SO KO WAHALA? PART 57

25 7 2
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                 NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)
*WATTPAD: @mumamnas2486*

8/R-Auwal/1443 - 6/10/2021

                5️⃣7️⃣

  Jikinta a sanyaye suka shiga gidan, duk a tsakar gida suka tarar da Mama, Aunti da Yaya Kabiru. Har ƙasa Leema ta tsugunna ta gaida su Mama, sannan ta gaida Yaya Kabiru. Kadaran Kadahan ya amsa, ba tare da ya kalle ta ba. Sum sum ta miƙe ta nufi ƙofar fita, "A'a ina za ki je?" Muryar Aunty ta katse ta. Kanta a ƙasa tace "Ɗakin ki za ni Anti" Ba ta jira cewar Anti ba ta fice da sauri ta nufi sashenta.

Shareta Isa ya yi ya cigaba da hirarsa da su Mama. A cikin hirarsu ya sakowa Mama zancen aikin da Alhaji Mai agogo ya zo masa da shi. Sai da ta ɗan yi jim sannan tace "Ni bana son rigima, amma idan har ba matsala to ka taimaka masa, amma da zarar ka ga da matsala ka sakar masa aikinsa. Tun da yace ko daga gida za ka iya yin aikin shi kenan. Allah ya baka sa'a da nasara. Allah ya yi muku albarka baki ɗaya."
"Amin Mamanmu, in kina tare da Auta mantawa kike da kowa Mama. Ai ni na daina hana Auta duk abin da yake so, don idan ya yi fushi ba dama."
"Ga ka ga shi ai, yana jin ka. In ɓera da sata to daddawa da wuri."
Murmushi Yaya Kabiru ya yi ya dubi Isa yace "Nasan Alhaji Mai agogo farin sani, yana da matuƙar kirki. Insha Allahu ba za ka samu damuwa da shi ba. Yanzu zan fita, ko bamu ƙara haɗuwa ba zan bar maka saƙo a wurin Mama." Yaya Kabiru ya ƙare fuskarshi ɗauke da murmushi. Mamakin yanda Yaya Kabiru yake nan-nan da shi yake, amma sai ya maze  ya yi masa godiya kawai. Sai kusan Ƙarfe Goma da rabi na safe sannan Isa ya yunƙura don ya tafi Kasuwa. Sashin Aunty ya leƙa ya yiwa Leema sallama sannan ya wuce wurin nemansa.

  Kai tsaye wurin Alhaji ya fara shiga bayan sun gaisa da Jabir. Sai da suka ɗan ƙara tattaunawa sannan ya bashi na'ura mai ƙwaƙwalwa (Laptop) yace "Ka kula sosai Isa, na yarda da kai ɗari bisa ɗari. Sannan gudun samun matsala ka dinga turo mini da duk  bayanan da ka shigar na kullum, don kayan nasara ba su da tabbas. Na gode sosai Allah ya yi ruƙo da hannunka."
"Amin" Isa ya amsa, sannan ya fita ya nufi teburinshi a ka cigaba da hadahadar cinikayya da gyare-gyare.

**********

  A tsaye ya tarar da ita a bakin teburunshi bayan sun dawo daga sallar Azahar, fuskarshi a sake yace "Barka da zuwa Hajiya, me ki ke buƙata." Cike da yanga da gwalangwaso tace "Waya zan siya, kuma na ga duk na nan ƙananu ne babu irin wadda nake so." 
"Ai babu damuwa, ga shago can a bayanmu ki shiga ki siya mana."
"No (A'a) bana son shiga cikin ne, idan babu damuwa ko za ka karɓo mini?"
"A'a, mu je na raka ki ki shiga ki siya da kanki." Ba musu ta bi bayanshi, daga ƙofar shagon ya tsaya ya kwaɗawa Musa kira, yana zuwa yace "Musa waya za ta siya, don Allah ku shiga ta zaɓa sauri take yi." Yana gama yi wa Musa bayani, ya koma bakin sana'arshi.

A tsaye ya tarar da Jabir yana cizon yatsa kai tsaye yace "Da fatan dai lafiya?"
"Ina fa lafiya, gaskiya Isa kai sabon yankan rake ne. Ba fa haka a ke yin kasuwanci ba, sam kai babu ruwanka da abinda ya kamata. Idan ba haka ba ai sai ka tambaye ni na gara maka layi."
"Ya Ilahi! Jabir ka yi wa Allah ka faɗa mini abin da yake akwai, ka tsaya sai kwalo-kwalo ka ke kana ja mini rai, ka faɗa kawai a wuce wurin."
"Yauwa ɗan gari, abinda na ke so ka gane, idan a ka zo siyan wayar da baka da ita komin tsadarta to ba cewa za ka yi babu ba, zaunar da mutum za ka yi ka kalallame shi da daɗin baki sannan ka yi wuf ka shiga wani shagon ka karɓo ka kawo masa. Idan ya baka kuɗin sai ka koma ka kaiwa mai shagon abinshi ka cire ribarka. Ka ga irin wannan manyan wayoyin  wallahi in ka haɗu da mai shago mara baƙin ciki sai ka samu Dubu Biyar cif..." Matar ɗazu ce ta dawo tace "Na gode sosai, na samu irin wadda nake so, karɓi wannan" ta miƙo wa Isa Dubu biyu. Girgiza mata kai ya yi yace "A'a ki barshi na gode." Cike da mamaki ta bi kuɗin da kallo, sannan ta ɗaga kai tana ƙare masa kallo. Jikinta a sanyaye ta wuce don ba ta ga alamun wahala ko kaɗan a jikinsa ba. Shadda ce gezna a jikinsa ɗinkin fakistan, kanshi ba hula, hannunshi ɗaure da tsadadden agogo. Ko ba a faɗa mata ba tasan, ba talaka ba ne. Cike da mamakin ganinsa a tebur ta bar Kasuwar.

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now