidan makoki.

Ta'aziyya ya ƙara yi wa Musbahu, sannan ya koma gefen da Abokanshi suka fi yawa ya zauna. Duk yanda ya kai wurin ɓoye ɓacin ranshi, sai da Kamsusi ya gane, da ido ya fara tambayarshi, amma sai ya maze kamar bai gani ba.

Sai da rana ta fara yi sannan ta tashi ta cigaba da rage aikin gidan, ranta a matuƙar ɓace a fili tace "Isa taka wasa ce, wallahi sai na koya maka hankali. Sai ka gane Leema ba ƙasƙantacciyar Macen da za ka yi wasa da rayuwarta ba ce." Sai kuma ta fashe da kuka, tamkar taɓaɓɓiya ta nufi ɗaki ta ɗau jaka ta fara loda kayanta a ciki, tana tsaka da haɗawa ta ji bugun ƙofa. Kamar ta share sai kuma ta miƙe ta zura hijabi tace "Waye?"
"Ni ce Salaha"

Buɗe ƙofar ta yi tana bin Kyakkyawar budurwar da kallo, hanya ta matsa mata ta shiga gidan, hannunta riƙe da kwandon abinci.

Sai da ta sunkuya har ƙasa tace "Aunty ina kwana?"
"Lafiya ƙalau" Leema ta amsa tana mamakin kyawun yarinyar.
"Baba yace na yi miki godiya, Kaka ma tace tana gaisheki da kyau."
Murmushi Leema ta yi tace "Ina amsawa, ki shigo ciki mana." Jikin salaha a sanyaye ta bi bayan Leema har cikin falon. A ɗofane ta zauna, ko daƙiƙa goma ba ta yi ba tace "Aunty bari na tafi gida kar Baba ya yi mini faɗa."
"Ɗan jirani Salaha" da sauri ta ɗauko filas ɗin da ta zuba dankalin ta bawa Salaha tace "Ki kaiwa ƙannenki ba shi da yawa." Kamar ba za ta karɓa ba, sai kuma ta karɓa ta yi godiya ta nufi gida da sauri.

Komawa ɗaki ta yi, ta cigaba da harhaɗa kayanta, don asubanci take son ta yi gobe.

A sati ɗaya da Hadiza ta yi a gidansu, sai da ta gunduri yaran gidan. Ta zamar musu ƙadangaren bakin tulu, kullum garin Allah ya waye sai tace a yi tuwo da miyar kuka, tun abin baya damun Hajiya har ya zo ya isheta. Da kanta ta samu Mahaifinsu ta lallaɓashi ya kora Hadiza gidanta, a ka haɗata da Sadiya don Abida ta samu shiga Jami'a ba zama take yi sosai ba.

SO KO WAHALATahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon